← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 121

Sashe 53

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da mai gadi ya ɓuɗe mata gate ta fito ya tsareta da idanu ta cikin glass, bata kai ga karisowa wajen motarsu ba, ya buɗe kofar motar ya fito, a zuciyarta ta ambaci tabbas shi ne, da yake ya sanya bakin glass bata ga kalar kwayar idanunsa daban dana Areef ba, bata saba ganinsu a tare ba, ba zata iya banbance su lokaci guda haka ba, kuma jini ba wasa ba, sannan kuma TRIPLETS ai ba karya ba, dole akwai wannan kama da idan ba a tare ka gansu ba, ba zaka iya banbanta su ba, amma fa ta ruɗewa kyau iya kyau, ta birkice, kuma tabbas a Areef ta ɗauke shi, shi kuma Aseef ne, cakwakiya kenan, ita dai Rimsha idanu kawai take binsu da shi, abin ya ɗaure mata kai, to wai shin wanene mason Akilar a cikinsu? Alamu dai sun nuna ba Areef bane, kamar yadda ya nuna mata da farko bai ganeta ba, bai da alaƙa da da ita, to hakan ne, yana da gaskiya.

TUN FARKO YA KAMATA KU ƊAUKI HASKEN WAYE MASOYIN AKILA A CIKINSU, WAYE TRIPLETS SUKE CEWA HEARTBEAT ƊIN SU❓ WAYE AUTANSU❓ IDAN BAKU MANTA BA YANA YAWAN CE MATA HEARTBEAT+HEARTBEAT, FATAN KUN GANE❓ SAURA KUMA ITA MA AKILAR TA GANE

Da fara'a ta kariso wajensa, da yake polo t-shirt ya sanya sai bata banbance yanayin jikinsu ba, cikin harshen Hausa ta ce mishi "Sannu da zuwa sarkin basaja, yanzu ma zaka ce mini baka gane ni ba ko?" Ta yi Maganar cikin zolaya.

Cikin harshen turanci ya ce mata "Kiyi magana da English ni bana jin Hausa". Babbar magana, to fa, ya tabbata basa jin hausa, amma ya akayi yake magana da ita a waya da Hausa,? To ko dai ba shi bane? Anya kuwa, kaina ya kulle sai Allah ya kaimu Monday da rai da lafiya dan jin ya wannan cakwakiya take, baya jin hausa kuma?🤔

Wayyo heartbeat+ Heartbeat, Auta+ Auta, Shagwaɓa+ Shagwaɓa, Kuka+ Kuka, Iya soyayya+ Iya soyayya, Tsarkakkan zuciya + Tsarkakkan zuciya. Ya kuke ganin Abin❓ Akwai cakwakiya a TRIPLETS sosai gaskiya. Masu cewa TRIPLETS ya zo ƙarshe to ku gyara zama, da sauran rina a gaba, wlh yanzu wasan zai fara, akwai tambayoyi da dama da idan na yi musu sai ku rantse da Allah yanzu ma zamu fara littafin nan, amma dai ba sai na yi muku ba, mu haɗu Monday kawai.

Ina barar addu'arku serious bani da lafiya, jikina yaki daÉ—i, kawai daurewa nake yi.
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E21-22

Cikin harshen turanci ya ce mata "Kiyi magana da English ni bana jin Hausa".

Babbar magana, to fa, ya tabbata basa jin hausa, amma ya akayi yake magana da ita a waya da Hausa,? To ko dai ba shi bane? Anya kuwa, kaina ya kulle, baya jin hausa kuma?🤔

Da mamaki ta zaro idanu tana kallon shi, baya jin Hausa kuma? Ta maimaita a ranta.

"Why are you surprised after I told you I'm not understanding hausa?". Ya yi maganar yana tsareta sosai da idanunsa, da yake a cikin bakar glass ne, sai bata fahimci yana ganinta É—in ba.

"How am I sure that you are not understanding after all we are chatting with hausa?". Wayarsa ya ciro ba tare da ya yi magana ba, numberta ya fara kira, É—agowa tayi ta kalle shi, alama ya yi mata da hannu a kan ta É—auki kiran.

Jim ta É—an yi kafin ta É—auki kiran, kara wayar a kunnensa ya yi, cikin harshen turanci ya ce mata "Hello my heartbeat good afternoon". Abin mamaki ita kuma sai ta ji maganar nasa da Hausa ya zo mata wayar tata, domin ta gasgata maganar abin da take ji, sai ta ce mishi cikin harshen Hausa "My heartbeat ina kewarka sosai". A cikin wayarsa ta ji muryarta na magana da English, babbar magana to me hakan yake nufi?.

A sukwane ta cire wayar daka kunnenta tana bin screen ɗin da kallo, shi kuma kallon rikitatciyar face nata kawai yake yi, da dai yaga bata da niyar magana ta shiga ruɗu sosai, sai ya ɗan matso kusa da ita, cikin shagwaɓa da harshen turanci ya fara magana "Sarkin shiga ruɗu ba, to ke yanzu a wannan ɗan abin me na shiga ruɗu fisabillilahi?". Ɗago idanuwanta ta yi tare da sauƙesu a kansa, "My heartbeat dole zan shiga ruɗu, taya hakan ta faru please,? How comes ni zanyi magana da Hausa kai kuma zaka ji da English, kuma ga shi murya ta ce da komai, sak yadda nayi magana, amma kuma ba da yaren da nayi ba yaje maka".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Na sha wahala sosai kafin na iya canzawa number ki language, sai da naje company musamman a ka buga mini wayar nan, lokacin da na je sayawa uncle Musharraf waya, a lokacin nasa aka buka mini ita, na kuma sanya a saka mata wannan tsari, ina sonki, kuma bana son ki san ni waye, ina sone in yi miki magana da yarenki dan hankalinki ya fi kwanciya da ni, dan ki karɓeni hannu bibbiyu, nasan idan na kiraki na fara magana da yarena, ba zaki wani ɗaukeni da muhimmanci ba, hasalima cemin zaki yi wrong number ne, saboda keɗin mai daraja yarenki ne, kuma hakan ya kamata kowani ɗan adam ya kasance, ya zama mai daraja yaren iyaye da kakanninsa, kada ya zama mai aron yare, sai dai a ari tasa yaren, kada ya yarda shi ya ari na wasu, wannan dalili yasa na sanya aka saka mini wannan tsari a wayata, dan koba komai idan kika ji nayi magana da Hausa, tabbas zaki saurareni, ko da kuwa ba zaki so ni ba, albarkacin wannan yare naki da nayi zaki bani dama, kuma nayi nasara, albarkacin magana da Hausar tasa kin bani dama, kin kula har na shiga zuciyarki, amma ina mai baki hakuri a kan hakan, nasan ban kyauta ba, yanzu dai kin ji, wayata ke canza maganar da na yi daga English ya baki da Hausa, shiyasa Hausar take fito miki a kema na fiki iyawa ai, dan ba mutun yake yi ba, computer yake yi". Ya kai karshen maganar cikin zolaya yana ɗaga mata gera ɗaya.

ÆŠaure fuska ta yi tamkar ba ita ce mai murmushi yanzun nan ba, a kule ta ce "A ina ka san ni? Waye ya baka number ta?". Zuba mata idanu ya yi na Æ´an mintoci kafin ya É—an gyara tsayuwarsa cike da kulawa ya fara magana.

"Haba My heartbeat why sudden changed on your face, from smile to mood? Don't you know that i really like your smile? Please put smile on your face, so that I can get peace of mind". Kin kula shi ta yi, sai ma juyawa da ta yi da nufin ta koma cikin gida, ita a dole ta yi fushi da shi.

Cikin sauri ya riƙo hannunta, gabaɗayansu sai da suka ji wani shock, abin ku da zuciyoyin masoya, ya riƙe hannun Rimsha bai ji komai ba, dan ba ita ce ainahin wadda zuciyarsa ke marari ba, ita ma tana riƙe hannayen ƴan uwanta, bata jin komai sai na shi yau, har wani irin yarr suka ji a jikinsu lokaci guda.

"Please My heartbeat am so so sorry, okey don't change your face again, I will amsa you like this". Kasa kasa ta ce ya sakar mata hannu, kara marairace murya ya yi tamkar zai yi kuka, a shagwaɓa ya ce "Okey zan saki, amma please promise me that you can't go anywhere without my parmition?" Jinjina mishi kai ta yi alamar ta yi alkawarin ba zata tafi ba.

Sakin hannun nata ya yi tare da cigaba da magana "Before na fara kiranki a waya i have had some of your pictures that your brother sent to me last, É—in kenan, so first time of seeing your pictures i fall in love with you, i bought this my phone second day of seeing your pictures, 3 day lokacin kuna gidan uncle naku, you are together with your sisters, uncles and your brothers, prof called me on video, wen I saw you, sai na ji i can't control my self or stop my self izuwa ga kiranki, already lokacin an haÉ—a mini wayar, Prof bai katse video call É—in ba, ina kallonki na tura miki massage na farko a tsakanina dake, ina ganin action naki time É—in, to kin ji yadda abin ya fara, please don't be angry with me, kin ji my heartbeat, my pleasure part 4".

"Part 4 kuma?" Ta maimaita, jinjina mata kai ya yi alamar yah part 4. "Why part 4? Who is the part 1, 2 and the 3?" Murmushi ya saki wadda ta kara bayyanar da tsantsar kyan da Allah ya ba shi, Allah ya yi halitta a kan TRIPLETS.

Ba ƙaramin rikitata murmushinsa ya yi ba, dama tun ɗazun sai faman satar kallon shi take yi, ya haɗu ta ko'ina, ai baza ma ta iya kwatanta shi da kowa a cikin zuciyarta ba, ba zata iya fushi da shi ba, yanzu tsantsar kaunarsa ma karuwa sosai ta yi a cikin zuciyarta, sai addu'ar Allah ya mallaka mata shi take yi.

"My TRIPLETS the are part 1 of my pleasures, and then your brother, prof part 2, my uncle Hossain part 3, then you part 4, then rest". Da mamaki cikin zola ta ce "Yanzu ko kunyata baka ji ba a gaba zaka ce nice part 4". Jinjina mata kai ya yi yana faÉ—in "Yes My heartbeat, do you want me to lied to you ne? Ni bana yiwa wanda nake so karya, kai not only wanda nake so, everybody bana yi wa kowa karya, yanzu idan nace kece farincikina sama da Triplets na zaki yarda?". Girgiza Mishi kai ta yi alamar a'a. "To kingani, ba amfanin na gaya miki maganar da nasan ba zaki yarda da shi ba, wadda sai dai ki amsa mini dan jin daÉ—i na kawai, is better ka gayawa mutun gaskiya ko da zai ji ba daÉ—i, daga baya zai gane gaskiya na gaya Mishi".
Chapter 53 · 0% Book details