Sashe 18
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nan take gaya mata Areef baya a cikin hayyacinsa yanzu, Sakamakon yakar wanna kunguya ta matsafan da aka sanya shi a ciki, to abin sai a hankali, idan ta shiga Areef zai iya kasheta, su kyale shi shi kaÉ—ai É—in dai.
A tsorace ta tambayeta shin ko Areef ɗin zai sami lafiya. "Rimsha Areef da izinin Allah ya ma sami lafiya ya gama, Kinga wannan yaki da ake yi, azzaluman nan sun tattaru ne a jikin Areef ɗin ne, dan su yi garkuwa da shi ko zasu tsira, amma hakan ba zai yi wu ba, yanzu dai sun yi nasarar shiga jikin nasa, amma fa nan da ƴan mintuna dole su sake shi ko suna so ko basu ko, domin Saif ya baza malamai ta ko'ina suna yi masu sauƙar Al Qur'ani mai girma tare da addua'o'i, ai dolene ma su rabu da Areef, ko da kuwa uwa ɗaya a ka Haife su".
Shiru Rimsha ta ɗan yi, kafin nan ta miƙe da sauri ta nufi sama tana faɗawa Malika bari ta je ta yi sallah saboda Areef, bari ta yi nafila ita ma ta rokar mashi Allah da ya kuɓutar da shi lafiya, tsabar sauri bama ta jira amsar Malika ɗin ba, a hanzarce ta faɗa cikin bedroom nata.
Kai tsaye toilet ta nufa, bayan ta É—auro alwala ta fito sai ta shiffiÉ—a dadduma tare da sanya hijabi ta tada Sallah.
Ita kuma Malika miƙewa ta yi ta fito harabar gidan, ƴan dube dube ta yi kafin ta ɓace ɓat.
A ɓangaren gidan Abbi kuwa.
kamar yadda Abbi ya faÉ—a haka aka yi, tun safe suka shirya suka É—auki Hanan suka nufi Katsina, Aunty da ita da Hjy Batula kuma, suka shirya Jelly suka nufi gidan babban yayansu, wato dai Abban Imran.
Hjy Batula ce ta ja motar, Aunty na gidan gaba ita kuma jelly tana gidan baya, sai taunar chewing gum take yi, Hjy Batula ta ce ta yasar da chewing gum É—in nan, kada ta kuskura ta shiga gidan surukuwa da shi, ta ce to sai sun isa gidan sarakuwar tukun nan ta yasar.
A waje suka yi parking na mota, suka fito, Aunty ta riƙo hannunta, ita kuma Hjy Batula tana ƙoƙarin ɗage glasa ɗin motar da sauransu, da Motar Irfan suka zo.
Bayan ta fito ne suka nufi cikin gidan, mai gadi bai hanasu shiga ba, domin ya ga kamannin Hjy Batula da Abba. Ciki suka wuce, har lokacin jelly bata yasar da chewing gum ɗin ba, ta dai ɓoye a bakinta, ta daina taunarsa.
A palo suka isko Ammie zaune tana kallo a Tv, bakinsu É—auke da sallama suka shigo, jin sallamarsu yasa ta juyowa domin taga suwaye ne.
Ganin Hjy Batula yasa ta É—aure fuska sosai tana binsu da kallon banza. Ita kuwa jelly tun da suka shigo take karewa palon kallo, baki abin magana ta kasa hakuri sai da ta ce "Gwaggon Batula wannan wani irin gidan kazanta ne haka? Jibi ko'ina da datti, amma dai masu gidan guragu ne basu da kafa da hannu ko?". Aunty ce ta rufe mata baki tana girgiza mata kai.
Hannunta ta sanya ta zame na Auntyn daga bakin nata. "Ke Aunty gaskiya ce baki so na faÉ—a ko me? Wlh gidan nan gidan datti ne, buhun datti ne masu wannan gida, jibi kura wajen Tv nan, kuma a haka a ka kunna Tvn? Aunty wlh datti cuta ce, kazanta tana mugun yi wa lafiya Illah".
Dafe kai Aunty ta yi domin tasan kaÉ—an ma ta gani in dai jelly ce, ita kuma Hjy Batula kasa kasa ta ce mata ta rufewa mutane baki.
Ammie dai sai binsu da idanunta kawai take yi, bata ce masu ko sannu ba, bata yi masu iso ba, dan ra'ayin kansu, suka iso ciki.
Suna isowa idanun jelly suka sauƙa a kan Ammie ɗin. Zuba mata idanu ta yi tana kallonta, sanye take da wani dogon riga irin na barcin nan, kayan duk datti, sai ta yi kama da mai aikin gidan ne ba matar gida ba, wata mai aikin ma, ba zata iya zama cikin uban datti haka ba.
Zama suka yi a saman sofa ba tare da an basu izni ba.
Sanin hali yasa Hjy Batula bata tsaya yin wani dogon turanci ba, faka faka kawai ta sanar da Ammien abin da yake tafe da su, ai kuwa wani mahaukacin tsalle Ammie ta yi, ta dire ta ce idan akwai wanda ya isa ya yi wa ɗan ta aure shegiya take, uban mutun ya yi kaɗan, ai ba uban da ya ɗauka mata cikin ɗan ya yi mata naƙuda, ya rene mata shi har ya girma, dan haka kuma babu uban da ya isha ya yi wa ƴaƴanta abin da bai yi mata ba, wlh tun suna shaida juna su fitar mata da jelly daga cikin gidan nan, idan ba haka ba ta sumar da ƴa, yanzu ta sanya su suyi danasanin saninta a rayuwarsu.
Aunty kam ta tsorata dan bata son hayaniya, Hjy Batula kuwa already ta san hali, dan haka ko É—ar bata yi ba, ita kuma Jelly wani irin É—aure fuska ta yi, ba mutunci, rai a jagule ta fara magana.
"Wannan mai kama da sumammiyar akuyar fa? Gwaggo Batula wace ce ita da har zata ce a fitar da ni daga cikin gidan nan? Ina cewa shi ne gidansu yaya Imran? Kuma wannan Æ´ar dattin ba mai aikinsu ba ce? Ko dai a wannan gida masu aiki ma suna da damar yin magana da power kamar haka ne?".
Shiru Aunty ta yi dan tasan halin jelly fin haka ma yi zata yi, dama bata ce zata mari Ammie ba ai an yi sa'a. Ita kuma Hjy Batula buge mata baki ta yi kasa kasa ta ce "Ke Jalila surukarki ce fa, mahaifiyar Imran ce".
Turo bakin nan ta yi kamar biro. "To gwaggo Batula dan ita ta haifi yaya Imran sai ta ce bata son ganina a fitar da nine? To ni dama waye ya ce ma ta so ni? Ni ma ai ba sonta nake yi ba, kuma ba zan zauna ma a gidan nan ba domin daddy ya taɓa gaya mani she is a wicked"
Kalubale gareku iyaye, bai kamata kuna zagin wata ko wani a gaban yara ba, domin baku san wace alaÆ™a ce zata haÉ—a Æ´aÆ´anku da waÆ´an nan mutane ba, gaba tafi baya yawa, wannan haka yake, yanzu dai ga shi nan, daddynta yana zagin Ammie a gabanta, ita kuma ta riÆ™e, a kwana a tashi ga Ammie ta zama surukuwarta, ku sani duk son da Iman yake yi mata, yafi kaunar farincikin mahaifiyarsa sau dubu, ba zai taÉ“a yarda ta zagi mahaifiyarsa ba, a kan hakan ana iya kwance wannan aure ma baki É—aya, to shawara dai ta rage gareku iyaye, ni dai na yi nawa, sai ku kuma ku gyara, dan nasan wannan matsala ce da take damun mu, sai ki ga uwa ta zauna tana zagin makontan ta a gaban Æ´aÆ´anta, kuma ana waje guda, komai ka iya faruwa, ta yi wu É—an maÆ™otan ya zo neman aure gidan naku, to ya kenan? ƳaÆ´anki ba za su ga uwar da daraja ba, sai ki ga kwana biyu aure ya mutu, Æ´a ta raina uwar miji, me ya kawo hakan? Wata kila ta taÉ“a jin kin ce uwar mijin Æ´ar datti ce ko Æ´ar kaza Æ´ar kaza, babu namijin da zai yarda a raina uwasa da Æ´an uwansa, wannan kuskure ne babba muke yi, ya kamata mu gyara.........â¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
E7-8
Turo bakin nan ta yi kamar biro. "To gwaggo Batula dan ita ta haifi yaya Imran sai ta ce bata son ganina a fitar da nine? To ni dama waye ya ce ma ta so ni? Ni ma ai ba sonta nake yi ba, kuma ba zan zauna ma a gidan nan ba, dan daddy ya taɓa gaya mani she is wicked".
Sosai Hjy Batula ta buge mata baki da ɗan karfi, kuka ta saka masu, har da birgima a kasa, taɓe maki Ammie ta yi tana ganin ikon Allah, wai wannan mahaukaciyar ce matar ɗan ta? Ta tambayi kanta da kanta.
Ita kuwa Aunty a cikin zuciyarta tana jin da ace Mummy Abla ta kyaleta, bata daketa ba, yanzu ga shi ta sake kwaɓe masu komai.
Tsawa Ammie ta daka masu akan su fice mata daga gida tun ransu bai ɓace ba. Waya Hjy Batula ta ciro wayarta ta kira Abbi dan ta sanar da shi abin da yake faruwa, bugu ɗaya ya ɗauki kiran, ba ɓata lokaci ta sanar da shi ga abin da jellyn ta yi, ita kuma Ammie ga reply da ta bata akan ba zata karɓi jelly ɗin ba.
Shiru Abbi ya ɗan yi kafin ya yi magana kasa kasa dan kar daddyn Jelly ya ji, yasan hakinsa sarai idan ya ji zai ɓata rai ya ce an wulaƙanta mashi ƴa, hakan yasa ya yi magana kasa kasa dan zaman lafiya yake so ba faɗa ba, umarni ya yi masu a kan su dawo da jelly ɗin gida, idan suka dawo daga Katsina za su kira Imran, sai su san abin yi.
To ta amsa da shi, ta yi wa Ammie sallama tare da riƙo hannun jellyn ta miƙar da ita suka nufi waje, wani irin matsiyacin kallon banza Ammie ta bisu da shi, sai da suka ƙurewa ganinta ta koma saman sofa ta zauna tare da ɗauko wayarta.
Number Imran ɗin ta fara laluɓa dan ta kirashi, ta bashi umarnin akan idan ma ya auri jelly to ya saketa ko ta tsine mashi albarka, sai dai kash a kashe ta sami number, ta ji babu daɗi sosai, saman sofa ta ɗaura wayar ta cigaba da kallonta.
Su kuma bayan sun je mota, sosai Hjy Batula ta yi wa Jelly faɗa tare da nasiha, ta kara mata da cewa, in dai bata girmama Ammie ba, to tabbas yaya Imran ba zai taɓa sonta ba, zai dai'na kulata, zai yi watsi da ita, domin yana Kaunar mahaifiyarsa shi ma, shiru ta yi tana sauraron Hjy Batula tamkar wata mumina, yadda kasan an mata sauƙar karatun Al Qur'ani mai girma a kanta, tsit ta yi, sai da mummy Abla ta gama nasihar, ta tada mota dan su tafi.