Sashe 102
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi lamo a jikin kujera tana tunanin me ya kawo su wannan waje kuma, me Lion zai yi a nan?, Bata ankaraba sai gani ta yi gabaɗaya wutar clubs ɗin ta ɗauke, zaro idanunta waje ta yi tana faman kallon guys dake ta kunna hasken wutar tsadaddun wayoyinsu. A cikin duhun ta ji an buɗe gidan baya na motar tasu, ba ƙaramin bugu ziciyarta ya bada ba, jin alamar shigowar mutun a gidan bayan ne yasa bugun gaban nata ya kara tsananta, sai ƙoƙarin dannewa take yi, lokaci guda kuma ta sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya shaƙar numfashin mai ɗauke da daddaɗar kamshin perfume nasa da ta yi ne yasa hakan, ashe shi ne ya buɗe gidan bayan ya sanya mutumin da ya zo kamawa a ciki, ya yi wa mutumin ɗaurin goro tare da ɗaure mishi baki da wata tsumma wadda a wajen ya samu.
Gidan gaba ya zo ya shiga ya tada motar da gudun gaske suka bar clubs ɗin, har lokacin kuma wutar bai dawo ba, security dake wajen ma da karfin kakinsa ya yi amfani wajen wuce su, wato dai waya suka samu daga sama a kan akwai mota mai kira kaza zata zo fita, da ta zo a bata hanya ta fita, tun shigowarsu ya shirya hakan, lokacin da ya yi parking na mota kafin ya fito ya tsaya ya tura saƙo zuwa ga His excellency, shiyasa yana zuwa kawai aka bashi hanya ya fice abinsa.
Bai zame ko'ina ba sai gida, suna zuwa ya fito yana faɗin "Ki ɗauki abin da zaki ɗauka daga nan sai Kaduna". Ya kai karshen maganar tare da wucewa cikin gida dan ya ɗauki abin da yake da bukatar ɗauka, sun bar mutumin a cikin motar ɗaure ko motsi bai isa ya yi ba, dan ɗaurin mutuwa ya yi mishi, da sauri ita ma ta fito, har lokacin enginen wuta a kunne, zanensa da ta yi a baya ta ɗeba, tare da wasu hotuna da ta ajiye a drawersu, sai kayan haɗa tea na mum da take haɗawa dad ta ɗeba dayawa da dai sauran kayan da zata buƙata, trolley Jehan ta ɗauko ta shirya komai a ciki tare da nufar waje.
A cikin mota a wajen gate bakiɗaya ta isko shi, sanya trolley ta yi a cikin motar gidan baya kusa damutumin kafin ta dawo zata rufe gate ɗin, tana kokarin jan gate ɗin ta rufe sai ganin shi ta yi ya fito daga cikin motar ya nufota da nufin ya rufe gate ɗin, komawa baya ta yi ta tsaya tana kallon shi, ciki ya koma ya kashe engine tare da cire wayar sannan ya dawo ya rufe ƙaramin gate ɗin ta ciki da sakata kafin ya fito ya jawo babbar, wata danƙareriyar sarka ya sanya a jikin babbar gate ɗin, irin sarka ce da ake ɗaure manyan ɓarayi, ita ya fitar daga cikin boot na motarsa ya sanya wa babbar gate ɗin ta waje, sannan ya danna wata sabuwar kwaɗo da ya saya a shopping da suka yi ɗazun, sai da ya tabbatar ya yi wa gate ɗin ɗauri mai kyau kafin ya rufeta tare da juyawa ya nufi motar, da sauri ita ma ta juya ta shige ciki.
Da gudun gaske ya figi motar ya bar wajen, kai tsaye hanyar Kaduna suka nufa, sai sharara uban gudu yake yi tamkar zasu tashi sama, ita kuwa tuni ta lafe a jikin kujera sai barci abinta, duk wani checking point da ya wuce da karfin kakinsa ya yi amfani wajen wucewa ta yarda ba su tsayarda shi wajen bincikar motarsa da sauransu ba. Sai karfe 12 suka shiga Kaduna kai tsaye gida ya wuce, su Aseef sun jima da yin barci bayin Allah, ita ma Jehan tana can tana zuba barcin wahala Baiwar Allah, ta azabtu ba karya, ko wanka bata yi ba bare kuma cin abinci, tun wannan barci da ta yi time da Aseef ya kaita É—akin, tun shi bata farka ba.
Suna shiga gidan ya miƙawa Mark mutumin, dan suna shiga cikin gidan Mark ya nufosu da sauri yana yi wa ogan nasa welcome, Mark ɗan amana, ɗan ba ruwana, yana bala'in kaunar ogan nan nasa, dan halinsu kusan ɗaya. Umarni ya yi mishi a kan ya ɗauki mutumin ya cigaba da kula da shi yana bashi hukunci mai kyau zuwa lokacin da Nawazudden zai diro Naija, dan yana son haɗesu waje guda ne, kafin ya san abin da ya dace ya yi next.
Ita kuma Rimsha, sai barci take zubawa abinta, ba ta da labarin sun iso gida ma, kashe motar ya yi ya fito zuwa cikin gida, har ya kai tsakiyar harabar gidan, sai ya tuna ashe da ita suke tare, ɗan juyawa ya yi ya gani ko Mark na kusa ya buɗe mota ya tasheta, sai yaga walam babu Mark, ba dan ya so ba ya juya zuwa wajen motar, kofar side nata ya buɗe yana tunanin wai menene ma sunanta oho, hannu yasa yana ɗan bubbuga jikin kujerar, shiru bata farka ba, ganin zata ɓata mishi lokaci ne, ga shi yana son zuwa ya yi wanka tare da cin abincin ya kwanta, hakan yasa ya saɓeta a kafaɗarsa zuwa cikin kawai.
Da yake dare ta yi sosai, shiru kake ji, bedroom nata ya kai ta, saman bed ya kwantar da ita, ba tare da ya bi ta kanta ba ko ya kalli in da take ba ya juya sai bedroom nasa. Kayan jininsa ya fara cirewa, ya rage daga shi sai short sannan ya nufi toilet dan yin wanka, yau har cikin É—aki Mark ya kawo mishi abinci saboda TRIPLETS sun yi barci, babu mai kawo mishi.
Bayan ya kammala wanka, ya yi shiri cikin kayan barcinsa mai bala'in kyau da tsada, abincin Mark ya zuba mishi, ya ci mai ɗan yawa saboda yunwa da yake ji, bayan ya kammala ya sha lemu saboda abincin ta yi digesting, miƙewa ya yi ya nufi waje, shi kuma Mark ya kwashi kayan abincin ya nufi kitchen.
Palon kasa ya sauƙo, bedroom ɗin Areef ya fara shiga, tare ya samesu saman bed suna zuba barci, Aseef ga waya a hannunsa, da alama chatting yake yi barci ta yi awon gaba da shi, Allah sarki yana bala'in kaunar ƴan uwan nan nasa, ba zai iya yin barci ba tare da ya shigo ya duba lafiyarsu ba.
Saman bedside drawer ya zauna tare da fara karanto addua'o'i yana tofa musu, barci suke yi cikin kwanciyar hankali, dukkansu fuskokinsu ɗauke da annuri, da alama cikin matsanancin farinciki barcin ya ɗaukesu, gently ya karɓi wayar hannu Aseef tare da ajiyewa a gefe yana mai cigaba da tofa musu addu'a, zubawa ciwon Areef idanu ya yi yana kallon yadda ya shafa maganin a wajen, da kallo ɗaya ya yi wa wajen yasan Areef faɗa ya je ya yi ya fama wannan ciwon, har ya kai hannu kamar zai taɓa, sai kuma ya fasa dan baya son su tashi daga wannan barcin farincikin da suke yi.
Ya ɗan jima yana yi musu addua'o'i kafin ya miƙe, gently ya kaiwa Areef sumbata a goshi yana mai jin tsantsar kaunarsu a ransa, a nitse ya zagayo ta ɗayar ɓangaren da Aseef yake, shi ma ya bashi sumbata, cike da so da kaunarsu fal a cikin ransa ya wuce ya nufi nasa bedroom ɗin, saman bed nasa ya haye ya kwanta, duk a gajiye yake sosai, wayarsa ya jawo ya kashe kafin ya yi addu'ar barci ya shafa, a hankali ya lumshe dara daran blue eyes nasa, after some minutes idanuwansa a lumshe ya sanya hannu ya laluɓo remote ɗin Ac ya kara gudu tare da jawo bargonsa zuwa cikinsa ya kashe wutar ɗakin tare da kunna lamp dake bedside drawers masu bada wuta sky blue, babu jimawa barci ya yi awon gaba da shi, a hankali yake sauke numfashi cikin kwanciyar hankali, da gani ba ƙaramin jin daɗin barcin yake yi ba.
A É“angaren gidan Abba kuwa, lokacin da Imran ya isa da jelly, dai'dai lokacin shi ma Akil ya danno hancin motarsa tare da Umaisha..............â¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
E43-44💋
A ɓangaren gidan Abba kuwa, lokacin da Imran ya isa da jelly, dai'dai lokacin shi ma Akil ya danno hancin motarsa tare da Umaisharsa, a tare suka fito daga cikin motocin nasu, ɗaukar jelly Imran ya yi dan idan ya ce ta tafi da kafarta, zasu jima basu shiga ciki ba, kun santa dama da iya zuzuta abu, tsabar iskanci idan ya ce ta taka kafa sai taki, yes tana jin zafi amma har da karawa ta yi, rufa musu baya su Akil suka yi, sai da ya isa tsakiyar palo ya sauƙeta tare da zaunar da ita saman sofa ya juyo ya miƙawa Akil hannu dan su yi musabaha.
Fuska ɗauke da fara'a Akil ɗin ya miƙa mishi hannu suka gaisaz Umaisha ta dawo kusa da jelly ta zauna tana faɗin "Yaya Imran ina wuni?" Da fara'a sosai a face nasa ya amsa da "Lafiya lou ya karfin jiki". Dan Akil ya gaya mishi bata jin daɗi, da lafiya ta amsa mishi. Gin motsinsu yasa Akila fitowa dan taga su waye ne, ganin sune yasa ta kurma ihu ta taho da gudu ta rungume Umaisha da jelly ta faɗa jikinsu tana dariya, zama Imran da Akil suka yi saman sofa mai zaman mutun uku Imran yana faɗin "Ke Heartbeat zaki yi ki karya mini mata ko? To maza ki tashi a jikinta bata da lafiya".
Rungumeta jelly ɗin ta yi tana faɗin "Aunty Akila wlh jikina ciwo yake yi mini". Kara rungume sosai Akilar ta yi tana yi mata sannu duk da bata san menene yake damunta ɗin ba, a wannan hali Ammie da Abba suka sauƙo daga sama suka samesu.