← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 121

Sashe 85

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cool murmushi ya saki yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya, sai yanzu ya ji daÉ—i a ransa, shiyasa yake bala'in kaunar uncle Hosain É—in nan, duk yadda zai bi ya faranta mishi rai ya sani, yana kula da shi ba É—an kaÉ—an ba, yana son farincikinsa sosai tamkar kaninsa na jini. "To shikenan Uncle zanje wajen Abban nata gobe In Sha Allah". Okey daddyn Rimsha ya amsa mishi da shi, daga nan suka shiga hirar duniya abinsu da kuma kewar juna, yana yi yana karawa Aseef É—in karatu, Aseef da daddyn Rimsha sai Allah, suna matikar kaunar junansu ba kaÉ—an ba.

A ɓangaren Rimsha kuwa, Kitchen ta nufa, hannunta ta wanke kafin ta ɗauki abincin, ga mamakinta yau da ta cewa Mark sannu ya ce mata Okey, tambayar kanta ta yi to ko dan ta jima bata shigo Kitchen ɗin bane yasa ya amsa mata yau kuma? Oho mishi mutun kamar wani aljani, daga shi har ogan nasa baka taɓa gane musu, kamar waƴan da ake pappasu, yau ka gansu fari, gobe kuma baki, sai ma ka rasa gane ina ne alkiblarsu dan bakin hali. Duk wannan masifa fa a cikin zuciyarta take yin shi, Mark na kona mata rai da abin da yake yi matan nan, dan iskanci yau ka gan shi fari, gobe kuma baki, ji take kamar ta yi ta tsitsinkawa ɗan banza mari har sai wannan farar ɓul ɓul ɗin kumatun nasa sun yi jawur kamar tumatiri ruɓaɓɓe ko zata ji daɗi. Shi dai ko kallon in da take ma bai yi ba, kawai yau en amsawar ne suka zo shiyasa ya ce mata okey ba tare da ya kalli in da take ba.

Wucewa ta yi zuwa bedroom É—in Lion, a bakin kofa ta tsaya ta yi sallama, can kasa kasa da ta kasa kunne ta ji ya amsa kamar baya son buÉ—e baki ya yi magana, kutsa kai ciki ta yi tana mai jin kirjinta na dukan uku uku, a in da ta saba ajiye mishi, nan ta nufa ta ajiye tare da zama, ta wutsiyar idanunsa ya kalleta.

Yau dai da zamanta a wajen bai fi minti biyar ba sai ga shi ya miƙe ya nufota, gefenta ya zauna a in da ya saba zama kenan, cike da kasada da tsoro ta ce mishi "Good evening". Bai amsa ba amma dai ya gyaɗa mata kai, da yake tana duƙe ba kallonsa take yi ba, sai bata san ya yi hakan ba, abinci ta fara zuba mishi, kamar dai yadda ta saba, bayan ta kammala ta tura mishi a gabansa, spoon ya ɗauka ya fara ci.

Shiru ta zauna tana ɗan satar kallon kyawawan fararen kafafunsa da ya lanƙwashesu dan yin zaman cin abinci ta sunnah, wato kamar yadda annabi yake yi kenan. Can kasa kasa kamar a mafarki zazzakar muryarsa ya daki dodan kunnenta a kan ta miƙo mishi wayarsa da laptop nasa, okey ta amsa tare da miƙewa a nitse.

Tana miƙewa ya ɗago dara daran blue eyes nasa ya bita da kallo, ɗauko laptop ɗin ta yi tare da wayar, har lokacin bai kawar da kallonsa a kanta ba, zubawa face nata idanu ya yi yana son yaga action ɗin da zata ɗauka lokacin da zata kalli home screen na laptop ɗin.

aura kaɗan ta saki laptop ɗin ya faɗi kasa ya tarwatse lokacin da idanunta suka sauƙa a kan screen ɗin, ta sha ruwan mamaki sosai ganin wata kyakkyawar farar baturiya mai kama da daddynta sak babu maraba, ba dan ta ganta da gashi ba ma, da sai ta ce wannan daddynta ne, sun yi kama sosai over, tsayuwa ta yi tana kallon matar ta manta ma da shi ya aiketa, ta mance ma da a ɗakinsa take, ga shi dai matar ba babbar mace bace bare tace ko yar daddynta ne ko wani abu, a yadda take ganin matar ba zata wuci 28 years ba, da alama ma budurwa ce, tariyo fuskar ƴan uwan daddynta da ta sani gabaɗaya ta fara yi a cikin ƙwaƙwalwarta, duk wadda ta tuno sai taga baya kama da wannan mata sosai sai daddynta, ba dan wannan mata ta fi Jehan shekaru ba, da sai ta ce Jehan ce, dan kuwa babu maraba. Ganin wannan ta shiga duniyar tunani ba zata kawo mishi laptop ɗin bane yasa ya yi mata gyaran murya tare da ɗauke kallonsa daga kanta.

A hanzarce ta ɗago tana kallonsa, jikinta duk ya mutu, da sauri ta kariso wajen nasa tare da zama kafin ta miƙa mishi laptop ɗin, hannu yasa zai karɓa hannunsu ya goge na juna, cikin sauri ta sake mishi dan wani irin shock da ta ji, shi kuwa ko a jikinsa ya karɓa ya ajiye a gefensa wajen da ya saba ajiyewa, kasa kasa ya ce ta bashi ruwa, a hanzarce ta zuba ta miƙa mishi, still ya zo karɓa hannayensu ya sake haɗuwa, cikin sauri ta sakar mishi cup ɗin, shi kuma bai kai ga riƙewa da kyau ba, ruwan gabaɗaya ya zube mishi a saman cinyarsa, gently ya ɗago da idanunsa ya sauƙe a kan face nata dan yaga wai me matsalar yarinyar nan ne? Dan hannunsu ya taɓe na juna take haukace mishi haka.

Daidai lokacin da ya ɗago idanu, ita ma ta ɗago nata dan ta kalli wani irin action ne a kan face nasa da ta zubar mishi da ruwan, yau a karo na biyu suka kalli juna ido cikin ido, da sauri ta yi kasa da kallonta, shiru ya ɗan yi kafin ya ce da ita ta miƙo mishi hannunta bari ya gani, a razane ta ɗago kanta, nan take idanunta suka cika da kwallah, addu'a take yi Allah yasa ba wani hukunci zai yi wa hannun nata ba dan ta zuba mishi ruwa a jiki, shi kam tambayar kansa yake yi wai me matsalar yarinyar nan ne? Daga ya ce ta bashi hannu har ta fara kwallah, daga hannunta ya taɓe nasa ta zubar mishi da ruwa a jiki, ba dan akwai abin da yake son sani a tattare da ita ba ai da ya bata hukunci mai tsanani, yariya kamar ba lafiya take ba.

Jikinta har ya fara kerma ta miƙo mishi hannun nata tare da runtse idanu, nan take hawayen da suka cika mata idanu suka gangaro saman kuncinta, kallon second biyar ya yi wa hannun nata kafin ya kai nashi hannun ya kama natan, waro dara daran sleeping eyes nata waje ta yi, jujjuya hannun nata ya yi kamar mai neman wani abu, ga yatsun nata zara zara da su sak irin na Areef, ya ɗan yi mamaki ganin irin ƴatsun Areef a tattare da nata, amma bai wani damu ba, dan ba yadda Allah baya halittar bawa, shi dai ya riƙe hannunta ne dan ya ga wai me matsalar ta dan hannun nata ya ɗan taɓa nashi har take yi mishi ɓarna, baya son hukunta ta, dan haka baya son ta yi mishi ɓarna ta ɓata mishi rai, baya son abin da zai dakatar da shi daga binciken da yake yi, shiyasa zai kawar da duk wani abin da zai ja ta yi mishi wani ɓarnan da ba daidai ba har ya hukunta ta.

Almost second 30 yana riƙe da hannun nata yana jujjuyawa kafin daga bisani ya saketa tare da maido da kallonsa zuwa saman face nata, da sauri ta yi kasa da idanunta, "Dama ganganci yasa kike yi mini ba daidai ba?" Shi ne abin da ya faɗa, girgiza mishi kai ta yi har lokacin tana hawaye, "To me matsalarki dan hannunki ya taɓa nawa zaki zuba mini ruwa a jiki?". "Babu komai". Ta bashi amsa, shiru ya yi daga nan bai sake magana ba, sai ma miƙewa da ya yi ya nufi dressing room nasa dan ya canza kaya, bin shi da kallo ta yi tana mamakin wai shin yau wace iriyar sa'a ne taci a rayuwarta da har ta yi mishi laifi bai hukunta ta ba, ita da ko bata yi laifi ba in dai ta biyo hanyar da aka yi mishi laifi a wajen to sai ya hukunta ta, anya yau lafiya yake kuwa? To ko dai mala'ikun rahma da imani sun rokawa zuciyarsa samun imani da rahmar ne? Ta tambayi kanta, bata san akwai abin da yake nema a tattare da ita bane yasa bai yi hakan ba, yo idan ba dan haka ba ai da wani zance ake yi yanzu.

Tana zaune a wajen har ya fito, gently tamkar baya son motsa laɓɓansa ya furta ta kwashe kayan abincin ta fitar ta dawo ta gyara mishi gado da kuma ɗakin baki ɗaya, ɗan zaro idanu ta yi cike da mamaki, ita da ko yadda ake gyaran ma bata iya ba, ga komai na ɗakinsa sai an bisu daki daki, idan kayi mishi kuskure ɗaya ka shiga uku, amma ya zata yi ? Ai dole yau ta zo ta zage dantse ta yi mishi.

A hanzarce ta kwashi komai ta fitar, shi kuma saman sofa ya koma ya zauna tare da jawo laptop nasa, zarginsa ya tabbata gaskiya, tun daga irin kallon da ya ga Rimsha tana yi wa wannan mata, to wace ce wai? Mu dai kasance a tare zaku san koma wace ce. Bai taɓa ɗaga idanu ya karewa daddynta kallo ba, idan suna shirme shi da Aseef lokacin da Aseef ɗin yake Washington DC ma, sai dai ya kunna yana jinsu yana wani abin, ba zama yake yi yana karewa face nasu kallo ba, amma duk da haka ya fahimci wannan mata tana kama da daddyn Rimsha ɗin sosai, shiyasa ya yi wa Rimsha hakan dan ya tabbatar, dole daddyn Rimsha yana da relationship da wannan matar, cigaba da aikinsa ya yi, hoton daddyn Jelly ya fitar yana bincike a kansa, da kuma yaushe ne suka rabu da daddyn Rimsha ɗin, dan yanzu case ɗin daddyn Rimsha yake da waƴan da suka zauna da shi kafin ya rabu da family'nsa, dan yana son gane ainahin me ya rabasu har haka, kuma kun san daddyn Jelly ya zauna da daddyn Rimshan kafin daga baya su rabu.
Chapter 85 · 0% Book details