← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 121

Sashe 37

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ASEEF abin da nake so da kai kana jina?" Gyaɗa mishi kai ya yi ba tare da ya yi magana ba. "Yauwa, musulmi ba zai taɓa zama cikakken musulmi har ya shiga aljanna ba sai yana kiyaye harshensa, Annabi da kansa ya yi wa duk wandan ya kiyaye abu biyu zuwa uku alkawarin shiga aljanna babu fashi, na farko, ka kiyaye abun dake tsakanin hakwaranka na sama da na kasa, wato harshe kenan, idan har kana iya kiyaye harshenka, to ana sa ran ka samu babban rabo, abu na biyu ka kiyaye abun dake tsakanin kafafunka, wato al'auranka, muddin ka kiyaye gabanka baka aikata zina ba, muna yi maka kyakkyawar zaton da samun Rahmar Ubangiji, abu na uku gani, ka kiyaye idanunka wajen zuwa lallai sai ka leƙa abin da ya zama haramun, misali kallon fina finan banza da tsiraicin wani, mutane biyu kawai Allah ya yafewa da su kalli tsiraicin juna, mata da miji, bayansu duk wanda zai zo a baya tofa akwai matsala, uwa tana iya yi wa ƴaƴanta wanka suna yara ta kalli tsiraicin su kafin sukai munzalin haramta ita ma a gareta, idan ba ya zama dole ba, Aseef ina son ka san wani abu guda wadda duk wanda ya sanya hakan a ransa dole ya tuba ya koma ga Allah, ina son ka saurareni da kyau, Sahabban annabi bayan guda koma da Allah ya yi musu albishir da gidan aljanna tun a duniya, tofa sauran manyan sahabbai da suka rage ASEEF har wa yau bamu san menene makomansu ba, dayawa daga cikinmu muna yi musu kyakkyawar zato, amma fa bamu san aljanna zasu shiga ko wuta ba, Ubangiji bai bawa kowa daman sanin aikinsa ya karɓu ko bai karɓu ba, ka kwana kana sallah, kana azumi, zakka, hajji, ba abin da baka yi a manya manyan ayyuka Alkhari, sadaka, amma kada ka kuskura ka saki jikin cewa wannan aikin naka tana karɓuwa, domin me? Saboda baka sani ba wata kila akwai in da ka tabka babban kuskuren da ya shafe dukkan ayyukan alkharin nan naka, idan bawa yana da hankali bai kamata ya saki jiki da duniya ba, saboda baka da tabbacin abin da aka turoka a duniyan ka yi shi mai kyau kuma an karɓa, Aseef muddin aikinka bai karɓuba ka shiga uku ka lalace, bari kaji Annabi da kansa akwai lokacin da Allah ya sauƙar mishi da aya ya daka mishi warning akan yana shiga abin da bai kamata ya shiga ba, a lokacin sai da annabi ya yi furfura saboda tsananin shiga tashin hankali na abin da ya faru, to shi kaga Allah yana son shi da Rahma har hakan ta faru, zaka iya zuwa kana tapka babban kuskure da zai goge duk wani aikinka ba tare da ka sani ba, Sahabban annabi ban cire maka ko ɗaya ba, harta waƴan da suka san makomansu ɗin, waƴan da suka san aljanna zasu tafi irinsu Sayyidina Abubakar, Omar, Usman, Ali, ɗalhatu binu Ubaidullahi, abu ubidu binu zarrai da sauransu, su kansu idan aka kira lahira jikinsu kerma yake yi, kuka suke yi suna kara neman gafara da sassauci wajen ubangiji, wannan kawai bai isa yasa bawa ya kasance cikin tashin hankali a kullun ba? Manyan Sahabban da suka san yes aljanna zasu tafi, suna kuka idan suka ji annabi ya fara magana a kan lahira, to mu da ko rabin su a aikin Alkhari bamu yi ba, sai kaga bawa ya samu waje ya kwanta ana kiran sallah yana zaune tamkar wani kurma, ya ilahi ya lillahi, wlh bai kamata bawa ya zauna cikin kwanciyar hankali har ma ya yi tunanin cutar da wani ba, mutuwa gaskiya ce, tashin alkiyama gaskiya ce, yau ina kakaninmu? Wasu ina iyayenmu? Ina kannenmu? Wasu ina yayyunmu? Idan ka juya kaga matsalar dake a kewaye da kai ma kawan ya isa ya sanya ka kara jin tsoron Allah ka girgiza, ya isa ya sanya ka kara komawa ga Allah dan samun rabauta, kafin Annbi ya rasu, da Sahabbai suka tambaye shi ya Rasulullah yaushe za'ayi tashin alkiyama, ya ce da su sanin gaibu sai lillahi, Allah ne kaɗai ya barwa kansa sani, amma akwai misali da Ubangiji ya yi mini, zan yi muku shi dan ku kotanta, mikar da yatsun hannunsa gabaɗaya ya yi, kun dai san yatsun hannu ɗaya ta fi ɗaya, sai ya ɗauki babba ta tsakiya da kuma manuniyar yatsa, ya mikar da su sosai, ya ce da sahabbansa abin da ta regewa duniya ta tashi bai wuce ɗan wannan fifikon dake tsakanin yatsarsa ta tsakiya da kuma manuniya ba, ku duba ɗan ratan dake tsakanin yatsunnan, a lokacin annabi yace abin da ta ragewa duniya kenan, bare kuma yanzu da ya yi shekara 1445 da yin wannan maganar, to ku lissafa abin da ya saura kenan, a lokacin da Sahabbai suka ji wannan magana, hankalinsu ya yi mummunar tashi, masu kuka suna yi, annabi ya yi ƙoƙarin kwantar musu da hankali ta hanyar nunawa su sayyidina Abubakar cewa su fa ƴan aljanna ne, amma ina sunki yin shiru, suka ce idan ba sun ga kansu a cikin aljanna ba, sun karɓi takardansu da hannun dama, baza su taɓa daina kuka suna neman gafara da sassauci wajen ubangiji ba, ɗan adam ako da yaushe mai kuskure ne, tana iya yiwuwa su je su aikata wani abin da zai shefe musu aikin alkharinsu na baya, to su da suke Sahabbai ma kenan, ina ga mu da ba ɗaya kanwar biyu? Sai kaga mutun sai wani jiji da kai yake yi yana faɗi kamar ba nan da ɗan lokaci kaɗan cikin kasa zan koma ba, jama'a duk wasu masifa da suka zo a cikin Al Qur'ani mai girma da hadisan Manzon (S.A.W) da suke nuna almomin tashin alkiyama ne, to wlh sai bayyana suke yi, me ba'ayi yanzu? An maida zina abin kwalliya! An mai da luwaɗi gasa! An mai da lesbian sana'a! Saɓon Allah ya zama har tinƙawo da shi ake yi! Uba ya nemi ƴa ya kwanta da ita, yaya ya yi wa kanwarsa ciki, makwabci ya yi wa ƴar makwabcinsa ciki, mata su kashe mazansu a kan shirmen banza, ba'a ɗauki ran a bakin komai ba, matan aure suna zina, Maza na cin amanar matansu, namiji ya auri yarinya kuma ya zagayo ya yi wa kanwarta ciki, wasu ma tamkar a garin dabbobi suke, ka auri yarinya sannan ka kwanta da uwarta, ya ilahi ya lillahi, me ba'ayi?! Cutar mutane an mai da shi yanzu tamkar wani ilimi, har koyan danfara ake yi, karya na gudu kana bin shi a guje sai ka kamo shi, dole dole sai anyi karya, zalunci da hasada na gudu kuna binsu ku kamo su, dole dole sai an zalunci jama'a, kashe mutane kamar kiyashi ya zama contract! Gasa ta gina manya manyan gine gine a duniya ta bayyana, wadda annabi da bakinsa ya faɗa tana daga cikin manya manyan almomi na tashin alkiyama, masifu kala kala sai bayyana suke yi, shi kansa wannan faɗa ta yahudawa da musulmai ya zo mana a cikin Al Qur'ani mai girma? Kafin tashin Alkiyama sai anyi shi, duk wasu alamomi sun bayyana, jama'a muji tsoron Allah, mu tsaya tsayin daka dan gina lahirarmu, bai kamata hankalinmu ya kwanta mu saki jiki da duniya ba, har sai ranar da muka karɓi takardanmu da hannun dama, mu lizimci yin istigifari dan idan munyi laifi ma Allah ya yafe mana, a kowace rana ku rinƙa tuna mutuwa fiye da yadda kake tunanin abinci, dan mutuwa tafi abincin saurin zuwa, idan kwana ya kare ko tafiya kake zaka tsallaka babbar titi sai an zare ranka, second ɗaya mala'ika azarailu baya karawa bawa wajen zare rai, ko a ina yake kuwa, shi kuma abinci kana iya jira har sai an kammala, to dan haka mu lura, mu tuba mu koma ga Allah, zunubanmu ya yi yawa, Allah gafurun rahim ne, amma ku sani a yanzu ne kuke da damar tuba kafin lokaci ya kure, a lahira ko kabari ba'a tuba, iya duniya Allah yake karɓar tuba".... Yana magana yana hawaye bibbiyu, duk dakiyar zuciya irin na daddyn Rimsha sai da ya yi hawaye ba kaɗan ba, haka zalika shi ma Aseef, paka motar ya yi a gefen titi tun lokacin da daddyn Rimsha ya fara maganar, ya kifa kansa da jikin steering motar, hawaye yake yi sosai, wani na bin wani, duk sai ya ji duniyar ma ta ishe shi, ya ji jikinsa gabaɗaya ya mutu, me bawa zai nema a duniyar nan da ta wuce lahirarsa? Me zai tsayar da bawa yin wasu shirme a duniyar nan? Ya ilahi ya lillahi, gaskiya duk wanda ya zo duniya, ya mutu ya tafi wuta to tabbas shi ya so, shi yaga dama, kuma ya zama babban mai asara number ɗaya a duniya, dan Allah ya bamu lokaci da kuma dama, Allah Arrahaman ne, mai rahma a kan bayinsa, tabbas wannan hakane, Allah ne kaɗai zaka yi babban laifi ya kuma baka damar tuba ka koma gare shi, ka sake yi ya sake baka damar tuba, duk dan ka samu rahmarsa, ba wanda zai yi wa bawa haka sai mahaliccinsa, wani ma nan a unguwarku idan yana jin haushinka, haka kawai sai ya ɗauki gaba da kai ba gaira ba dalili, idan kayi kuskure yi mashi laifi kaɗan, to ka shiga uku, ba zai taɓa yafe maka ba, sai ya ɗau fansa, kunga ya tabbata idan ka mutu ka shiga wuta kai kaso.

Sosai suke kuka duk cikinsu babu mai iya rarrashin wani, sun jima a haka kafin Musharraf ya É—auki robar ruwa ya fita ya wanke fuskarsa ya dawo.

Yana dawowa ya hau rarrashin Aseef, da kyar ya samu ya yi shiru, sai shessheƙar kuka tare da ajiyar zuciya yake sauƙewa, idanuwansa sunyi jawur kamar wuta, abinku da farar fata, har wani ja kumatunsa ya yi, tamkar wadda a ka wawwankawa marika.

Sun É—auki almost 1 hour a wajen kafin su dawo daidai, kunna motar Aseef ya yi suka nufi in da zasu je, wato white house.
Chapter 37 · 0% Book details