← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 121

Sashe 20

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki ne ya kamata, wai har da wani cewa to, shi kuma bai kawo komai a ransa ba, ita kuma ta dage shi ba É—an Nigeria ba ne, shiyasa ta yi mashi wayo dan ya gaya mata kasarsa ta hanyar cewa da ta yi bata san kasarsa ba, bare ta san tsarabar me zai kawo mata, amma ya ce a Naija yake, ta ce goriba ya ce mata to, anya kuwa da gaske yake yi? Anya ya san wannan goriba kuwa? Amma dai zata gani ai, ba dai ranar laraba ya ce ba, to shikenan ai.

Ta nutsa duniyar tunanin can ta tsingayo zazzakar muryarsa kasa kasa yana faÉ—in "My heartbeat ki zo na baki abinci a baki kin ji ko?". "Ka bari sai ranar Wednesday idan kazo sai ka bani a baki É—in". "Are you serious?" Tabbatar mashi da hakan ta yi, sosai ya ji daÉ—i kamar me, suna hira yana cin abinci a nutse, sai wuraren karfe 2 na dare suka yi sallama cike da kewa da kuma masifar kaunar juna, ba dan sun so rabuwa ba, dare ne kawai ya yi, daren ma dan ita yake tausayawa yasa ya hakura, baya son ta kasa tashi tayi sallar asuba.

GIDAN LION💋

Dare misalin karfe 8, Rimsha, Imran, da kuma Areef, suna zaune a palon sama, Areef dai Alhamdulilah jiki ya yi kyau sosai da sosai, waƴan nan shaiɗanun matsafa sun sake shi da karfin ikon Allah, amma anci kwakwa fa, Lion ya sha baƙar wahala ba kaɗan ba, su TGA sun yi nasarar tarwatsa kunjiyar tsafinsu Josephine ɗin, sai dai sun rasa sojoji da dama, ciki kuma harda babban yaron TGA, shi ma TGA ɗin ya ji ciwo sosai a kefen cikinsa, yanzu haka yana gadon asibiti. To sai dai muche Alhadulillah, an gama da shegun matsafa, yanzu Josephine da Areef sun fita daga koma.

Sai hira suke yi cike da kula, da kuma girmama juna, massage Lion ya yi wa Imran akan RIMSHA ta kai mashi abinci, da alama yau ya ji yunwa sosai, bawan Allah yau yasha wahala sosai gaskiya, kawai mutun ba zai taɓa gane hakan a kan face nashi or a yanayinsa bane, domin kuwa kullum a siffa ɗaya yake idan baku mance ba, amma yau saboda waƴan nan ƴan iska matsafa na jikin Areef ya sha wahala over, dan sai da ya yi wa Areef ɗin dannar yankar rago kafin ya samu ya fara yi mashi addua'o'i da karatun Alqur'ani mai girma, ba ƙaramin dambe suka sha ba, Imran kam guduwa ya yi tun da Areef ya maka shi da kasa sau ɗaya, ita kuma Rimsha tana ɗaki tana sallah tana kuka tana riƙon Allah da ya bawa Areef ɗin lafiya.

Yanzu dan ance ta kai mashi abin bata damu ba, dan tana ganin É—azun sun wanye lafiya, a shirmenta wai ta fara gane me Saif yake so, yarinya yarinya ce, har izu yau TRIPLETS nasa ma sun kasa iya tantance abu guda É—aya da yake so bayan kaunarsu, sai ita ce wai ta gano me yake so, to fa mu dai je zuwa.

Miƙewa ta yi ta nufi kitchen, binta da kallo Imran ya yi, ciro wayarsa ya yi domin ya kira tailor da ya bawa ɗin kin kayansu, ya ga ji da kallonta da shigar riga da wando, yana tsoron abin da zai je ya dawo, baya son su yi aikin danasani.

Tabbatar mashi tailor ya yi akan tabbas rana ita yau azo a karɓi kayan, to ya amsa da shi kafin su yi sallama, ajiye waya ya yi suka cigaba da hira da Areef.

A cikin zuciyarta ta yi sallama a bakin kofar kitchen ɗin, annabi ya ce katabbatar da kana yin sallama ne a in da aka san darajar sallama, a in da ake amsata, kada ka yi sallama a in da za'a walakanta sallamar, to shi Mark ai bai san darajar Sallama ba, kuma ba amsata zai yi ba, shiyasa take yi a cikin zuciya, karisawa cikin kitchen ɗin ta yi, sannu ta yi mashi, tamkar babu shi a cikin kitchen, kamar dai yadda suka saba, bai ɗago kai daga abin da yake yi ya kalleta ba, haka zalika, bai amsa sannun da ta yi mashi ba, kamar wani mai aljanu, ɗazun ya yi mata magana da bai taɓa yi ba, yanzu kuma ta yi mashi yaki amsawa, to Allah ya shirye shi.

Wucewa ta yi ta wanke hannunta kafin ta É—auki abin nasa, har lokacin tamkar babu Mark a cikin kitchen É—in nan, ficewa ta yi abinta, sanye take da wandon jeans baki ya kamata da ga sama har kasa, jikin wandon akwai kyalli sosai farare a jiki, sai ta sama kuma, top mai dogon hannu ta sanya, launin maroon color, ba karamin kyau ta yi ba, kamar kullun hijabin É—an karami mai taken please call me ne a jikinta, bakin hijabi ne kalar wandon, kafarta na sanye da takalma flat shoe Maroon color, sai tashin kamshi nata perfume É—in take yi.

Sallama ta yi mashi a bakin kofar É—akin, yana zaune saman sofa set yana latsa wayarsa, jin ya yi shiru ne yasa ta kutsa kai cikin, tana mai kara kwaÉ—a wani sallamar.

A wannan karon ma saura kaɗan ta saki tray ɗin abincin saboda razana da kallonsa da ta yi, sai dai Allah yasa ta riƙe abincin da kyau sosai, hakan yasa bai ɓare ba. Sanye yake da kayan barci, wando dogo har kasa, sai riga mai guntun hannu, damatsan hannunsa suka firgitata, domin gajartar hannun rigar ta bayyanar da su a waje, kamar dai kullun kunsan yana tashin wannan fitinannen kamshin nasa, da alama yau barci yake ji da wuri, Shiyasa ya buƙaci abicnin da wuri haka, ga alamar hakan ka a face nasa, sai lumshe idanu yake yi, gashin kansa a kwance, ta zubo mashi a fuska kasancewar ya sunkuyar da kai a kan wayarsa.

A in da ta saba ajiye mashi abin cin, a nan ta ajiye mashi, saboda neman magana irin nata har da wani ce mashi good evening, ai ko tamkar babu shi a cikin É—akin bai amsa ba.

Ganin hakan yasa kawai ta fara zuba mashi abinci, sai da ta zuba rabi ya sauƙo daga saman sofar ya dawo wajen da yake zama dan cin abincin, ya zauna, abin da ya bata mamaki shi ne kafin ya zauna sai da ya yi bismillahi, tana jiyoshi ya yi kasa kasa, kenan hakan ya nuna duk wasu dokoki da wasu abubuwa da suka danganci addin dan korar shaiɗan a kusa da mutun kenan yana yi, kuma yasan su fa, amma meyasa baya amsa sallama na? Ta tambayi kanta, abin da bata sani ba shi ne, kamar yadda ya yi wannan bismillahi yanzu, to fa haka yake amsa mata sallamarta, sai dai maganar tasa ce idan ba'a kusa da shi sosai kake ba, ba ji zaka yi ba.

Bayan ta gama zuba mashi ta tura mashi abincin a gabansa, ba ɓata lokaci ya ɗauki spoon ya fara cin abincin nasu, wani irin kalar green ne abinci, ita ko kallon abincin ma bata son yi, sai mamaki take yi, abin cin wani gubar wani, su kuma nata abincin ne suke jin ko da me sun yafe cin shi.

Spoon É—aya ya kai bakinsa, da kyar ya haÉ—iye abinci, kawai ma dan baya son dawo da ita ne yasa ya haÉ—iye da kyar É—in, ta lura da hakan, da mamaki take satar kallon shi, ko me ya faru da abincin Oho.

Ajiye spoon É—in ya yi tare da É—aukar wayarsa, kasa ya yi da kansa yana latsawa, zuba mashi idanu kawai ta yi tana kallon yadda ya kara É—aure fuska sosai, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo, tabbas akwai abin da ya faru da abincin, wannan irin uban É—aure fuska da ya yi haka ba'a banza ba.

Nan take wani irin tsoron shi ya dira mata a ranta, ji take yi tamkar ta tashi ta gudu, dan ganin ya kara É—aure fuskar, suna a haka Mark ya shigo É—akin ya same su, hannunsa rike da bowl mai É—an girma, gabansa ya zo ya ajiye bowl, ba tare da ya yi magana ba ya juya ya koma wajen hukuncin da aka yanke mashi yanzu, shi mai girkin ma first.

Da mamaki take kallon pepper dake cikin bowl É—in, an wankesu da kyau, ga su fresh, ta rasa me hakan yake nufi, me kuma za'ayi da su.

Miƙewa ya yi, ya koma saman sofa ya zauna, gently ya ce ta cinye attarugun nan dukka, zaro idanu waje ta yi, yau ta shiga uku laifin me tayi? Ta tambayi kanta da kanta, abin da bata sani ba shi ne, abinci da ta kawo mashi, yau Mark ya yi kuskuren da bai taɓa yi ba, yaji ta kubce a cikin abinci, shi kuma Lion kwata kwata baya cin yaji, komai kankantar ta saboda gym da yake yi, idan har ya ci yaji takan iya yi mashi mummunar illar a jiki, kuma tun kafin ya fara gym ma, shi baya haɗa hanya da yaji, ba'a taɓa yi mashi girki da ya ji ba sai yau, Mark ya yi kuskure, kuma yau kamar ba lafiya ba, sai bai ɗan ɗana abincin ba, haka ya shiryawa ogan nasa, to ita laifin kawowa kawai ta yi shi ne a kace ta ci attarugun, shi kuma Mark na shi hukuncin wa iya zubillah kwakwalwa ba zata ɗauka ba, kuma babban abin haushin shi ne ma zai hukunta kansa, idan kuma ya yi ɗaya ba daidai ba yasan halin ogan nasa, bai ma isa ya tsallake ba. BABBAR MAGANA MAI GIRKA ABINCI DABAN WAƳAN DA HUKUNCI KE SHAFA SU MA DABAN, KENAN KO MAI KANKANTAR SA HANNUN DA MUTUN YAKE DA SHI A WAJEN YI WA LION KUSKURE YA SHIGA UKU TAB ƊI JAM!!!.
Chapter 20 · 0% Book details