Sashe 55
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ita ma ta zube gwiwowinta kasa a gabansa, cikin sanyin murya ta fara magana "Already you knew that i really love you, wadda zata soka ba tare da sanin waye kai ba, ita ce masoyiya ta gaskiya, sanin waye kai a yanzu ne ya girgiza ni, ya sa naji tamkar matsayina bai kai a soni É—in ba, amma ka dai'na tunanin zan dai'na sonka, never wlh, because kai ne first love É—ina".
Rimsha dai ta mai da su Tv, sai kallonsu take yi gwanin burgewa, da yake anguwa manya ne, babu mutane, kowa yana harkan gabansa, sai É—ai É—ai kun motoci dake wucewa lokaci zuwa lokaci.
"Yanzu you trust me ko?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e, saboda tsabar daɗi bai san time da ya matsa hannayenta dake cikin nashi ba, sai da ya ji ta ambaci wash ya farga tare da ɗan sassauta riƙon da ya yi musu. Kada ku manta fa, ita Akila a ɗaukarta da Areef take magana ba Aseef ba, bata ma san Aseef ɗin ba, ya kenan idan ta san ba wanda take tunani bane kuma? Mu dai je zuwa, Areef Rimsha ta yaba mata kyawawan halayensa ba Aseef ba.
Miƙewa tsaye ta yi tare da jan jannunsa dake cikin nata sama, alamar ya miƙe shi ma, ba musu ya miƙe tare da ɗan duƙawa yana kakkaɓe mata ɗan kuran da ya hau saman skit nata wajen da ta duƙa, ita dai har yanzu mamaki take yi, bata san cewa yes yadda take ganin turawa a Tv wajen kula da soyayyansu da abin da suke so hakan suke a zahiri ba, ta ɗauka a iya Tv ne, bata san a zahiri ma hakan suke ba, in dai suna son abu, to suna bashi tsantsan kula da iya iyawarsu.
Sai bayan ya kammala kakkaɓe mata ya miƙe ne ita ma ta ɗan duka ta goge mishi wajen gwiwowinsa daya zube su kasa, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har da sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya ya yi lokacin da ta fara kakkaɓe mishi.
Bayan ta Kammala ta miƙe tsaye suna fuskantar juna, ganin ta kafe shi da dara daran nan nata na gado ne yasa ya ɗan kyasta mata yatsunsa guda biyu a saman face nata, ɗan runtse idanun nata ta yi tana murmushi.
"Kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa". Ya faÉ—a yana murmushi, ita dai har yanzu bata yarda ba, idan ya ce ita kyakkywace, dan tana ganin ai daga cikin Æ´an uwansa Turawa ya fito, a wawtarta da shirmenta, tana ganin daga kan turawa kyau ya kare, bata san cewa a ko'ina akwai kyawawan gaske ba, kamar dai ita É—in, sai a tara turawa 50 ba'a a sami mai kyanta a cikinsu ba, hasken fatar kawai zasu fita da shi, kyau kam iya kyau Allah ya zubawa jinin Dr Salman da barrister Naurat, Ba fulatani da Baturiya, ya kuke tunanin haÉ—in zai fita, ai kunga suma madaran kyau ne a wajen.
Turo ɗan bakin nan nata kamar biro ta yi, cikin shagwaɓa ta ce "Ni Heartbeat ka dai'na ce mini kyakkyawan nan, dan nasan kawai kana faɗa ne dan ka ji daɗin bakin ka". Shima turo mata ɗan bakin nasa ya yi, tare da shagwaɓe murya "No serious nake gaya miki, you are so very gorgeous more than your expectations wlh". Shiru kawai ta yi ba dan ta yarda ba.
Sake kyasta mata yatsun sa guda biyu ya yi a fuska "Ga fa goribar ki a mota, na sanya Areef ya nemo mini tun kafin nazo, shi kuma ya sanya Prof ya nemo, a takaice dai ga shi nan na kawo miki, amma me ake yi da shi?". Jim ta ɗan yi tana maimaita sunan Areef, idan bata manta ba, idan kuma ƙwaƙwalwarta ya bata daidai sunan Areef Rimsha ta kira wadda ta ambata a matsayin masoyin ɓoye, to amma me yasa yanzu kuma ya ce ya sanya Areef ya memo mishi goriba, to shi kuma waye? Ko dai su dukka sunansu Areef Areef ne? Abin ya ɗan ɗaure mata kai.
Shi kuwa bai lura da yanayin da ta shiga na tunani ba, sai hira yake yi mata. "My heartbeat dan Allah yanzu zaka iya gaya mini sunanka?" Ta tambaya tana mai da kallonta kasa. Kai tsaye ya ce mata Aseef, maimaita sunan ta yi, sai ta ji da Aseef da Areef ai ba banbanci, hakan yana nufin ita ce bata ji sunan da Rimsha ta kira da kyau bane koyaya ne? Ta sake shiga ruÉ—u, sunan sunzo kusan iri É—aya, wai me yake faruwa ne? Ta kasa gane komai.
To fa Akila ta kasa gane komai, shawara kawai ki bisu a duk yadda suka zo miki, idan ma kin gansu dukkansu biyu, duk sunan da yazo bakinki, in ma Aseef or Areef duk maka musu kawai, ai dole su amsa tun da suka rikita mini ƙwaƙwalwa, Allah sarki Baiwar Allah sai ma kin gansu su biyun da black glass, a nan ne zaki yi ainahin rikicewa, a dai Nigeria idan ba Rimsha da Imran ba, ba mai iya banbanta su.......🤣 Ita ma Rimsha Allah ne kaɗai yasan baiwar dake gareta, yasa take iya banbantasu, shi kuma Imran ya sansu tun ba'a kai haka ba.
"Heartbeat Ammie ta ce kada na jima, zan koma gida ba dan ina son rabuwa da kai ba, sai dan kada na tsallake maganar mahaifiyata, ka kula mini da kanka, zamu yi waya ko? Yanzu ai zaka dai'na ɓoye mini number ko?". Jim ya ɗan yi kafin ya wuce ya buɗe bayan motarsa ya fito mata da kwalin goribarta da kuma kawatin da ya yi mata tsaraba, already Rimsha ta jima da yin barci abinta, kwata kwata Akila bata san cewa tare yazo da Rimsha ba, shi kuma hira ta yi daɗi ya manta ya gayawa Akila ɗin tare suke da Rimshar.
"Heartbeat ya kamata ka je ka gaida Ammie fa idan ka sake zuwa". Yana jawo akwatin zuwa gabanta ya ce "Okey zan je idan na sake zuwa, yanzu dai ga kayanki, zaki iya É—auka ne ko dai na kai miki ciki?".
Kada ku manta duk maganar da suke yi cikin harshen turanci suke yinsa, sannan karin wani haske, kada ku manta da Naurat da Dr Salman da farko a kasar Russia suke zaune, a can a ka haifi su Abba, to suma basu jin hausa sai da suka dawo Nigeria, hakan yasa su Jehan babu hausa a bakinsu sosai, dan iyayen nasu ma basu cika yin hausar ba, to suma su Akila turanci ya fi zama a bakinsu sama da Hausa, amma kuma sunfi kaunar yaren Hausa sama da turancin, shiyasa suke magana da Hausar idan suka haÉ—u da su Aafia, dan sun ce Hausa tafi musu ko wace yare a duniya, a takaice dai family'n Dr Salman duk gayyan Æ´an yin turanci ne, na yi muku bayani ne dan kada ku ce to a ina suke jin American English da suke magana da TRIPLETS, to suma tushensu dai English É—in turawan ne, shi suka iya, fatan kun gane?.
Da sauri ta buÉ—e kwalin goribar dan ta tabbatar da gaskiya, tabbas kuwa goriba ce da aduwa very fresh a ciki, gwanin ban sha'awa, É—agowa ta yi tana kallon shi, while shima ita yake kallo.
"Me ake yi da su My heartbeat?" Ya tambaya yana zura hannu a cikin aljihun wandonsa. "Ci ake yi". Waro dara daran brawn eyes nasa ya yi yana kallon goribar, maimaita kalmar ci ya yi a filli, jinjina mishi kai ta yi tana mai tabbatar mishi da ci kuwa.
Hannu ya miƙe mata, a kan ta bashi guda ɗaya, bari ya ci ya ji, shi da abincin Nigeria mai shegen daɗi da Musharraf yake girkawa a Washington DC ma, ya kasa ci bare kuma goriba.
Da farko kin bashi ta yi, sai da ya fara zuba mata shagwaɓa kamar zai yi kuka, sannan ta ɗauko goriba ɗaya aduwa ɗaya ta miƙa mishi, karɓa ya yi tare da kaiwa bakinsa da nufin ya gutsiri goribar, dan a wanke take kuma tana cikin leda kafin a sanyata cikin kwalin, sannan a cikin fridge Areef ya sanyata, a tunaninsa fruits ne kamar irinsu Apple, shiyasa ya sanya Mark ya wanketa tas, aka zuba a leda sannan aka sanya a cikin fridge ɗin, wai dan karta ruɓe kafin Aseef ɗin yazo.
(Wayyo cikina, goruba yaga gata, har da fridge 🤣 Wayyo rashin sani yafi dare duhu🤣🥱)
A tunaninsa laushi take da shi kamar apple, sai da ya kai bakinsa sai ya ji abu kamar dutse, da sauri ya fitar yana furta subhanallah, ya tsuke ɗan bakin nan nasa, tare da haɗa geran sama da ta katsa, tsabar dariyar mugunta Akila bata san lokaci da ta yi baya tana ƙoƙarin faɗuwa ba.
Bata kai ga faɗuwa ba ya yi maza ya riƙo hannunta ɗaya, har lokacin yana tsuke da ɗan bakin nan, ya je ya gabtari dutse ta kusa cire mishi hakwara a cewarsa, gata da shegen bauri kamar me, bai yi Sa'a ba, ya sami mai bauri a maimaikon zaki, tufarwa ya fara yi yana goge bakinsa da hannunsa, har lokacin sai dariya take yi mishi.
A shagwaɓe ya ce "Heartbeat stop laughing for me now". Yadda ya yi maganar ma, dariya ya kara bata, har da sanya hannu ta dafe cikinta saboda dariyar.
Turo ɗan bakin ya yi yana ƙoƙarin saka mata kukan shagwaɓa, cikin sauri ta tsayar da dariyar tana faɗin "Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat". Turo ɗan bakin ya karayi sosai, bai ce da ita komai ba, sai aikin zubar da yawu yake yi, tana son ta yi dariya, tana tsoron rigimarsa kuma, haka ta danne ta yi shiru suka yi sallama, ba dan sun so rabuwa da juna ba, sai dan kada Ammie ta yi faɗa.