← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 121

Sashe 27

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A razane ta miƙe tsaye tana ganin yadda waƴan nan jibga jibgan sojojin ke dirowa kasa daga saman bayan motoncinsu, dukkansu fuskar nan tasu babu alamar annuri, ga su da tsawo da kuma murɗaɗun jiki tamkar wasu warriors, su goma sha biyu ne cif cif kamar yadda ya faɗa, mamaki ne ya kamata dama da gaske yake yi da ya ce zai karo wa su sojoji goma sha biyu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun wannan wace iriyar zuciya ce ke gare shi,? Muguntarsa ta wuce gaban misali.

Dafata Imran ya yi yana faɗin "Na san abin da kike tunani, bai wuce cewa da gaske ne daman Saif yake yi na karo wasu sojojin ba, to ki sani ni tun ranar da ya yi maganar na san cewa yes confirm sai ya kawo su kamar yadda ya faɗa domin duk abin da kika ji ya faɗa to wlh sai kin yi shi, ko mutuwa zaki yi sai kin yi shi, in ya so daga baya ki mutu, tun da ya ce sai kin yi wa waƴan nan kafuran aiki to fa ba makawa kuma babu mai canza hakan sai shi idan ya yi ra'ayi, ya sauƙo daga dokin zuciya da ya hau, ni yanzu damuwa ta ɗaya, tayaya zaki kasance a cikin waƴan nan kafurai masu fuskar shanun? Ba su da imani da tausayi, abin haushin ma, shi ne shiga ɗakinsu da zaki rinƙa yi, kafurai ne ba musulmai ba, bare na ce za su bi dokar Allah, gaskiya daddy bai kyauta ba maganar da ya gayawa Saif, ga shi yanzu ya ja maki bala'in da in danginmu dukka za su haɗu babu mai fiddaki, amma In Sha Allah komai zai wuce nan da ƴan kwanaki kaɗan, ina da tabbacin zai sauƙo, zuciyar zata yi sanyi".

Rushewa tayi da kuka tare da zube gwiwowinta a kasa ta toshe baki da hannayenta dukka biyu, ƙwaƙwalwarta yana tariyo mata irin muguntar da ya rinƙa yi mata, hannu yasa ya ɗagota yana mai rarrashinta.

A wannan halin Areef ya shigo garden É—in ya same su, da fara'a ya shigo, amma ganinta a wannan hali yasa ya É—aure fuska sosai. "Prof me ka yi mata take kuka?". "Me kuma zan yi mata Areef? Kawai dai taga sojojin nan da Lion ya ce zai kawo ne, to ta ga ya cika maganarsa ne, shi ne take kuka.

Murmushi kaɗan ya saki, cikin sigar rarrashi ya fara magana "Our princess ina raye ba zan taɓa barin hakan ta faru ba, ɗan uwana ne fa, na san ta yadda zan bi da shi, kada ki wani damu, In Sha Allah wannan aikin gabaɗaya kin kusa dainawa, daga yau zuwa gobe, zan san ta yadda zan dakatar da shi, ba dai na sami lafiya ba, kawai ki zuba ido ko sha kallo, yanzu dai share hawayenki gimbiyar TRIPLETS". Ba karamin daɗi ta ji ba, cikin sauri ta goge hawayenta tare da fara zuba mashi godiya.

Girgiza kai ya yi tare da sanya hannunsa ya É—an rungumota a gefen jirjinsa, wani iri ta ji a jikinta, shi kuma ko a jikinsa bai damu ba, bai ji komai ba.

"Ku zauna mana, Prof ina da magana da kai". Ya faÉ—a tare da saketa ya zauna saman sofa, kusan a tare ita da Imran suka koma suka zauna.

"Prof what is goruba?". ÆŠan zaro idanu waje Imran ya yi, tunani ya fara yi, wai a ina Areef kuma ya jiyo sunan goriba? Me kuma zai yi da ita? Dan dai tabbas shi dai ba iya cin gorobar zai yi ba, bai ma santa ba, amma ya zo yana tambaya.

"Prof i said what is goroba?". "Areef what are you going to do with the goruba?". Kai tsaye cikin wasa ya ce "My future wife mana zan kaiwa, wai kai Prof ina ruwanka ne? Just kawai tell me what is it, kai ni nama fasa son sani menene, just kawai a kawo mani goroba from now to tomorrow"........ To fa goruba kuma🤔

"To Shikenan za'a kawo maka, ba dai goroba ba? Ai gidanta kazo, Allah yasa ka iya ci". Imran bai yarda a kan wata zai kaiwa ba, domin shi dai yasan TRIPLETS ba É—aya daga cikinsu da yake da girlfriend, kai idan ma ba Rimsha ba, ba su da wata mace da suke yi wa magana, hakan yasa bai yarda da zancen ya ce wata zai kaiwa ba, ya mayar mawai kila yana son ya gwada ci ne, tun da wani lokaci tana cewa zai ci abincin hausawa, to amma a ina yaga goriba? A ina yaji sunanta da har zai gwada ci É—in? Shi da ko saninta bai yi ba? Akwai wata a kasa.

Areef zai yi magana Imran ya rigashi da cewa "Rimsha Saif na buƙatar abinci, ki je ki kai mashi, dan Allah Rimsha ki kula kin ji ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi tare da amsawa da to, daga haka ta miƙe ta bar wajen, su kuma cigaba da hira suka yi.

Kamar kullun Mark ya kammala haÉ—a mata abincin, hannunta ta wanke kafin ta É—auka ta wuce izuwa bedroom nasa.

Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, yana balcony, ya miƙe a saman ɗaya daga cikin tsadaddun kujerun dake a wajen, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, sai wani Lumshe idanu yake yi kamar mai jin barci, pajama ne a jikinsa, launin army colar, ya saki wannan kyakkyawar dark black curly hairn nan nasa, sai wani kyalli gashin take yi, kwana biyu da suka ɗan yi a Nigeria har ya ɗan yi duhu saboda zafi, fatarsa ta rage haske, sai dai kuma ta kara kyau da kwanciya luf luf kamar matar jariri, ya kara fresh sosai.

A in da ta saba ajiye mashi abincin, a nan ta ajiye, ita ma zaman ta yi tana jiran shi, shiru shiru ba shi babu labarinsa, sai ƴan waige waige take yi kamar mai neman wani abin, ji take yi tamkar ta tashi ta ɗan yi mashi taɓe taɓe tun da baya nan, amma sai ta tuna da abin da Imran ya gaya mata kafin ta zo, tuna hakan yasa ta daure ta cigaba da zama jiran shi kawai.

Sai da ta kwashi minti 30 a wajen a zaune kafin ya miƙe ya taho, wa iya zubillah, kallo ɗaya ta yi mashi, ta yi saurin kawar da kai, dan kada ya kamata, da yake yana nufota ne, amma ta kasa manta kyawun da ta kallah.

A in da ya saba zama ya zo ya zauna, abinci ta zuba ta tura Mashi, ba ɓata lokaci ya ɗauka tare da fara ci, sai satar kallon shi take yi.

Ɗan dai'dai ya ci abincin, ya ajiye spoon ɗin tare da yi mata alama da hannu akan ta zuba mashi ruwa, cikin sauri ta zuba ta mika mashi, ba ɓata lokaci ya karɓa ya sha, bayan ya ciro cup ɗin kuma, ya ajiye mata tare da miƙewa ya fice daga ɗakin, cikin sauri ta kwash kayan abincin ita ma ta fita.

Kitchen ta mayar da kayan abincin kafin ta dawo in da su Imran suke zaune, zama ta yi suka cigaba da hira.

Misalin karfe 10 daidai Imran ya je ya ɗauko AKILA, tun jiya dama Rimsha ta kirata a waya ta gaya mata cewa ta zo mata da kayan tea ɗin, yaya Imran ya ce zata zo su wuni, sai dai a gidan Akil ya je ya ɗaukota, yaki zuwa gida da kansa, domin ya ji labarin kiran da Ammie take mashi ta bakin Akil ɗin, to yaki zuwa, ya fi so sai ya haɗu da Abba sun tattauna kafin ya timkareta, sai Abbansa ya yanke hukuncin me zai ce mata kafin su haɗu kenan, shiyasa ya kira Akil akan ya ɗauko mashi Akilar daga gidan, ya ce wa Ammie za su je wani gari ne haka, domin yana so Akilar ta yi kwana biyu haka a gidan, ta ɗan ɗebewa Rimsha kewa, ai kuwa Akil da ya je, sai ya ce wa Ammie Abuja za su je, ita kuma in dai Akil ko Imran ne za su ɗauki Akilar, to bata damuwa, koma wata ne suje su yi, dan tasan suwa ye ta haifi........... OH WASA WASA AKIL DA IMRAN SUN ZAMA MAKARYATA SABODA SOYAYYA.🤔 SU DA BASU SAN MENENE KARYA BA, BASU YI, SUNA MA TSAWATARWA MASU YI, AMMA YANZU SABODA KAUNAR FAMILY'N ABBANSU SUN FARA KARYA SOSAI....🤔

Da Akil ya je gida ɗaukar Akila, Ammie ta tambaye shi ina Imran, sai ya ce mata ai baya kasar ne ma baki ɗaya, amma ya kusa dawowa, haushi kamar ta yi yaya, haka ta hakura ba dan ta so ba, ta yi kwafa tana jiran dawowar shi, dan dole ya saki jelly, bata san shi ma Akil ɗin yana tare da matarsa ba, in dare ya yi, sai ya dawo gida ya shiga ɗaki kamar mai barci, idan dare ta tsala kowa ya yi barci, sai ya fita ya gudu gidansa wajen Umaisharsa abinsa. (Ƴaƴan Ammie akwai ƴan air wlh🤣)

Yau murna a wajen Rimsha ba'a magana, ta rungumi Akila sosai kamar wani ya ce zai rabasu, ita tasan Akila Æ´ar uwarta ce ta jini, ita kuma Akila bata san hakan ba, kuma ga shi daddynta ya ce kada Imran ya faÉ—a, hakan tasa bai faÉ—a ba ya yi shiru, ita ma bata gayawa Akilar ba.

ÆŠaki suka kule, sai zuba hira suke yi, a in da Akila take bata labarin masoyinta ya ce zai zo ranar Wednesday, tana cikin murna mara misaltuwa, sai murna Rimsha take taya ta, tun da Akila ta zo bata haÉ—u da Areef ba, haka ma Lion basu haÉ—u ba, hasalima daga Lion É—in har Areef É—in ba su san ma tazo ba, gara Lion ma Imran ya gaya mashi zai je ya É—auko sister sa wa Rimsha, sai da ya bashi izini tukun nan ya É—aukota.
Chapter 27 · 0% Book details