← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 121

Sashe 105

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddyn jelly ne ya katse su da cewa "Kai duk ku lafa haka nan, Hanan dai Æ´ata ce, kuma idan har tana son kanina Ahmad to na bata, Ahmad ga Hanan ka tambayeta idan tana sonka to shikenan, ka kawo mini sadakinta ni zan isar da shi Katsina da kai'na". "Wannan gaskiya ne, Ahmad ga Hanan idan tana sonka, to zamu shige maka gaba zuwa Katsina, nasan ba za'a hanamu aurenta ba". Cewar Abbi. Shiru palon ya yi kowa ya zubawa Hanan da A'A idanu, sai wani kasa da kai take yi, shi kuma ya tsareta da ido babu ko kyaftawa.

Hanan, ya ambaci sunanta, kin É—ago kai ta yi, sai ma kara kasa da kai da ta yi, abin ku da jinin Turawa, su Abbi dukkansu babu kunya a lamarinsu, duk Naurat suka biyo, idan baku manta ba su Turawa dama haka suke, a gaban iyaye ake shan soyayya, suma iyayen a gaban Æ´aÆ´a suke shan love nasu son ransu, to shi ne yasa abin sam babu kunya a cikinsa, su A'A ma gabaÉ—aya cikin turawa suka yi karatun, so babu wata kunya a lamusansu, wannan dalilin ne ma yasa zaku sami Abbi da Aunty a palon kasa suna soyayyya, Aunty ta tada kai da cinyarsa ko a jikinsu, shiyasa suke zuba love iya son ransu har su daddyn jelly babu mai jin kunya yin soyayyya, misali lokacin da su Akil suka zo da matansu, ai kunga haÉ—uwa suke yi a palo, kowa yana kula da matarsa babu kunya, to uzuri zaku yi musu, suma ruwa biyu ne ba É—aya ba, shiyasa suke a haka, kuma su su Abbi idan baku manta ba, a can suka taso har sai da suka zama manyan samari kafin su dawo nan, daddyn Jelly shi kaÉ—ai Naurat ta haifa a Nigeria, shiyasa idan kuka lurama duk cikinsu shi ne kaÉ—ai mai É—an kunya, kuma yana nuna kunyarsa a fili kowa ya san shi da ita, amma hakan baya nufin shima É—abi'ar Turawan ya kyale shi, a'a akwaita sosai, ciki kuma har da zuba love babu kama hannun yaro, kuna dai ganinsa shi da Jelly'nsa ma bare kuma Ayla da take matarsa, ai abin nasu a jini yake.

"Kina sona Hanan?" Ya yi maganar yana kara tsareta da idanun, da yake ita kam jinin Katsina da mutan Kaduna ne, akwai kunya a lamuranta, sai ta kasa magana, tana son tashi ta bar wajen ma ta kasa, saboda tana ganin idan ta tashi za'a ce ta dawo, kuma ga kowa yana kallonta, dan haka sai ta cusa kanta cikin cinyoyinta tana murmushi, dan tana son A'A, ya yi mata, kuma shi ma irin mijin da kowacce mace zata buƙata ne, akwai kyau sosai na jinin Hausa Fulani, akwai kuɗi, ga ilimin addini da boko ba kaɗan ba, nitsastse da shi, bashi da hayaniya, so har cikin ranta tana kaunarsa, tun ranar ma da ya zo ya yi mata kyau sosai, ta rinƙa satar kallonsa.

Aunty ce ta katsesu da cewa "A'a fa Hanan kada ki yi mana hakan, ya muna shirin komawa India zaki wani ɓoye fuska, ki ɗago ki gaya mishi gaskiya kina son shi ko yaya?". Ta yi maganar cikin zolaya, shi dai Irfan sai murmushi yake yi bawan Allah, duk ya rame kamar mai wani ciwon, kuma ba wani ciwo da yake damunsa, kawai rashin samun kwanciyar hankali ne ta sako shi a gaba.

"Kada ku takurawa ƴa ta" Cewar daddyn Jelly, hannu A'A ya saka ya karɓi wayar da yake hannunta, numbersa ya sanya a wayar tata ya yi flashing, sai ga number tata ta shigo wayarsa, mai da mata da wayar tata ya yi a cikin hannun nata yana faɗin "Yaya Maik ku kyaleta ne, zuwa gobe zan dawo muku da amsa". Ita dai maman Ayla sai kallon A'A take yi, ita kuma Aylar sai zuba barci take yi a cinyar mijin nata, kunsan yanzu tana mumzalin barci ne, da ta kwanta kaɗan sai barci abinta.

A'A na ƙoƙarin sake yin magana aka sako labarai a Tv, "Ku kara mana Volume". Cewar Abbi, Aunty ce ta kara Volume ɗin, natsuwa suka yi dukkansu dan saurara, wata ƴar jarida ce ke magana kamar haka "A safiyar yau ne Allah ya yi wa shararren ɗan siyasarnan wato ABUBAKAR SALAHUDDEEN rasuwa, ya rasu ne kuma sakamakon taimakon da ya je yi, duk wanda ya san ABUBAKAR SALAHUDDEEN ya san shi mutun ne mai taimakon talakawa, yana kan hanyarsa ta zuwa gidan hutawarsa dake cikin Kaduna ya hangi wata yarinya a bakin titi tana zaune tana kuka, matashiyar budurwa ce da zata kai shekaru 18 zuwa 19 a duniya, ganin hakan kun san shi da taimakon yasa ya ce a tsayar da mota, da kansa ya fita ya nufi in da wannan yarinyar take zaune tana kuka, dan kunsan duk mai hankali ya ga yarinya budurwa da daddare a kan hanya tana kuka dole zai tambayeta ko me ya faru, yana isa wajenta dan ya tambayeta me ya faru, yarinyarnan ta zaro wuƙa mai kaifin bala'in ta shammacesa ta daɓa mishi da iya karfinta a cikinsa, daga shi sai wasu ƴan'sanda biyu dama suka tafi, nan take ya yi kokarin faɗuwa kasa ƴan'sandan suka riƙe shi, a nan ne ita kuma yarinyar ta gudu, dan babu security sosai a tattare da shi lokacin, gidan hutawarsa zai je ya huta, shiyasa bai ɗebi securitys ba, dama kun san mafiya yawancin lokaci haka yake yi, daga nan ƴan'sandan suka ɗauke shi zuwa asibitin, tun a hanya Allah ya yi mishi cikawa, ya ce ga garinku, a safiyar yau muka sami labari, ita kuma yarinyar ta gudu, sai dai an yi nasarar samun hoton fuskarta, a yanzu haka jami'an tsaron su bazama nemanta, wannan shi ne hoton ABUBAKAR SALAHUDDEEN tare da makashiyarsa JEHAN NAWAZUDDEN, da ƴan'sanda suka sami hotonta ne, a nan ne muka san cewa ƴar gidan Nawazudden ce, wanda ya kasance tsohon ɗan takarar shugaban kasa da ya rasu ta hanyar haɗari, sai abin mamaki a nan shi ne, Nawazudden dai ya mutu da shi da family'nsa dukka, to bamu san ya akayi ita kuma Jehan ta kasance a raye ba, hukuma suna nan suna bincike, kome yake ciki zamu rinƙa kawo muku labarai a kai a kai, ku kasance damu, mun gode da sauraran mu". Babbar magana, masu karatu, akwai lauje cikin naɗi, da ni da ku duk mun san cewa wannan labaran ba gaskiya bace, da farko Jehan bata kai 19 years ba 16 to 17 years gareta, na biyu kun san ba'a kan hanya ta daɓa mishi wuƙa ba, a cikin gida ne, kuma ba ɗaɓa mishi wukar a ciki ta yi ba, yanke mishi gaba ta yi, amma ya akayi cikin ƙanƙanin lokaci a ka juye maganganun dukka, kenan dan a rufawa ABUBAKAR SALAHUDDEEN asiri ne a matsayinsa na ɗan siyasa ne a kace hakan ko kuma yaya abin yake,? Lallai an shiryawa Jehan kadar zare ba na wasa ba, daga ganin wannan abin babban shiri ne daga abokan gaban mahaifinta, dan yanzu faɗar ta koma ta siyasa, ba abin da zamu ce sai dai Allah ya kuɓutar da Jehan, mu dai je zuwa, komai zai warware a hankali, ku kasance da alkaramin Fateema Zahra Musa dan jin yadda zata kasance.

A wani irin mahaukacin razane A'A ya miƙe tsaye, dan ABUBAKAR SALAHUDDEEN ba kowa bane face mahaifinsa da ya haifesa, AHMAD ABUBAKAR SALAHUDDEEN shi ne suke ce mishi A'A, miƙewa su Abba ma suka yi dan su taushe shi, saboda duk sun san mahaifinsa ne, miƙewa ita ma maman Ayla ta yi tana faɗin "Alhadulillah, Alhadulillah, Alhadulillah, Allah na gode maka da ka muna mini mutuwar Abubakar kafin na bar duniya, azzalumin, mugu, macuci, banso ka mutu a haka ba, na so ne ka mutu a walaƙance, wanda ko kare sai ya fika daraja, bakin shaiɗani". Tana magana tamkar wadda ta zare, da alama farinciki ne ya yi mata yawa.

Kwantar da Ayla a hankali daddyn Jelly ya yi tare da miƙewa yana faɗin "Mama lafiya me yake faruwa,? Menene tsakaninki da Abubakar kuma?". Nisawa ta yi tana ta uban murmushi wadda tun da ta zo gidan bata taɓa yin shi ba "Abdul Malik wannan Abubakar ɗin da kake gani ba mutun bane, shaiɗan ne yazo a siffar mutun, ba kuna tambayata waye uban Aliya ba,? To shi ne, shi ne uban Aliya". Tashin sense da ba'a saka miki date. Nan take kallo ya dawo kanta, gabaɗaya palo suka zuba mata ido, Ayla baiwar Allah sai zuba barci take yi, bata san me yake faruwa ba.

"Shi ne mahaifin Ayla kuma?" Cewar Abbi, "Kwarai kuwa shi ne uban Aliya, babu wata tantanma, bakin azzalumin, ai naso Aliya ta girma ta kai mishi kanta da kanta ne, idan ya isa yanzu kuma ya ce ba yarsa bace, ai da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, da ya tashi bani ita sai ya bani ita kaman uban nata sak, babu in da ta baro shi, lokacin da take cikin cikina, ya ce ba cikinsa bane, ni kuma nasan ba mazinaciya bace, ban taɓa zina ba sai da shi, bayan shi ni ban taɓa kusantar wani ɗa na miji ba, nasan cikinsa ne, amma ya ce ba nashi bane, ya barni cikin bakin azaba da wahala, saboda son kai irin nasa, to ga shi yanzu babu wanda ya isa ya ɗaga idanu ya kalli Aliya ya kuma kalli Abubakar ya ce ba ubanta bane, kama harta idanunsa bata bari ba". Tana magana tana murmushi yau zuciyarta fari tas.

Cikin dakiya Abbi ya ce "Dan Allah ki yi mana bayani dallah dallah yadda zamu gane, ya akayi ya zama mahaifin Aliya? Kun taɓa yin aure da shi ne?". Dariya ta yi kamar zautatciya, da alama ta cutu sosai na abin da ya yi mata, da alama yau farincikin ya zautar da ita baiwar Allah, bata jin komai yau sai murna, dan haka bata damu ba zata iya wangale komai yau, dan tasan ko bata faɗa yau ba, to dole gobe ta faɗa, dan dole mijin Ayla ya buƙaci jin tarihinta.
Chapter 105 · 0% Book details