Sashe 91
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dole haka ya goyata a bayansa ya bi bayansu, wasan duhu suka fara yi yana yi musu kisan ɗai'ɗai, ta kankame shi tamkar zata shige cikin jikinsa, ta lafe a bayan nasa kamar babu ita, jikinta sai kerma yake yi, duk abin da take ciki yana jinta, yana jin duk abin da take yi,. A haka ya rinƙa yi musu kisa mummuke har ya gama da su ukun dukka, ciro wayarta da ya karɓa ya yi daga aljihunsa, ya kunna wutar wayan, palo ya sauko har lokacin tana bayansa, kofar palon ya je ya rufe, maimakon ya fara rufe gate ɗin gidan, sai ya bar gate ɗin a buɗe ya rufe iya palo kawai ya koma balcony.
Gently ya ce ta sauƙa mishi a baya, kara kankame shi ta yi ita gaskiya ba zata sauƙa ba, dan bata yarda mutanen sun kare ba, sauƙo da ita ya yi, a sukawane ta kara faɗawa saman faffaɗar kirjinsa ta rungume shi sosai tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ba karya ta tsorata iya tsorata, bata yarda mutanen sun kare ba, tana jin kamar akwai wasu, kuma wasu ma zasu sake zuwa, duk tsoronsa da take ji yau sai dai ya kasheta amma ba zata bar jikinsa ba, nisawa ya yi kafin gently ya ce "To sake ni bari na ɗauko mattress sai mu kwanta". Tamkar bata jin me yake faɗa, jikinta sai kerma yake yi, yau shi ne karo na farko da wani ya taɓa bashi tausayi a rayuwarsa, a cikin wannan hali da take ciki dole ta baka tausayi, kuma tabbas ya jinjina mata, a kananun shekarun nan nata ta iya jure duk wannan bala'i da suka shiga lokaci guda, ya jinjinawa karfin imaninta, ba ko wace zuciya bace zata ɗauki abin da ta ɗauka, tana da 14 years ƴar gata uwa da uba, kamata ya yi ace yanzu tana kwance jikin mahaifiyarta tana jin ɗuminta, amma ko in da mahaifiyar tata take ma bata sani ba, tana raye ko ta mutu? Allah masani, ba ƙaramin ƙoƙarin Rimsha ta yi ba, baki ma ba zai iya misulta irin kokari da karfin imani da take da shi ba, hakan yasa bai yi mata tsawa ba, ya saɓeta a kafaɗarsa zuwa cikin bedroom ɗin na daddynta, ya yi mata uzuri sosai saboda halin da ta tsinci kanta a ciki, ga shi yau a gabanta ya kashe mutane har guda uku, kuma cikin duhu, ai dole ta tsorata, dole yau ya yi mata uzuri.
Mattress na gadon daddy ya É—auko, dan ba zai iya kwana a cikin É—aki ba, zafi ya yi yawa, ga shi babu wuta a gidan, akwai engine wuta, sai dai babu mai a cikinta. Balcony ya kawo mattress É—in ya shinfiÉ—a, tana kankame da wuyarsa taki sakinsa, har lokacin kuka mai tsuma rai take yi, sai faman sauke wani irin numfashin wahala take yi.
Bayan ya shinfiɗa mattress ɗin a kasa, sai ya koma ya ɗauko bed sheet ya dawo, bai ɓata bakinsa wajen cewa ta sauka jikinsa ya shinfita bed sheet ba, dan yasan ba zata sauƙa ba, duk yadda take tsoronsan nan ace yau ta haye jikinsa haka, shima ya san bala'in ya kai bala'i a gareta, kuma dama dole ta tsorota, ga uban duhu kamar me.
A haka dai ya lallaɓa ya shinfiɗa bed sheet ɗin, sannan ya koma ya ɗauko wayarsa tare da pistol gun da ya taho da shi suka dawo balcony ɗin, "Sauka ki kwanta to". Ya faɗa a nutse. Kada ku manta cikin harshen turanci TRIPLETS suke magana.
Ina ai ko motsawa ba zata iya yi ba, ita dai yau duk bala'i ba zata rabu da shi ba, sai dai su mutu tare, ji ya yi tamkar ya yi wurgi da ita kasan benen nan dan haushi, amma ina ba dama, dole ya lallaɓata matikar yana son ya cinma abin da yake so, bugu da kari kuma yanzu a hannunsa take, shi ya fito da ita daga gida, duk abin da ya sameta, hakkin ya rataya ne a wuyarsa, so dole ya kula da lafiyarta.
Bashi da zaɓi dole ya kwanta da ita a saman mattress ɗin, tana manne da kirjinsa kam taki saki, ta kamkame rigarsa ta gefe da gefen cikinsa, sai sauke ajiyar zuciya take yi, gabaɗaya ta ji gidan nasu ma ya fita a ranta, ta tsani gidan, ita dai ya mayar da ita wajen yaya Imran, da farko ta yi murnar ganinta a gidan nasu sosai, amma yanzu bata so.
Shiru suka kwanta yana jin saukar numfashinta a wuyarsa har barci ya É—auketa, lokacin da ya sami kwanciyar hankali dare ta tsala wuraren karfe 2 har lokacin tana a jikinsa, bai yi barci ba idanuwansa biyu, sannu a hankali ya fara jin wani irin yanayi a tattare da shi na kwanciyar da ta yi a jikin nasa, É—azun duk bai ji komai ba saboda da shi da ita duk hankalinsu ba'a kwance yake ba, yanzu ita tama yi barci, shi kuma ya sami natsuwa sosai shiyasa.
Ɗan ɗago kansa ya yi tare da laluɓar wayarta ya kunna hasken screen ɗin, fuskarta ya haske, duk ya yi jaga jaga da busasshen hawaye, anci kuka an ƙoshi. Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya juya da ita ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa dan ya sauketa daga jikin nasa, da kyar ya iya zame hannayenta daga riƙon da ta yi mishi.
Bayan ya kwantar da ita ya jawo bed sheet ɗin ta gefenta ya rufa mata tare da juyawa ya bata baya. Jim kaɗan barci ta ɗauke shi shima, ko tsoron kwana a cikin gidan bai ji ba, ga gawarwakin da ya kashe a ciki, ko da yake, dama kama su ya zo yi shiyasa bai sauƙa a hotel ba ya sauƙa a nan gidan dan ya kama azzalumai ɓata gari.
Can misalin karfe 4 na dare, karan sautin garuwar hakwaranta waje guda ne suka farkar da shi daga barci nasa, kun san dama shi bashi da nauyin barci, abu kaɗan ya yi motsi kusa da shi zai farka, rawan sanyi take yi sosai da sosai saboda sanyin asuba ya fara sauka, hakwaranta sai garuwa da juna suke yi, gabaɗaya ilahirin jikinta rawa yake yi, barci cike da idanuwansa sosai, da kyar ya warosu a kanta, lokacin kuma hasken wata ya ɗago sosai, shiyasa ma sanyin ta yi yawa, juyawa ya yi gabas da yamma babu wani abin da zai sake rufeta da shi, ba zai iya miƙewa zuwa cikin ɗaki ba, dan wani irin azababben barci dake damunsa, jikinsa sam babu kwari, bashi da zaɓi dole ya jawota jikinsa dan sanyin ya yi mata sauki, yasan ko ya ce ta tashi ta tafi ɗaki ɓata bakinsa zai yi, wannan uwar tsoro ai tana tashinta ma zata yi tsalle ta ɗane shi dan bala'in tsoro, haka ya jawota jikinsa ya kara tattare bed sheet ɗin gefen nata ya rufeta da kyau, shi kuma dai bai ji wani sanyi ba, hasalima zafi zafi kaɗa kaɗan yake ji, dama kun san su kam ai sarakan sanyi ne, sun saba da sanyin da ya ninninka wannan mai kankara ma. A haka dai suka cigaba da barcinsu, gently ya mayar da idanunsa ya lumshe su ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi.
Bashi ya farka ba har sai karfe 5:30, a nan ma ba karamar dirama suka sha ba, taki rabuwa da shi, sai da ya daka mata tsawa sannan ta dawo cikin hankalinta tare da takurewa a saman mattress ɗin tana kuka ƙasa ƙasa, shi kuma ya wuce toilet ɗin daddy ya ɗauro alwala dan lokaci anata sallah a masallatai, bayan ya fito ne ita ma ta miƙe cike da tsoro ta nufi cikin, tana bala'in tsoron haɗuwa da wani dan dai bata yarda ba wasu mutanen ba, kuma tana tsoron Lion ɗin, haka ta daure baiwar Allah ta nufi bedroom nasu ita da Jehan, wanka ta yi sauri sauri ta fito ta shirya cikin wata ƴar doguwar rigarta wadda da kaɗan ya wuce gwiwarta, da rigar tana kai mata har kasa, amma yanzu da ta ɗauko shi ya yi mata guntu, dan an jima ai rabonta da kayanta na gidan, rigar tana da dogon hannu, jikinta kuma kamar rigar sanyi yake, ma'ana yana da kauri, sai dai ta roba ce, tana kama jiki, ta bi jikinta ta kwanta luf, shape nata ya fito sosai da sosai, daga shape na sama har na kasa.
Zumbulelen hijabi ta zumbula har kasa, da sauri ta fesa perfume ta fito ta nufi balcony ɗin, a lokacin kuma karfe 6 da rabi ta yi, in da ya shinfiɗa dadduna ta nufa, yana kwance saman mattress ɗin, da alama ya mayar da barci ne, dan akwai barci sosai a idanunsa, sam taki kallon in da yake. Sallah ta yi tare da zama ta fara askar har zuwa karfe 8, rana ya ɗago sosai, lallaɓawa ta yi cike da tsoro ta nufi kitchen nasu, zuciyarta sai dukan uku uku yake yi, haka ta wuce gawarwakin mutanen daren jiya ta nufi kitchen. Komai yana nan yadda yake, akwai gas akwai komai, kayan tea ɗin da mum take haɗawa dad ta buɗe drawer ta ɗebo, yunwa take ji sosai, wanke pot ta yi tare da zuba ruwa ta ɗaura tea ɗin.
Bayan ta ɗaura sai ta koma palo ta cire hijabin jikinta ta ɗaura saman sofa sannan ta dawo kitchen ɗin, tsayuwa ta yi kusa da gas ɗin har sai da tea ɗin ya tafasa dai'dai yadda take buƙata, cike da tsoro da kuma fargabar me zai je ya zo ta ɗauko cup ɗin daddynta guda biyu masu bala'in kyau ta zuba musu tea ɗin bayan ta tace kayan ciki kenan, saman tray ta jerasu, shi sai ta ɗauko mishi madara da suga tare da milo, dan black tea ne ta girka, zuciyarta sai harbawa yake yi ta nufi sama da kayan tea ɗin.