Sashe 114
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yake ita ma jikinta ya saba tashi da asuba, sai ga shi ta farka, tare da miƙewa zaune, wani azababben sanyi ne ya bugeta lokacin guda, cikin sauri ta takure jikinta waje guda, baiwar Allah ta yi barci mai nauyi bata ma san ana ruwan sama ba, jin zuban ruwa yasa ta fara waije waije dan nemo ina yake, can saman sofa ta ganshi a kwance yana latsa waya, ware jacket ɗin nasa ta yi tare da sanyawa a jikinta ta takure waje guda tana rawan sanyi, jacket ɗin ya yi mata yawa sosai. Shiru shiru har aka yi sallar asuba, shi kuwa yana kwance abinsa daga shi sai T-shirt polo da jeans sky blue, amma baya jin wani sanyi, ita ce dai ta takure kanta, dama kuma kun san yanayi ba ɗaya ba, shi ya saba da sanyi mai kankara, dole ba zai ji komai ba a wannan sanyi tamu ta nan.
Karar sautin garuwar hakwaranta yasa shi ɗago idanunsa izuwa kanta, mamaki yake yi wai ita wannan wace iriyar mutun ce? Yanzu sanyin me ake yi a nan da har zata rinƙa bari har haka? Kai anya ba wani cuta yake damunta ba kuwa?. Ayya shi bai san mu a wajenmu wannan sanyi ne sosai mai ratsa kashi ba. Cigaba da latsa wayarsa ya yi bai sake bi ta kanta ba har gari ta fara haske, sannan ne ruwan saman ya tsagaita, lokacin karfe 5:44, miƙewa ya yi ya wuce izuwa cikin gida, da sauri ta miƙe ta bi bayansa, a tare suka shige, kai tsaye ya nufi bedroom nasa ita ma ta nufi nata.
Sallah dukkansu biyu suka yi dan lokaci ya kure, haka zalika kusan a tare suka shiga wanka, dan a tare suka dawo cikin gidan, bayan ya yi wanka ya fito, shiryawa ya yi cikin pajama launin white color, saman bakin bed nasa ya zauna yana ƙoƙarin kiran number Areef sai gasu sun shigo a tare kamar abin haɗin baki.
Saman sofa suka zauna, cikin sanyin murya da nuna kula da juna suka É—aga mishi gaisuwa, shiru ya yi bai amsa ba, can kuma sai ya É—ago da kallonsa zuwa kan Aseef, da ya dukar da kansa kasa kamar mai tunanin wani abin, ga kuma waya a hannunsa kamar mai latsawa, sai dai ga dukkan alamu ba wayar ma yake kallo ba, ya shiga duniyar tunani ne.
Zuba mishi idanu sosai ya yi yana kare mishi kallo, har yanzu akwai ragowar shatin yatsun É—an'sandan nan da ya mare shi a fuskarsa, wajen ya yi ja. "Who slapped you?". Ya faÉ—a yana É—aure fuska sosai, dama ga fuskar ba'a magana, tamkar hadari kullum, Æ´ar firgita ya yi tare da fara latsa wayarsa daka hannunsa, shi ya mance ma da marin nasa da akayi, yanzu bala'in da yake ciki tafi karfin mari.
"Wani É—an'sanda ne ya mare shi". Cewar Areef, "A kan me?!" Ya faÉ—a a tsawace, sai lokacin ya É—ago kansa tare da kai kallonsa kan fuskar É—an uwan nasa.
Æacin rai iya É“acin rai Lion ya ji, akan me wani zai É—aura hannunsa a saman kyakkyawar fuskar heartbeat nasu,? To koma waye uban shi sai ya karÉ“i hukunci wlh, dan bayan shi ba wanda ya taÉ“a É—ora hannu a saman wannan kyakkyawa kuma lallausar kumatun, shi ma sau É—aya ya taÉ“a marin shi, kuma da dalilin, so dan haka bai ga dalilin da wani mahaluki zai É—aura hannunsa a jikin TRIPLETS nasa ba kuma ya kyale shi, ba'ayi wannan mutumin ba a duniya a cewarsa.
Nan take Areef ya gaya mishi duk yadda aka yi, abin ya fara damunsa yanzu, wato kenan a kan Jehan wani ya mare shi? Wai shi ya rasa gane me matsalar TRIPLETS nasa da jinin Nawazudden ne, shi gaskiya yanzu sun fara ɓata mishi rai, ya fara jin ya tsani Nawazudden ɗin ma, akan me dalilinsa ƴan uwansa mafi soyuwa a garesa zasu rinƙa shiga haɗari, gaskiya shi ba zai yarda da hakan ba, dole ya taka musu birki kuma ya ɗauki mata, sai dai fa abin da bai sani ba shi ne, ya makaro, dan shi kan shi soyayyar Nawazudden ɗin tana cikin zuciyarsa, shi ne bai sani ba dan bai san menene ma soyayyar ba, amma tabbas shi ma yana kaunar Nawazudden da family'nsa, dama idan baku manta ba, da Rimsha da babanta muguwar shiga ran bala'i ke garesu, idan ka zauna da su to dole sai sun shiga ranka ta yadda zaka kaunace su ba tare ma da ka sani ba, to shi ɗin ma hakan ce, yana bala'in Kaunar Nawazudden ɗin, shi ne bai gane ba, kuma cire son Nawazudden a ransa ba abu bane mai yiwuwa a saukake yadda yake faɗe a baki, su kuma su Aseef sun riga da sun yi nisa, ba zasu iya dai'na son uncle nasu ba, ya zamo wani ɓari na jikinsu. TO FA BABBAR MAGANA SHI KUMA LION KISHIN BALA'I KE GARE SHI NA FITAR HANKALI, YANZU YA FARA KISHIN TSAKANIN ƳAN UWANSA DA DADDYN RIMSHA NE KO YAYA? DAN WANNAN DAI ALAMAR KISHI CE.
Shiru suka yi gabaɗayansu ba wanda ya sake yin magana, after some minutes Areef ya miƙe yana faɗin "Zan je prison tare da Mark ina dawowa". Zaro idanu Aseef ya yi yana faɗin "Prison kuma? Me zaka je yi a can". Nufar waje ya yi yana faɗin "Ƴar uncle zan je gani". Zai miƙe ya bishi Lion ya riƙo hannunsa tare da juyowa suna fuskantar juna.
"What is wrong with you?" Ya faÉ—a a sanyaye yana kuma tsare shi da blue eyes nasa.
Girgiza kai ya fara yi yana faɗin "Nothing". Shiru ya yi bai sake magana ba, dan dama baya tambayarsu abu ya sake maimaitawa, shi kuma Aseef ɗin ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi dole ya yi dan ya tabbatarwa da ɗan uwan nasa ba komai, ya san cewa idan har Lion ɗin yasan cewa a kan mace ya shiga wannan damuwa har haka, to fa shi da auren Heartbeat har abada, dan wlh Lion sai ya wargaza komai, zai ce dama ai yasan mata balai ce, daga haka kuma sun jawa Rimsha, abubuwa dai zasu kwaɓe sosai, shiyasa ya gwammaci ya ɓuye damuwarsa shi kaɗai, ko Areef ba zai gayawa ba, dan yasan dukka bakinsu ɗaya ne, idan Areef ya ji, to tamkar a kunnen Lion ne, dan sai ya gaya mishi, haka suke gabaɗayansu, ko shi Areef ya gayawa magana ya ce kada ya gayawa kowa, to fa sai ya gayawa Lion, wuyarta dai a faɗa mishi ɗin ne, ana faɗa zai labartawa Lion ɗin, shi ma Lion ɗin wani lokaci yana gayawa Areef ɗin magana idan ta shafesu or daddy, a takaice dai dukkansu bakinsu ɗaya ne, so mafi alkhari a gareka idan baka son ɗaya daga cikinsu yasan da magana, to ka ɓoye kayanka a cikinka, dan soyayyar da yake tsakanin TRIPLETS ya wuci wasa, sun wuci tunanin mai tunani.
A palon sama Areef ya ci karo da Rimsha tana riƙe da Jacket ɗin Lion da ya rufa mata daren jiya, "Good morning my lovely brother". Ta faɗa tana ɗan murmushi, "Morning our Queen ina zaki je?" "Zan mayarwa da yaya Saif rigarsa ce". Shiru ya ɗan yi yana kallon rigar kafin ya ce "Okey je ki dawo ina jiranki a wajen mota ki zo mu je wajen sister a prison". Cike da murna ta amsa mishi da to, da sauri ta wuce zuwa cikin ɗakin, shi kuma ya wuce zuwa kasa.
💋PRISONERS💋
Ɗakin da suka kai Jehan ɗaki ne mai ɗauke da mata guda uku da ita huɗu, biyu daga cikin matan, manya ne masu ɗan shekaru wanda a kallah zasu kai 28 haka, ɗayar kuma matashiya ce. Da yake bata san su ba, sai tana ɗari ɗari da su, saman gadon da ya kasance mallakinta ta zauna a bakin tana tunanin yadda zata yi da gidar Hjyr daɗi, ita ba halin da take ciki bane ma ya dameta, su Adiva dake gidan Hjyr daɗi sune a gabanta, da kuma yadda zata yi ta rusa gidan, a cewarta bata bukatar taimakon kowa, dan bata yarda da kowa ba, su kansu hukuma bata yarda da su ba, a cewarta ɓata gari sun yi yawa a ciki, dan haka sai ta natsu ta samu aboki na kirki wadda ta san ba na banza bane daga cikin hukuma kafin ta bashi hujojin da take da su, yanzu bukatarta ta fita daga cikin prison ɗin nan ne, idan ta fita, zata fara bincike a kan hukuma dan nemawa kan tafita, kafin nan kuma sai ta tabbatar da ta tsaya da kafafunta ta yadda zata ci uban Hjyr daɗi babu surki, ta tsani matar tamkar ta sanya wuƙa ta cinke mata maƙogoron wuya kowa ya huta.
Ɗaya daga cikin matan dake cikin ɗakin ne ta katse mata tunani da cewa "Yarinya sannunki da zuwa gidan holewa da shagali tare da sharholi, amma gaki ƴar karamar yarinya har haka laifin me kika yi da ya cancanci a kawo ki nan?". Ɗaya daga cikinsu ne ta sake katseta da cewa "To ya wuci kisa ne, kin san fa yaran yanzu duk ƴan ta'adda ne, bar ganinta yarinya hmmm wannan daga ganin idanunta a bushen nan ba karamar ɓarna zata yi ba a duniya". Ita dai shiru bata tanka musu ba, miƙewa matar da ta fara maganar ta yi ta dawo kusa da ita ta zauna tana faɗin "Ki saki jikinki, nan gidan jin daɗi ne ai, ki zama jan wuya dan ki zama zakarar gwajin dafi a gidan nan, a nan ba'a yin shiru shiru, wlh idan kika yi shiru shiru azabtuwa zaki yi, ki buɗe baki ki yi magana, yanzu dai gaya mini laifin me kika aikata da har aka kawo ki nan?".
(Niko na ce baki san da waye kike magana ba gaskiya, jehan ai ba shiru shiru ba ce, kawai bakunta ce, amma daga baya zaku san wace ce ita ai)
Juyowa Jehan É—in ta yi ta dafa matar tana faÉ—in "To ke laifin me kika yi da har aka kawo gidan yarin?".