← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 121

Sashe 8

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GyaÉ—a mashi kai kawai ta yi kafin ta wuce ta haye saman gadon, shi kuma, ya wuce ya nufi gaban mirror dan ya shirya.

Kafin ya gama shiri ya dawo, har ta yi barci abinta. Kusa da ita ya zo ya kwanta yana fuskartar sama, kamar mai yin wani tunani.

Can kuma kasa kasa ya furta "Ina son sanin su waye iyayenki? Ina son sanin a ina suke? Meyasami babanki? Meyasa mamanki ta rayu dake cikin kunci da wahala duk da cewa ta ce mahaifinki yana da kuɗi? Ina buƙatar waƴan nan amsoshi wadda kuma nasan mamanki ce kawai zata iya bani su!".

Shiru ya sake yi yana mai jin tsantsar kaunarta yana kara ratsa shi, tabbas yana bala'in kaunarta, amma kuma yana tsoron samun haihuwa da ita ba tare da ya san tushenta ba, in fact a matikar tsorace yake a duk lokacin da ya haɗa jiki da ita, jarabace kawai irin tasa yasa yake kusan tar ta ɗin, domin kuwa yana ji a jikinsa tabbas tana da alaƙa da su mummyn jelly, damuwarsa ɗaya kada ya kasance wadda ta haramta ne a gare shi ne, yasan mumyn jelly bata da ƙanwa, to yaya abin yake kenan?.

Da wannan tunane tunane barci ya kwashe shi, sai wani sauƙe ajiyar zuciya yake yi cikin barci, ita kuwa, Baiwar Allah, cikin kwanciyar hankali take zuba barcinta, numfashinta na fita a hankali.

GIDAN ABBO.

Tun da suka isa gida, Aafia ta kasa sakin jiki da su, sai wani Æ´an kame kame take yi, ba yadda Ummi bata yi ba, amma ina, A'AFIA taki yarda ta saki jikinta, da suka ga haka, sai suka kyaleta, É—akin Jelly Ummi ta kaita kafin ta dawo ta fara sallamar Æ´an biki, shi kuma Nawid É—akinsa ya wuce abinsa, ya je ya yi wanka ya kwanta yana tunani irin auren da aka yi mashi, gabaÉ—aya ya mance da zancen Abbo, ita ma Ummi bata kara tambayar ina Abbo É—in ba, bata kara neman numbersa ba, abin kamar ba lafiya ba, duk sun mance Abbo kam.

GabaÉ—aya jama'ar da suka zo bikin Ummi ta sallamesu akan anriga da an É—aura aure an wuce wajen, taki nunawa bakin waje Aafia, Æ´an uwanta kawai ta nunawa ita tare da yi masu bayanin abin da ya faru na canjin Amaryar da aka yi, ba karamin daÉ—i suka ji ba, sun kuma yi alkawarin zasu yi gangami suje su gaishe da Abbi, sannan su yi mashi godiya, sosai Ummi ta ji daÉ—i, amma kuma har yanzu tana tunanin Jelly, kewarta na nan a cike a cikin ranta, Allah ya jarabceta da son jelly ba kaÉ—an ba.

Har karfe 10 na dare Abbo bai dawo ba, babu shi babu labarinsa, haka zalika su kuma, ba wanda ya sake zancen shi, da alama ya rufe masu baki ne, ya kuma mantar da Nawid abin da ya faru a daren shekaran jiya.

Ummi da kanta ta shirya Aafia tsaf, ta yi mata kwalliya tare da bata kayan da ta sayawa jelly wadda zata sanya a ranar shiganta ɗakin miji, da yake Aafia ɗin bata da wani ƙiba, sai kayan suka zauna mata a jikinta sosai, danƙareriyar lace ce, milk color, kwalliyar jikin lace ɗin nan an yi sune da manya manyan zanen fulawa blue color, sannan an zuba mashi wasu shegun Stones masu bala'in kyalli, kuma stones ɗin sun daku da jikin lace ɗin sosai, lace ne mai shegen tsada, sai wani walwali yake, manya manyan abubuwan hannu na gold ta sanya mata a hannu wadda sun kasance nata ne da ta jima da saya ta ajiyewa matar ɗan nata kwaya ɗaya tilo a duniya zai aura, bakaramin kyau Aafia ta yi ba, sai dai idanunta da suka yi ja, alamar ta ci kuka ta ƙoshi, wani dankareren sarkar gold Ummin ta sake ɗaukowa ta sanya mata a wuya, sannan ta bata duk wasu kayan gyara da HJY BATULA ta haɗawa jelly bata gama shanyewa ba, ba musu ta ƙarɓa ta sha, komai Ummi ta ce mata, bata cewa A'a, sun zama kamar raƙumi da akala, a takaice dai, da kayan da aka sayawa Amarya jelly, da shi aka yi wa Aafia amfani, humra masu shagen daɗin kamshi Ummi ta sanya mata.

Amarya fa masha Allah, ta yi kyau tamkar ka sace ta ka gudu da ita, sai tashin kamshi take yi, mayafi Ummi ta rufa mata sannan ta riƙo hannunta suka nufi bedroom ɗin Nawid.

Da sallama suka shiga cikin ɗakin, sai hawaye Aafia take yi kasa kasa a cikin mayafin, domin kuwa yanzu a duniya babu abin da take tsoro biyun namiji, tamkar yadda take tsoron mutuwa, haka take tsoron haɗa ido da angon nan nata, jikinta sai kerma yake yi, Allah sarki baiwar Allah, ta ɗanɗani bakar azaba a hannun ƴan kidnaping, abin ya zauna a zuciyarta, hakan ya haifar mata da razana a cikin ƙwaƙwalwarta, wannan yasa kuma take mutuwar tsohon maza, ciki kuma har da angon nata, wato Dr Nawid, mutumin da take mutuwar so, yau ya zama mallakinta amma tana ji tamkar kabari aka kawota shiga ɗakin nan nasa da suka yi.

Lokacin da suka shigo yana zaune a gaban laptop nasa yana aiki, ya yi wanka yana sanye cikin kayan barci masu kyau brown colar, idanunsa na sanye da medicated glass, hannunsa na riƙe da pen ga kuma tarin takardu a gabansa, laptop ɗin nasa kuma tana ɗaure saman table dake tsakiyar bedroom ɗin nasa, shi kuma yana zaune saman wata sofa irin wadda ake sanya guda biyu a cikin bedroom ɗin nan.

Jin sallamar Ummi yasa ya É—ago kansa yana amsawa, cike da kulawa ya yi Maganar.

Karisowa cikin É—akin suka yi, a gefensa Ummi ta zaunar da Aafia, É—an gyara zama ya yi ta yadda Aafia É—in zata zauna da kyau, sannan ita kuma Ummi ta koma É—ayar sofar ta zauna.

Wani irin razana A'AFIA ta yi lokacin da Ummi ta zaunar da ita kusa da shi, jikinta har wani kerma ya fara yi, kasa ta yi da kanta tana cigaba da hawayenta, abin gwanin ban tausayi, daga Nawid har Ummi ba wanda ya lura da tana hawaye, saboda mayafin ya rufe mata fuska, kuma ta sunkuyar da kanta kasa.

Nasiha sosai Ummi ta yi masu kafin ta yi masu sallama ta fice daga É—akin. Ji Aafia tayi tamkar ta tashi ta bi bayanta, amma ba halin yin hakan, saboda bata da amsan da zata basu idan suka tambayeta lafiya.

Ummi na fita ya juyo da kallonsa kanta, cike da kulawa ya ce "Sannunki?". Shiru ta É—an yi kafin ta ce "Ina wuni?" Ta faÉ—a cikin muryar kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Maganar da ta yi tasa ya gane tana kuka, dan haka sai ya juyo da kyau suna fuskantar juna, hannu ya sanya ta buɗe mayafin nata, cikin sanyin murya ya fara magana "Kiyi hakuri, nasan wata kila kema baki so na, wata kila akwai wanda kike so, kila ma har kunyi alkawarin aure, amma ina son kiyi hakuri mu yi wa iyayenmu biyayya, Ummina tana masifar sonki, ke kuma Abbinki yana suna da har ya bani ke, ba zan taɓa mantawa da shi ba, ki dai'na kuka, na miki alkawarin zan riƙe ki hannu bibbiyu, ba zan taɓa saki cikin kunci ba, duk duniya idan kika cire iyayena, yayanki Prof shi ne mutun na uku da nake so, to ko dan Imran zan sanya ki farinciki, yanzu dai dan Allah ki daina kuka kin ji ko? Abar batun dangantakar da yake tsakanin Ummi da Aunty Hadiza, ke kanwata ce domin da ni da Prof duk ɗaya ne, dan haka ki ɗauke ni a matsayin Prof Kinji?".

Kara tsananta kukan nata ta yi sosai, domin ita kaÉ—an tasan ciwon da yake a cikin zuciyarta.

Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, kafin ya sanya hannu ya riƙo hannayenta, yana ƙoƙarin yin magana, a razane ta kwace hannayen nata, jikinta ya kara tsananta kermar da yake yi.

Bai damu ba, domin yasan waye Imran, yasan shi da addini sosai, so yana tunanin gabaɗaya kannensa haka suke, shiyasa da ta kwace hannunta sai ya yi tunanin ko dan irin faɗan da ake musu a gida tun suna yara akan kada su bari namiji ya taɓa su ne.

Cire medicated glass ɗin face nasa ya yi, sannan ya ajiye pen ɗin hannunsa, cikin natsuwa ya fara yi mata nasiha tare da nuna mata cewa shi mijinta ne, ko ya taɓata ba wani matsala, dan haka kada ta damu, har lokacin kukanta kawai take yi bata kula shi ba, da alama kuma bata cikin natsuwarta.

Ganin hakan yasa ya jawota jikinsa ya rungumeta yana É—an bubbuga bayanta, jin nasihar da ya yi mata ne yasa bata tashi daga jikin nasa ba, ta kwanta ta cigaba da kukan da take yi.

"A'AFIA baki so nane yasa kike yin wannan kuka haka?" Ya yi maganar can kasa kasan maƙoshinsa, tayi kuka sosai, ta kasa magana, sai dai kuma ta ɗan rage kukan nata yanzu.

Hannu yasa ya ɗago haɓarta yana kallon face nata, idanunta a runtse, shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya ce "Dan Allah me zan yi maki ki dai'na wannan kukan ne? Ni bana son kukan nan, ke amana ce a wajena, sannan kanwata ce ke, kuma matata, idan baki so na ne, ki gaya mani, ni nasan ta yadda zanyi wa Ummi bayanin ta fahimceni, kuma nasan shima Prof nasan zai fahimceni, sannan Abbinki ma zai fahimta, auren dole bashi da wata faida, ni nasan zama da wanda baka so babban ciwo ne, ba kowace zuciya zata iya jurewa ba, to kada ki damu, idan baki sona ko kuma kina da wanda kike so, ki gaya mani kinji kanwata?". Ya kai karshen maganar yana cire mata mayafin jikinta.

Girgiza mashi kai ta fara yi, amma dai ta kasa buÉ—e baki ta yi magana.
"Bakiso na ne kike girgiza kai?".

Sake girgiza mashi kai ta yi a karo na biyu.

"Kina sona?" Nan kuma shiru ta yi mashi bata motsa ba. Shiru shima ya É—an yi kafin ya zame mata mayafin nata gabaÉ—aya ya ajiye a gefe.
Chapter 8 · 0% Book details