← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 121

Sashe 39

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai damu ba ya ajiye wayar a gefensa ya ce zuwa anjima zai sake kiranta. Bai kai karfe 10 ba barci ta yi awon gaba da shi ba tare da ya shirya ba.

Can cikin barci, har tsakiyar kansa ya tsinkayo ringing É—in wayar tasa, É—an motsawa ya yi tare da É—an juyawa kaÉ—an, kira ta farko ta katse ta biyu ta sake shigowa, a hankali ya waro idanunsa yana kallon saman É—akin, idanun nasa sun yi jawur dasu saboda barci bai ishe shi ba.

Miƙewa ya yi tare da salatin annabi kafin ya ɗaura da addu'ar tashi daga barci, a hankali ya zura hannu ya ɗauko wayar tasa, ya kawota daidai saitin fuskarsa.

Ganin number daddyn Jelly ne yasa ya É—an washe idanunsa tare da kai kallonsa kan time dake jikin wayar, karfe shabiyu da rabi, É—an zaro idanu waje ya yi, kafin ya yi picking call É—in kiran ta katse.

A gaggauce ya bi kiran, bugu ɗaya ta ɗauka, manna wayar a kunnensa ya yi, ban da sautin kukanta babu wani abin da yake tashi daga ta cikin wayar. Hankali a tashe ya miƙe zaune tare da yaye bargon da ya lulluɓa, bawan Allah har haɗe kalmomi yake yi wajen tambayarta me yake faruwa, me aka yi mata? Kara rushe mishi da kuka mai sauti ta yi, har da shessheƙa.

Bai san lokacin da ya diro kasa daga saman gadon ba, cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa yake kara tambayarta menene ya faru? Ina daddy yake?, Ina su Abbi? Wani abu ne ya same su?.

Cikin kuka ta ce "Yaya Imran ni kazo yanzun nan, idan ka ɗan jima kaɗan mutuwa zan yi". "Subhanallah to naji zanzo yanzu, amma menene yake faruwa? Ina daddy? Wani abu ya same su ne? Idan baki gaya mini ba ba zan iya tuƙi ba WLH, hankali ba zai taɓa kwanciya ba".

Kara sautin kukan nata ta yi tana faÉ—in "Kai dai kazo yanzu mana, idan ba haka wlh zan mutu, wayyo mummyna, nashiga ukuna na lalace".

A firgice ya fita daga É—akin, ko kashe wayar bai yi ba, tunaninsa kuma bata bashi cewa ya kira Abbi ko zai san me yake faru ba, ta rigada ta kiÉ—ima shi sosai, Bawan Allah. Har ya kai tsakiyar palon sama, sai ya juyo ya dawo dan ya É—auki key É—in motarsa.

A gaggauce ya fice daga ɗakin bayan ya ɗau key ɗin, kai tsaye bakin gate ya nufa, gateman yana zaune a bakin aikinsa, cikin fitar hayyaci ya bashi umarnin ya buɗe mishi gate, ganin yanayin da yake ciki yasa gateman ɗin ya yi wa Lion massage akan Prof zai fita kuma ga yanayin da yake ciki, da yake sam Lion bashi da nauyin barci har cikin tsakiyar kansa ya ji shigowar saƙon, sai dai bai duba ba, saboda idan baku manta ba, baya haɗa abu biyu lokaci guda, baya aikin kaza lokacin kaza, yanzu lokacin barci ne, dan haka babu wani abin da zai duba kuma.

Shi kuma Imran cikin motarsa ya wuce tare da kunnata, ganin Lion bai yi mashi reply bane yasa gateman É—in ya buÉ—e wa Imran É—in gate, saboda duk wanda yake tare da Lion yasan shirun shi ma magana ce, baya shiru babu dalili, haka zalika baya magana babu dalili, a nasu faÉ—en idan har baya son Imran ya fita zai yi musu reply da su hana shi fita, idan ya yi shiru kuma yana nufin su barshi ya fita kenan.

Kai tsaye gidan Abbi ya nufa, wani irin mahaukacin gudu yake shararawa a kan titin nan, har lokacin bai katse kiran ba, ita ma bata katse ba, tana jin duk abin da yake yi.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan, horn ya fara zubawa ba ɗaga kafa, ba ƙaramin tsorota mai gadin ya yi ba, da sauri ya taso har yana haɗawa da gudu ya zo ya buɗe mishi gate ɗin.

A gaggauce ya danna hancin motar cikin gidan, ya kasa karisawa parking space na gidan ma, a tsakiyar gidan ya paka motar tare da fitowa da gudu, Allah ma yasa ya iso lafiya, kuma da yake darene babu motocin sosai a kan hanyan, da rana ne sai Allah kaɗai yasan me zai faru a irin yadda ya fiton nan, ga uban gudu da ya rinƙa shararawa.

Kai tsaye cikin palo ya nufa, da mamakinsa sai ya ga kofar palon a buɗe, ba ɓata lokaci ya afka ciki kawai, sai haki yake yi bawan Allah.

Wani irin birki ya ja ya tsaya turus yana ganin ikon Allah, zaune take saman sofa tana shan ice cream, kayan barci ne doguwar riga zuwa gwiwarta a jikinta, a wannan daren take shan ice cream mai uban sanyin nan, ta tsantsara make up kamar ba ita ba, sai tashin kamshi take yi, ta yi kyau sosai da sosai.

Ganinsa yasa ta ajiye ice cream ɗin ta nufe shi da sauri tana faɗin "Haba yaya Imran rabon da na ganka tun yaushe?" Ta kai karshen maganar tare da faɗawa a saman kirjinsa tana turo baki. Tabbas ya yarda da maganar daddynta da yake cewa idan ka biyewa jelly, in bata kasheka ba, to zata haukata ka, yanzu wannan abin da ta yi mashi da yazo da karar kwana ai da shikenan sai dai a kwashi gawarsa, dubi yadda ya rinƙa sharara gudu a kan hanya, ba dan Allah ya tsare ya kawo shi lafiya ba ai da wani zancen ake yi yanzu ba nashi ba, zuciyarsa sai harbawa da sauri sauri take yi, da mai ƙaramin zuciya ne ma bugawa zuciyar tasa zata yi.

A kule ya ce "Me yake faruwa kika kirani kina kuka?" Ba ko É—ar É—ar ta ce "Kewa mana, kewarka nake yi, wlh har ciwo zuciyata take yi mini, ka daÉ—e fa baka zo gidan nan ba, me nayi maka da zaka hana ni ganin fuskarka da kai kanka? Sai dai kayi ta kirana a waya ko?".

Haushi tamkar ya sakar mata mari, amma ba komai zai yi mata abin da ya fi mari zafi, ya lura idan ba mai da ita cikakkiyar mace ya yi ba, ba zata taɓa yin hankali ba, zata yabawa aya zakinta yau wlh, ba tare da ya yi magana ba ya ɗauketa suka nufi waje, bata tambaye shi ina zai kai ta ba, sai ma kwanciya da ta yi a kirjinsa.

Kai tsaye cikin motarsa ya sanyata a gidan gaba, har lokacin bata tambaye shi ba, shi ma bai yi magana ba, da gudu ya figi motar suka bar gidan suka nufi gidan Lion, matsowa ta yi ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa tana lumshe dara daran idanunta tare da shaƙar kamshin jikinsa........❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E15-16

Kai tsaye cikin motarsa ya sanyata a gidan gaba, har lokacin bata tambaye shi ba, shi ma bai yi magana ba, da gudu ya figi motar suka bar gidan suka nufi gidan Lion, matsowa ta yi ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa tana lumshe dara daran idanunta tare da shaƙar kamshin jikinsa.

Su Abbi kuwa, suna can suna barci basu san me yake faruwa ba.

Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kai hannunsa yana shafo kanta yana tuki da hannu ɗaya, rage guduwar motar ya yi dan kada a je a sami matsala.

"Yaya Imran Allah nayi kewarka fa sosai, ka kai sati baka zo gida ba, kullum sai ka rinƙa cemin zaka zo zaka zo, amma shiru, yau dan ban san in da kake bane da sai na je na same ka". Allah sarki da iya gaskiyarta take kaunarsa kamar yadda yake kaunarta, bayan daddynta shi ne mutun na biyu da yake cikin zuciyarta, shi ne ko da yaushe yake ce mata zaizo zaizo kuma baya zuwa ɗin, shiyasa yau ta yi mishi wannan tsiyar dan ta samu ganin shi.

"Haba jelly shi ne zaki yi mini irin wannan wasan? Idan da wani abin ya faru da ni fa? Kin san a wani hali na baro gida kuwa? Kin san halin da kika jefani kuwa? Kin san da ya na kariso gidan bappa kuwa? Gaskiya bai kamata ki yi mini haka ba, kuma ko da sunan wasa kada ki sake yi wa wani haka, ba iya ni kaɗai ba, kowa da kowa kada ki sake yi mishi irin wannan wasa, babu kyau, zaki iya sanya mutun ya mutu ko ya suma kin ji ko?". Ya yi maganar cikin sanyin murya, yasan yarinta ce ke damunta, kuma ya haɗu da kaunarsa da take yi, nan take ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, saɓanin ɗazun da yake jin haushinta, yake kuma jin zuciyarsa na tafasa kamar zata faso jirjinsa ta ɓullo waje.

Rungumo shi sosai tayi tare da manna mishi kiss a kumatu tana faÉ—in "To yaya Imran ba zan sake ba, amma kai ma dan Allah kada ka sake kin zuwa na ganka, idan kayi mini hakan Allah zan yi kuka".

Horn ya yi a bakin gate É—in gidan Lion yana shafa kanta, kasa kasa ya ce "Ba zan sake ba, yanzu ma aiki ne ya yi mini yawa yasa ban zo gareki ba, amma badan haka ba ai kema kin sa dole na zo wajen matata ko? Kin san fa ina masifar kaunarki, dole na kai kaina gareki farincikina". Murmushi ta fara yi mishi tana turo É—an bakin nan nata kamar na daddynta, daidai lokacin gateman ya wangale mugu gate É—in.

Cikin natsuwa ya kutsa hancin motar cikin gida, kai tsaye parking space ya nufa. Bayan ya kashe motar ne ya juyo suna fuskantar juna. "Wannan kwalliyarfa?" Ɗan turo baki tayi. "Yaya Imran dan kai mana nayi, Aunty ce ta koya mini, dama nasan idan na kiraka zaka zo ne shiyasa nayi maka kwalliya idan kazo ka gani". Ba ƙaramin daɗi ya ji ba, hakan yasa ya jawota jikinsa sosai tare da rungumeta da kyau.

"My jelly ina matukar kaunar ki, ina son ki matata, ba'a son raina nayi nisa dake ba, kullun cikin tunani da kuma kewarki nake, bana taɓa jin farinciki har sai na kalli hotonki, wai baki gani bana iya barci da daddare har sai na ji muryarki ne?" Shigewa jikinsa da kyau da kyau ta yi, a shagwaɓe ta ce "To yaya Imran ai nima kasan ina sonka ko?". Jinnina mata kai ya yi alamar e.
Chapter 39 · 0% Book details