Sashe 83
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun zo zasu shiga É—akin Lion É—in ta tsaya, kallonta suka yi "Lafiya Rimsha?" Areef ya tambaya, cikin muryar kuka ta ce "Yaya Areef ina tsoron shiga É—akin yaya Saif ni kam, zan zauna a nan palo kawai". ÆŠan lumshe idanunsa ya yi tare da sake warosu a kanta, da hannu ya yi mata nuni da ta shiga ba damuwa, bata son yin musu da babban mutun, dan haka sai ta shiga kawai.
A saman bakin bed nasa Aseef ya zaunar da ita tare da É—auko A box, saman bedside drawer ya É—aura A box É—in kafin ya fara buÉ—e wa yana duba magani, zama gefenta Areef ya yi, Aseef ne ya yi musu dressing na wajen tare da taimakon Areef É—in, shi ya nuna mishi maganin da zai yi musu amfani da shi da sauransu.
Rimsha ta sha kuka ba karya, dan maganin yana da zafi, sai rarrashinta suke yi, Aseef ya rakata har ɗaki sannan ya dawo, a ɓangaren Lion kuwa, sam bai ji daɗin saka Brady da ya yi da ya yi faɗa da Areef ba, dan kuwa yasan tsab zai yi wa Areef lahani, amma ba yadda ya iya zuciya ce ta ɗebe shi, ya ji babu daɗi yadda Areef ɗin ya fifita Rimsha da ya sani jiya jiya a kan Brady da suka jima.
(kai gaskiya Lion da sauranka, saboda wakalanci dan baka É—auki É—an adam da daraja ba shi ne zaka ce kare ya fi ta, a fifita kare sama da mutun kenan? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan rashin sanin darajar mutun har ina? Gaskiya ya kamata ace Lion ko ba yawa ne ka san darajan mutun.)
A ɓangaren Imran kuwa, lokacin da ya fita, pharmacy ya je ya haɗo mata magunguna ya dawo, har lokacin barcin wahala take yi, kiran Akila ya yi a waya ya tambayeta ina dollyn Jellyn, ta gaya mishi tana nan, ta bawa mai gadi ya zai fi kula da ita, dan wata rana idan tana da class ta tafi school babu mai bawa dollyn abinci, okey ya amsa mata da shi tare da ce mata zai zo ya ɗauka da daddare, tom ta amsa mishi da shi, ruwa mai sanyi ya tsaya a palo ya ɗauko mata tare da komawa cikin bedroom ɗin nasu, gefenta ya zauna jikin nata ya tsananta zafi over, har lokacin sai ajiyar zuciya take sauƙewa, wani irin mugun tausayinta da so da kaunarta ne suke kara ratsa shi, a hankali ya fara ƙoƙarin tashinta dan ta sha magani, yana yi kirjinsa na dukan uku uku dan yasan za'ayi dirama ba karya.
Da yake bata da lafiya sosai, sai bata wani bi ta kansa ba, ko da ta tashi, kuka kasa kasa kawai ta sa mishi, rarrashinta ya rinƙa yi tare da bata magani, karɓa ta yi ta watsa a baki, shi kuma ya sanya mata ruwa a baki, bayan ta gama ta koma ta kwanta tana kuka kasa kasa, yau dai bakin tsiwa ya mutu murus, kukan ma baya fita sosai. Kusa da ita ya kwanta, sai rarraahinta yake yi, da haka har wani barcin ya ɗauketa, kun san mai zazzaɓi da yin barci minti minti, shiru ya zuba mata idanu yana kallonta yadda take barci tana ajiyar zuciya, zubawa ɗan bakin tsiwar nan idanu ya yi, a hankali furta "Allah yasa daga haka bakin ya yi sanyi".......... To nima dai da Amin na amsa maka dan gaskiya idan bai yi sanyi ba akwai matsala kana ruwa.
A ɓangaren Rimsha kuwa, uniform nata ta cire tare da wucewa toilet dan ta yi wanka, har lokacin hannun nata yana ɗan yi mata zogi kaɗan kaɗan. Bayan ta gama wanka, ta shirya cikin doguwar riga abaya baka ta haye gado, yunwa take ji amma tana tsoron fitowa waje, a wannan hali Areef ya shigo ya same ta, lallaɓata ya yi ta miƙe su je su ci abinci, bata yi mishi musu ba dan yunwa take ji dama, tsoro ne ya hanata fita.
A palon kasa suka isko Aseef saman table yana jiransu, zama suka yi, kamar dai yadda suka zauna da safe, sun sakata a tsakiya, Mark ne ya zo ya yi serving nasu, bata musa ba, ta ci abincin nasu, yau kam ma kusan irin abincin Nigeria ne, shinkafa ce tasu ta can zara zara, sun dafata koriya shar, ta ji nama ba karya, sai wasu daga cikin kayan lambunsu da suke amfani da shi da sauran ingredient nasu, ta ci sosai dan ba karya ta ji yunwa, bayan sun kammala suka miƙe Areef ya ce ta zo su je garden, ba dan ta so ba ta bisu, yanzu tsoron Lion da Brady take yi sosai ba karya.
Zaune suka isko shi yana waya da daddynsu, daddy ya ce yana son ya zo Nigeria, shi kuma ya ce a'a ba yanzu ba, daddy ba zai iya jure rashinsu a kusa da shi ba, amma hakan ya hakura ba dan ya so ba, Brady na kwance a jikinsa, ya sha wahala ne yasa ya lafe a kirjin Lion É—in tare da lumshe idanu.
Ita da Areef kujera É—aya suka zauna, shi kuma Aseef kusa da Lion ya je ya zauna yana wani murmushi, yana son gayawa Lion ya je ya nema mishi auren AKila, amma ya fi son ya sami lokaci na musamman ya gaya mishi.
(Jama'a Lion da zuwa neman aure, Wayyo cikina anya kuwa wannan abin zata yuwu?🤣 Ba gara ma Areef ɗin ba, kuma dai ji yadda Lion yake cewa Imran ya kula da waƴan nan halittu🤣 wayaga Lion a wajen Abba ya je neman aure🤣)
💋GIDAN ABBA💋â¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
E35-36💋
💋GIDAN ABBA💋
Tun da Ammie ta shaki kamshin perfume É—in Lion sabuwar rayuwa ya shigeta, duk wasu aljanun dake gidan da wasu dodannin sun gudu, rayuwarta ta bayane ya fara dawo mata, Baiwar Allah ashe duk rayuwar da tayi tsawon shekarun nan bata cikin hayyacinta, bata sani ba, yanzu ne ta dawo normal.
Wani daddaÉ—ar kamshi air freshener ne yake tashi tun daga cikin babban palon kasa har zuwa harabar gidan, ko'ina na palon a tsananin gyare yake tsab, sai tashin kamshi ko'ina yake yi, har wani kyalli kayan cikin palon suke yi saboda tsantsar gyara da suka sha, gidan shiru da alama Akila ta tafi school.
Baki ɗauke da sallama Abba ya shigo cikin palon, ko kaɗan babu alamar mamaki a kan fuskarsa, domin kuwa shi ma yanzu ya dawo cikin hayyacinsa, abin da yasa kuma bai yi mamakin gyara palon da aka yi ba, saboda already yasan Ammie ba kazamiya ba ce, mace ce mai bala'in tsabta na amutu, akwaita da son gyara, ga bala'in son kamshi, shiru shiru bata son hayaniya, sai dai fa idan ka taɓota, zaka gane annabi ya faku, bata da fara'a sosai, amma ba laifi tana ɗan murmushi, yanzu gabaɗayansu ita da Abba sun dawo cikin hayyacinsu sanadiyyar turaren Lion........NASAN KOWA A ƘAGE YAKE DA YA JI TARIHIN AMMIE, TO KU GYARA ZAMA IN SHA ALLAH TARIHINTA NA NAN TAFE NAN BA DA JIMAWA BA, NIMA NA ƘAGU NAJI MENENE MATSALARTA? ME TAYIWA WAƳAN NAN SHAIƊANUN ALJANUN SUKE AZABTAR DA ITA HAR HAKA, GA DUKKAN ALAMU DAI SUN NUNA MUTUNIYAR KIRKI CE A RAYUWARTA TA BAYA, TO MENENE YASA HAKAN YAKE FARUWA DA ITA? KU KASANCE DA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA DAN JIN YADDA KOMAI YA WAKANA.
Sama ya nufa yana mai shaƙan kamshin air freshener mai bala'in daɗi da yake fitowa daga cikin bedrooms nasu, a ƙage yake da ya shiga cikin ɗakin nasu, ɗakin Ammien ya fara nufa, baki ɗauke da sallama ya shiga, tana zaune saman dadduma ta idar da sallar azahar tana addu'a, ko'ina a cikin ɗakin nan a gyare yake tsab, ga azababben daddaɗar kamshi da kuma sanyin Ac mai ratsa zuciya yana tashi.
Sai wani lumshe idanu yake yi ya kariso cikin ɗaki, da sauri ta miƙe tare da nufo shi tana yi mishi sannu da dawowa cikin harshen turanci, da yauwa ya amsa mata tare da rungumota, ta sha kwalliya da wata danƙareriyar doguwar riga mai bala'in kyau da tsada, bata yi wani make up sosai ba, dan ba wani son make up ɗin take yi ba, iya ka powder ta murza da kwalli, ta ɗaura gyalen rigar a kanta kafin ta sanya hijabi, dukkansu bayin Allah sun shiga sabuwar rayuwa, da alama ma sun mance da rayuwar da suka yi a baya, idan kuma basu mance ba, to akwai wani abu a kasa, amma lokaci ne zai nuna mana komai, dan abin da mamaki yadda Abba bai yi mamakin sauyawarta ba, duk da eh yasan haka take a baya, amma basu nuna wata alamu da zata nuna cewa sun san sun yi rayuwa cikin kazanta da wahala ba, ko da yake dama idan dodannin ma suka zo suka zanesu, mantar da su komai suke yi, koma dai me lokaci zai nuna mana menene yake faruwa? Menene gaskiyar lamari?.
Sannu da zuwa ta yi mishi, shi kuma cike da nuna so da kulawa ya tambayeta ina su Imran, AKil, AKila, basu dawo bane?, Da mamaki cikin harshen turanci ta ce "Su Imran ban san in da suke ba, Akila kuma ta tafi school, amma ka kira mini Imran É—in a waya, ya zo maza, ko ina suka shige Oho". Sai da ta yi maganar ya tuna Akil ya gaya mishi zai koma Madina sati mai zuwa, ya sha'afa da zancen baki É—aya sai da ta yi maganarsu yanzu.