← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 121

Sashe 109

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tsaka da tafiya Mark ya ce "Sir is seeing like this girl bata kai 19 years da suka faɗa ba, amma how comes suka ce she is 19 years old?" Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da cewa "Dukka maganganu ma da suka faɗa ai ba gaskiya ba ce, i really trust my uncle, ni nasan family'nsa ba zasu yi karya ba, na fi yin aiki da kawa zucina fiye da abin da naji kuma na gani, wani lokaci zaka ji karya kuma ka ga karya, amma shi kawa zuci gaskiya yake zayyano maka, duk abin da Jehan ta faɗa shi ne gaskiya, kawai sun juya maganar ne saboda wani dalili nasu da ban yi tunani a kan shi ba, sai dai kuma ina tunanin sun ce she is 19 years old ne dan idan an je court su yanke mata hukuncin kisa, or something like this, dole ma akwai makarkashiya a wannan case ɗin, dole shirya kasheta aka yi, da yuwuwar dama an jima ana farautarta, abune wadda yake a bayyane ga mai ƙwaƙwalwa, zai iya gane ina aka dosa, amma zan yi ƙoƙarin wajen ganin na duba case ɗin, sai dai fa zasu yi saurin kaita court, dan idan ka lura komai da suke yi, suna yin shi ne best on they are on choice, ba wai doka suke bi ba, so zasu kaita court da wuri dan a yanke mata hukunci, kuma ka zuba ido ka gani, ita kanta court ɗin zata yi saurin kula da case ɗin, za kuma ta yi saurin yanke mata hukunci, saboda an shirya hakan, a nawa ganin kamar uncle yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya aka kullah mata wannan sharrin, amma bari mu koma zan yi binciken wai shin da waye da waye ne ma uncle ya tsaya takara a lokacin da yake neman mulki, dole da sa hannun manya, akwai dai wani abin gaskiya".

"Amma sir if that is the case, i think za su yi kokarin kasheta a prison ɗin ma, because na lura yarinyar bata da tsoro ko kaɗan, idan suke je court zata iya faɗar gaskiya, kuma da alama ba zata ji tsoron barazana ba idan aka yi mata". Jinjina kai ya yi yana faɗin "Yes ba zata ji tsoron barazana ba, and then ba zata yi magana a court ba, saboda bata da hujja, kuma kasan abin an shirya mata gadar zare ne, duk ta yanda zasu yi suga bata yi magana a court ba, za su dan su rufe bakinta, kuma dai ita ma ba zata yi ba, tana da ilimi, she knew what she is doing, tasan ba'a magana a court matikar babu hujja, batun kasheta a prison kuma, ba za su yi hakan ba, saboda yin hakan da za su yi, zai iya tona musu asiri, ina da yakinin akwai abin da suke son cinmawa ne, akwai abin da suke son nunawa duniya game da uncle da kuma family'nsa, amma koma me ne zan duba na gani, ai idan sun san wata basu san wata ba, daga ta sama zan biyo musu, bari dai na bincika na tabbatar da gaskiyar ta duk da bana shayi a kan nata, amma zan duba". Shiru suka yi, Mark ya nitsa cikin nazari da tunani a kan case ɗin, shi kuma Areef yana tunani a kan kyakkyawar fuskarta mai kama da daddynta, dan shi wannan case ɗin ko kaɗan bata dame shi ba, yasan cewa dole ma sai sun saketa dan ubansu, ko suna so ko basu so, amma yana son ya bi komai ne bisa doka, baya son taka doka, ba dan haka ba ai da tuni ya karɓata.

A ɓangaren Aseef kuwa, kai tsaye cikin gida ya shiga da motarsa, dan heartbeat ta ce ya shigo, tana tsaye a window ɗakinta tana kallon shi, waya ya ɗauko ya kirata a kan ya shigo, cikin zolaya ta ce ya kalli sama, da sauri ya ɗago kai yana kallonta, cool murmushi suka sakarwa junansu kafin ta ce mishi tana zuwa, sai kuma ta katse kiran ta nufi kasa.

A palo da isko Ammie, cike da murna ta sanar mata da Heartbeat ya iso, okey ta amsa mata tare da ce mata to ya shigo mana, sai murmushi take yi ta nufi wajen nasa. Tun da ta fito ya tsareta da idanu yana kare mata kallo, sai yanzu yake ganin tsantsar kamanta da Jehan da ya baro a gida, dan shi bai san an kamata ba, Areef bai gaya mishi ba, ya ce mishi dai zai je gida ne kawai, ganin kamanninsu yasa ya kara yardanwa kansa da lallai Jehan ƴar uwar uncle ce, duk yadda aka yi akwai alaƙa ta jini, to kunsan fa kowa da yadda yake kallon mutun, shi dai Aseef ya ga kamannin Jehan da AKila, amma ba lallai ya zamana suna kama sosai kamar yadda ya gani ba, jini ne kawai da ko'ina baya ɓuya.

Sai da ta kariso kusa da motar kafin nan ya fito yana sakar mata kayatatcen murmushi, "Good morning my shagwaɓati". Ta faɗa tana Murmushi, tsareta ya yi da idanu bai yi magana ba, tana sanye da abaya mai bala'in kyau launin maroon color, ta yafa mayafin nata a kanta, kafarta na sanye da plat shoe kalar kayan nata, simple make up ta yi, ta yi kyau over.

"To me kuma kake ta wani kallona?" Ta yi maganar a shagwaɓe tana turo baki.

Nisawa ya yi kafin ya ce "Sarkin rigima, to ɗago ki kalleni" Make mishi kafaɗa ta yi tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta, "Ba zaki ɗago ba?" Kai ta gyaɗa mishi alamar e, hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, runtse idanunta ta yi tana mai jin kirjinta na bugawa da sauri sauri kamar ya ce zai yi mata wani abin.

"Shi ne kika rufe ido?" Gera ta ɗaga mishi alamar e, hannunta ya riƙo cikin nasa ba tare da ya saki haɓar tata ba "Me yasa ne kika ciki rigima?" Turo baki ta yi tana faɗin "Me yasa kai kuma ka cika shagwaɓa ne?" Ɗan rankwafowa kaɗan ya yi a kanta, kasa kasa ya ce "Wai bana ce ki dai'na turo mini ɗan bakin nan ba? Ko so kike yi na sha kaya na ne?". Cikin sauri ta waro idanunta waje sai cikin nasa, murmushi ya saki yana faɗin "To ba ga shi yanzu na sanya kin buɗe idanun ba, sarkin rigima kawai". Ya kai karshen maganar tare da sakin haɓar tata yana murmushi, wani irin harara ta masoya ta wurga mishi tare da kwace hannunta daga cikin nashi tana ƙoƙarin juyawa ta bar wajen.

Cikin sauri ya riƙo hannun nata yana faɗin "To yanzu kuma me nayi da za'ayi mini rigima? Kin san fa jiya kin saka ni ciwon kai, Allah kin iya rigima sosai Heartbeat, idan Areef yasan kina sakani ciwon kai ba zai kyale ki ba, sai ya baki punishment, sai dai ni kuma ba zan yarda ba, da a hukunta mini ke ai gara a zaneni". Wani irin shock ta ji lokacin da ya matse hannun nata a cikin nasa yana magana, buɗe tafin hannunta ya yi yana shafawa a hankali kamar mai murza mata mai, yana yi yana magana cikin kwanciyar hankali abinsa.

"Kazo muje ka gaishe da Ammie tukun nan". Tsareta ya yi da idanu yana kallon lallausan lips ɗin nan nata, har ga Allah suna burge shi, kuma yana son yi mata kiss, amma saboda ya girmama al'adun Hausawa yasa ya daure, ya jure dan farincikinta. "To ni Heartbeat ki bari mana na kalle ki sosai kafin mu shiga ciki". Ya yi maganar a shagwaɓe sosai.

"Kai ko". Ta faɗa tana kama yatsun hannunsa da yake murza mata fatar cikin tafin hannunta da shi, "Wai kai ina ruwanka da hannuna ne?" Ɗan matsowa ya yi yana faɗin "Laushinsu daɗi yake yi mini idan ina taɓawa, shiyasa nake son in yi ta shafasu". Kallon so ta wurga mishi tana mai buɗe tafin nasa hannun ta ji nasa laushin ya yake da zai takura wa nata hannun.

Bawan Allah baya wani aikin wahala, kullum yana cikin hutu, soft skin nasa ma har wani sheki yake yi bare fatar cikin hannunsa, ai ba'a magana, akwai laushi sosai da sosai, ɗan murza fatar ta yi har sai da ya furta wash, sake shi ta yi tana faɗin "Naka hannun ma ae yafi nawa laushi, amma saboda neman rigima sai ka rinƙa taɓa mini nawa ko?" "Naki ne ko nawa?". Ya faɗa yana ɗan juyar da tsayuwarsa da kyau ya dawo suna fuskantar juna da kyau da kyau.

"Innalillahi My shagwaɓati me ya sameka a kumatu? Ya naga shatin yatsun wani kuma a face naka? Marinka aka yi?". A ruɗe take jero mishi tambayoyin, ba karya marin da ɗan'sandan nan ya yi mishi ya maru, wajen ta yi jawur kamar ka taɓa jini ya zuba, da yake tun da ya shigo bai juya da kyau bane yasa bata gani ba, yanzu kuma ya juya suna fuskantar juna da kyau, hakan yasa ta gani. Bai ɓoye mata komai ba ya gaya mata abin da ya faru da kuma wanda ya mare shi, tambaya ɗaya ta yi mishi shi ne Lion ya sani, girgiza mata kai ya yi alamar a'a tare da sake riƙo hannunta yana faɗin "Ni ki dai'na maganar, ai Areef ya hukunta su, bana ma son Lion ya ji, dan nasan ba zai taɓa kyalesu ba, yanzu dai ki rufe idanunki bari na baki surprise".

Ba musu ta rufe idanun nata, komawa cikin mota ya yi, jim kaÉ—an ya fito tare da dawowa gabanta, mai gadi dai ya mayar da su kamar wasu Tv, yana kallon ikon Allah, sai kallon Aseef yake yi, yau yaga Bature, fari tas kamar madara. Zube gwiwowinsa ya yi a kasa a gabanta tare da buÉ—e wani É—an akwai mai É—auke da dankareren diamond ring, sai kyalli yake yi yana É—aukar idanu, baki mai gadi ya sake yau yana kallon American film a zahiri.
Chapter 109 · 0% Book details