Sashe 121
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Can misalin ƙarfe 11:20 ta sauko daga saman gadonta dan ta je ta ɗauro alwala ta zo ta yi sallar nafila, dan yunwa ya hanata barci Baiwar Allah. Toilet ta nufa, sarki ta yi tare da ɗauro alwala ta fito, dai'dai zata shiga hanyar da zai kaita ɗakinsu babu kowa a wajen, ko tsoro bata ji ba, ga shi dare ne kowa ya kule cikin ɗakinsa, kamar daga sama ta ga mutun a gabanta, da yake akwai hasken wata sosai, sai ta gane waye ne, kallon gefen ido ta yi mishi kafin ta kara ɗaure fuska sosai tana faɗin "Malam lafiya zaka wani zo ka tare mini gabana?". Yatsa ya ɗaura mata a saman lips nata yana faɗin "Not malam it's babyn baby". Kallon uku goma ta watsa mishi kafin ta ce "Bani hanya na wuce!". Matsowa kusa da ita sosai ya yi "Babu in da zaki wuce ki je, wai ke baki murmushi ne sai faɗa kullum ki ka iya?". Banza ta yi da shi bata sake tankawa ba.
Raɓawa gefensa ta yi zata wuce, cikin sauri ya sake shan gabanta, har cikin ranta tana bala'in tsoronsa, dan ganin fuskarsa ma razana ta yake yi, idan baku manta ba, TRIPLETS akwai kwarjini sosai, amma saboda dakiya irin tata ne take dannewa ta nuna kamar ma bata ji komai ba, daga ta ciki kuma, har wani dukan uku uku kirjinta yake yi na bala'in tsoronsa.
"Wai kai me na tare maka ne da zaka zo ka takura mini?". Matsowa kusa sosai ya yi da ita, har yana iya jiyo sautin numfashinta, "Tambayar me kika yi mini kike yi? To ki saurara, me yasa kika shiga cikin tunanina kika watsa mini lissafin ƙwaƙwalwata? Ya zama komai nake yi sai na kallin wannan kyakkyawa kuma fusataccen fuskar taki mai kama da unclena? Ga idanun nan naki sun saka ni a gaba da tunani, na kasa barci sai su nake tunawa, shi ne yasa nazo in ganki, ni anya ma ba zan ɗauke ki kawai mu tafi ba? Kai na fara jin hakan a raina, amma dai yanzu faɗa mini ke kina tunanin face na?". Wani muguwar harara ta watsa mishi kafin ta ce "Waye kai da zan yi tunaninka? Kuma sai na rasa waye ma zan yi tunani sai kai? Lallai baka da aiki, ni ka bani hanya na wuce hai!!". With full confidence take yin maganar.
"Komai kika yi ni burgeni kike yi, ji yadda kike tsaro magana kamar wata brigadier general na sojoji, ji É—an bakinta a wajen ban da tsiwa babu abin da ta iya, idan kika cigaba da yi mini haka for sure sai na shanye wannan É—an bakin, ni ki gaya mini kalamai masu daÉ—i bari na wuce zuwa gida hai!". Ya kai karshen maganar yana É—aure fuska, tunani ta fara yi to ko dai ta yi mishi ihu ne? Amma kuma ai tun da ya shigo har in da take hakan ya nuna cewa gandurobobin sun san da zuwansa, so ko ta yi ihu ba amfani, wannan bala'in dame ta yi kama? Zai wani takura mata, dan iskanci wai sunansa babyn baby.
Tana can tana tunani bata ankara ba sai jinta ta yi a jikinsa ya jawota yana faɗin "Zaki gaya mini kalamai masu sanya mutun love and romance dream ne ko dai ya ya?". Duk da tsoronsa da take ji bai hanata wage baki zata yi mishi ihu dan ya sake ta ba, ta san yadda ya riƙeta ɗin nan ba zata iya kwace kanta ba, kada ku manta su rungumar mace a wajensu ba laifi bane.
Cikin sauri ya toshe mata baki yana faɗin "Masifaffiya kawai, ni ki natsu ko dai wlh na shanye bakin nan naki, maza yanzu ki ce I love you my baby tare da wasu kalamai dan na samu na tafi Aseef sai kirana yake yi, ya damu sosai dan ina waje, bai san ina wajen wadda ta takura tunanina bane". Ya kai karshen maganar tare da sakinta ya kuma zame hannunsa daga bakin nata, dan ya fara shiga wani yanayi, da gudu ta raɓa gefensa ta wuce tana mai jin haushinsa, a kan me zai wani rungumeta? Har da ce mishi mugu azzalumi ta yi, shi kuwa juyowa ya yi tare da goya hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa yana binta da kallo har ta shiga ɗakinsu, murmushi kaɗan ya yi kafin ya ce "Sarkin faɗa, zaki dai'na ne, na rinƙa takura miki kenan, waye ya ce kiyi kama da uncle na? Ai tun da kika yi kama da shi kin shiga uku da ni, ba dai kin nuna baki so abin da nake yi miki ba? To mu zuba mu gani". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi office ɗin shugaban gandurobobin, sallama ya yi mishi kafin ya ce da Mark da yake zaune su tafi, gaba ya yi Mark ɗin ya rufa mishi baya suka nufi motarsu.
Gida kai tsaye suka wuce, a lokacin kuma Aseef bawan Allah ya gama rarrashin AKila, dan sai kuka take yi mishi, ta sanar da shi cewa su Abbi zasu dawo gidansu da zama gobe dan shirye shiryen bikin tun da goben saura kwana shidda kenan, ya shiga tashin hankali na wuce misali, amma haka ya daure ya danne ya yi ta rarrashinta tare da bata hakuri ya kuma kara mata kwarin gwiwa a kan su kaiwa Allah kukansu, su kuma bashi zaɓi, In Sha Allah komai zai zo musu da sauki, da kyar dai ya samu ta ɗan kwantar da hankalinta har suka ɗan yi hira, bayan sun yi sallama misalin karfe 1 kenan, barci gabaɗaya ya kaurace daga idanun bawan Allah nan, ya shiga tsananin damuwa ya rasa mafita, gaskiya shi ba zai iya rabuwa da ita ba, koma yaya ne, dole ya san abin yi a kan hakan.
Ko da Areef ya dawo, bai bari ya gane halin da yake ciki ba, da ya ji motsin shi ma, barcin karya ya yi, hakan yasa Areef ɗin ya shigo ya yi mishi addu'a kawai ya juya zuwa nashi bedroom ɗin, sai da ya yi wanka ya yi shiri cikin kayan barci kafin ya kwanta zuciyarsa cike da tunanin Jehan ƴar diramarsa, da haka barci ya kwashe shi ba tare da ya leƙa Lion ba.
A ɓangaren Lion kuwa..........