Sashe 88
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Toilet ya wuce da Brady ɗin, wanka ya yi tare da wankewa Bradyn kafa da sauransu, bayan sun fito dressing room nasa ya nufa, shiryawa cikin pajama milk color ya yi, ya ɗaura jacket mai ɗan girma a kai tare da ɗaukar wata ƴar karamar kyakkyawar trolley ya zuba kaya kala shidda a ciki, kala biyu ne cikakkun tsadaddun kaya jeans and T-shirt, kala biyu kuma three quarters ne masu bala'in kyau da tsada da T-shirt nasu, sai pajama guda ɗaya da kuma kayan barci guda uku da ya zuba daga baya, diamond watch nasa na TRIPLETS ya ɗauko tare da perfume nasa guda ɗaya, sai karamar kyakkyawar farar towel, shots and singles, da saukan kayan buƙata nasa, dukka ya shirya cikin trolleyn, bayan ya kammala ya sanya wani haɗaɗɗen cover shoe mai bala'in tsada kalar pajamar jikinsa wato fara, ya yi kyau ba karya, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshin perfume nasa yake yi, ya ɗaure kyakkyawar dark black curly hair sa a bayan wuya, ya ɗauki pistol gun, daga karshe ya sanya face mask a face nasa.
Jawo trolley ya yi zuwa cikin ɗakin, lokacin Brady ya fice waje, ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin Brady baya ɗakin, dan ba tafiya da shi zai yi ba, massage ya yi wa Mark a kan ya ɗaure mishi Brady ɗin kada ya ga tafiyarsu, sannan ya yi wa Areef massage a kan ya turo mishi Rimsha ta same shi a waje gate baki ɗaya, ya wuce ya ɗauki laptop nasa ya sanya a cikin trolleyn ta gefe, yana gamawa ya nufi waje abinsa.
Babu kowa a palon sama da kasan baki ɗaya, waje ya nufa kai tsaye, gabaɗaya sojojin dake gidan suka fara sara mishi, har suna rige rigen karɓar trolley dake hannunsa, hannu ya ɗaga musu alamar baya buƙata, buɗe mishi gate gateman ɗin ya yi, cikin taku mai nuna isa da izza ya nufi waje,. Ɗan nesa da gidan ya tsaya yana latsa wayarsa, alamar massage yake rubutawa.
Sanye take da kananan kaya dai kamar kullum, akwaita da son kananan kaya dan su ta taso tana sakawa, lokacin da daddynta, mummynta suke nan, shi ne kayansu ko da yaushe, shiyasa bata iya jurar saka wasu kaya sai su, wandon jeans ne pink color, sai riga fari, wandon akwai kyalli sosai a jikinsa, shi kuma rigar high neck t-shirt ne, ga rigar ya kamata sosai, da yake ita ba saka breziya take yi ba, sai gabaÉ—aya shatin tula tulan ya bayyana, dan ma ta sanya vest a ciki, bata saka bra sai vest, kanta na É—aure da pink É—in É—ankwali, gyalen abayar tane ta É—aura a kan nata, ta yi kyau sosai, sai zuba kamshi ita ma take yi, a tsorace ta fito wajen, kafin ta fito sai da gateman ya tsayar da ita, a kan ba zata fita ba, sai da ta gaya mishi Lion ne yake kiranta yana waje, sannan ya bata hanya dan yasan yanzu Lion É—in ya fita.
Ganin shi a ɗan nesa da gidan ga trolley a kusa da shi ba karamin mamaki ya bata ba, ɗan kunna hasken screen ɗin wayarta ta yi dan ta duba time, 8:20 cikin natsuwa ta karisa in da yake tsaye ɗin, cikin girmamawa ta ce mishi "Gani nan yaya Saif". Ko sannu bai ce mata ba, sai latsa waya yake yi, bai kuma kalli in da take ba, shiru ta tsaya a gefensa tana addu'ar Allah yasa lafiya. Tsayuwar minti goma suka yi a wajen sai ga wata danƙareriyar bakar mota kirar jeeb mai bakar glass ta paka a gabansu, sai kyalli motar take yi tamkar yanzu a ka fito da ita daga laidarta.
Wani jibgegen Baturen soja ne ya fito daga cikin motar, gabansa ya kariso cikin girmamawa ya miƙa mishi key ɗin motar yana risinar da kansa kasa, karɓa ya yi tare da ɗaga wa sojan hannu alamar ya je kawai, cikin sauri ya bar wajen ya nufi cikin gida, shi kuma Lion ɗin gidan baya na motar ya buɗe ya sanya trolleynsa kafin ya buɗe mazaunin driver ya shiga, ita dai tana tsaye tana ganin ikon Allah, bayan ya shiga ya kunna motar ne ya danna mata horn alamar ta shigo, da yake ita ma renon ice cream da madara ce ta gane nufinsa, sai ta buɗe gidan baya zata shiga, gently ya ce "Ni driver ki ne?".
Da sauri ta girgiza mishi kai tare da rufe kofar ta dawo gaba ta shiga, tana shiga ya bawa motar wuta suka É—auki hanyar barin cikin Kaduna, da yake ita bata san ta ina ake shigowa Kadunar or fita ba, sai bata san fita zasu yi ba, ta É—auka wani waje zasu je a cikin gari kawai su dawo, ga shi shi ya É—auki trolley da kaya, ita kuma daga ita sai na jikinta da waya a hannunta, lallai akwai case kenan, mu dai je zuwa.
A ɓangaren daddy jelly kuwa, suna barin gidan Abbi kai tsaye gidansu Anaya suka nufa, babu kowa sai mai aiki da Zaira da ta dawo daga school yanzu ba jimawa, bata da lafiya ne aka dawo da ita gida, school nasu daban daban da Anaya, su karfe 1 suke tashi, Anaya kuma karfe 2 , da farko school nasu ɗaya, daga baya daddynsu ya raba musu.
Sam daddyn Jelly bai ji daÉ—i ba, ya so su sami daddyn Anaya dan yana da magana da shi, amma baya nan yana Zaria, haka suka yi musu sallama suka nufi wajen shan ice cream, suna tafiya yana ta jan ta da hira, ta yi lamo a jikin kujera tana ganin hanya, a hankali yake tukin dan kula da lafiyarta, duk yadda ta É—an motsa sai ya tambayeta ko lafiya, gyaÉ—a mishi kai kawai take yi alamar e tana lafiya, cigaba da tafiya yake yi yana satar kallonta.
Daidai bakin wani ɗan karamin kasuwa irin na bakin hanya wadda yake a unguwa haka, ba za'a kira shi da kasuwa ba, dan ba girma gare shi na, irin waje ne haka da masu sayar da kayan miya su tumatiri da sauransu ke kafawa a bakin hanya ta cikin unguwa haka, daidai zasu wuce wajen a tsananin razane ta miƙe zaune tana faɗin "Daddy ka tsaya ga mamata can!.". Ba shiri ya ja wata iriyar birki, tun bai gama tsayar da motar ba ta buɗe ta fito da gudu, saura kaɗan wata motar ta taketa, Allah ya takaita mai motar ya kama birki, ita kam bata bi ta kan motar ba, wajen maman nata kawai ta nufa a guje, burinta kawai ta isa gareta.
Zaune take a kusa da masu sayar da kayan miyar, tana É—auke da kwanon bara a hannunta, ta yafo wani koÉ—aÉ—É—e kuma jemammen zaninta a kanta, ga wasu uban gudaje dake binta saboda dattin dake jinta, tamkar mahaukaciya haka take zaune a wajen, da alama ta murji bakar wahala na wuce misali, kuma da alama har yanzu bata da lafiya, ta rame sosai, fuskar nan tata duk ya mokaÉ—e saboda rama, wasu kasusuwar wahala ne suka bayyana a saman face É—in nata, tamkar mai cutar kanjamau.
Tun bata karisa wajen ba take ambatar mama, mama, mama, a hanzarce ita ma matar ta ɗago kanta dan ko mutuwa ta yi ta dawo ba zata taɓa mantawa da muryar ƴar ta ɗaya tilo a duniya ba, a guje ta zo ta rungumeta tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tare da ambatar sunan maman nata, ita ma maman rungumeta ta yi tuni hawaye suka wanke mata fuska baja baja. A wannan hali daddy ya iskosu bayan ya yi parking na motar da kyau, gabaɗaya jama'ar dake wajen hankalinsu ya dawo kansu, harta masu sayar da kayan miya a wajen dukkansu hankalinsu ya karkato izuwa kansu, sai kuka Ayla take yi tamkar ranta zai fita, ita ma maman kuka take yi ta kasa magana, an rasa mai rarrashin ɗan uwa.
Shi kansa daddy sai da idanunsa suka kawo kwallah, uwa ba wasa ba, almost shekara 4 kenan yanzu basu tare, ai dole su yi kuka, ko da ace ma rabuwar daÉ—i suka yi bare kuma rabuwar wahala, sace Ayla É—in akayi idan baku manta ba, kun ga kuwa rabuwar wahala rabuwar da basu shirya ba suka yi shi.
Sai da daddy ya ga kukan da take yi ɗin ya yi yawa, zai iya illatata, sai ya matso kusa da su tare da tsugunnawa a gaban nasu ya sanya hannunsa ya jawo Ayla ɗin zuwa jikinsa, juyowa ta yi ta kankame shi tana kuka tana faɗin "Daddy mamata ce, wlh ita ce, ita ce daddy!". Hannu yasa yana goge mata hawaye yana faɗin "Ya isa haka babyn daddy, ya isa kukan, ba shi ya kamata ki yi yanzu ba, murna zaki yi tun da mama ta bayyana, ki godewa Allah da ya bayyyana mana ita, dan Allah ki yi shiru kin ji ko?". Da yake bata yi mishi musu, bata saba ba kuma bata taɓa yi ba, sai ta yi ƙoƙarin haɗiye kukan nata, amma hawayen sunki tsayawa, ganin hakan ga kuma jama'a sun rufesu wasu ma har sun fara ɗaukarsu a video, sai ya miƙe tare da ita a jikinsa yana faɗin "Mama dan Allah ki tashi muje ko?". Bata musa mishi ba, ta miƙe ta bi shi, dan tun da ta kalle shi tare da ƴarta, tasan shi ne ya taimaki ƴar tata kenan, dan haka ba macuci bane, shiyasa ta yarda ta bishi zuwa cikin mota, jama'a da gulma sai video suke yi musu dan a sami na yin posting a media, yanzu da abu ya fara faruwa a waje, a maimakon jama'a su jajanta, sai su ɗauko waya su fara ɗauka, ko da kuwa accident aka yi a waje, Allah dai ya kyau.