← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 121

Sashe 35

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai Rimsha da yake ba mai cika son surutu bane, tun tana amsawa Anaya har ta dawo binta da to, a'a, da kuma e, wani lokaci ma girgiza kai kawai take yi tamkar Anaya É—in na a gabanta. Sai dariya kasa kasa Akila take yi, dan ta tula Rimsha ta gaji da surutun Anaya, ita kuma Anaya tamkar yanzu ma ta fara, babu niyar dakatawa a lamuranta.

Sai da aka kira sallar issha, cikin sauri Rimsha ta sallameta tana sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya tare da godiya ga Allah ta tsira daga takurar Anaya, ita kuwa Anaya cewa ta yi idan ta yi Sallah zata sake kiran ta, da okey kawai Rimsha ta bita da shi, ba dai idan ta kira ɗin sai ta ɗauka ne zata ji surutun ba? To wlh ba zata ɗauka ba, ta faɗa a ranta tana turo ɗan bakin, da haka ta nufi toilet dan yin alwala.

Bayan ta fito Akila ta shiga ita ma. A tare suka yi sallar mangariba suka zauna har lokacin issha ya yi, bayan sun yi issha ne Rimsha ta miƙe dan ta kaiwa Lion abinci, ita kuma Akila ta haye saman gado tare da jawo wayarta dan ta yi hira da masoyinta a WhatsApp, tun da yanzu ya bata damar tana iya yi mishi massage a WhatsApp, amma ko a WhatsApp ɗin numbersa a rufe take.

Kamar kullum, Kitchen ta nufa dan É—aukar abincin, bayan ta wanke hannayenta ta É—auka a nutse, ba tare da ta ce da Mark ko sannu ba, shi ma ko sannu bai ce mata ba, kamar kullu ko kallon in da take bai yi ba.

Da sallama É—auke a bakinta ta shiga É—akin, yanzu ta daina tsayuwar jiran sai an amsa mata sallamar ta, tana zuwa zata yi sallama ta faÉ—a.

Babu kowa a É—akin, da alama sun fita, a in da ta saba ajiye abincin, a nan taje ta ajiye tare da zama tana tunanin ina kuma suka shiga.

Bata gama rufe tunanin nata ba ya shigo cikin É—akin yana mai yin sallama kasa kasa, da mamaki ta amsa sallamar kasa kasa ita ma, kenan dama idan zai shigo É—akin nasa yana yin sallama? Ta tambayi kanta tana É—an satar kallon shi, yes idan zai shiga É—akin nasa yana yin sallama, duk da yasan babu kowa a ciki, amma yana yin Sallama saboda sunnah ce ta annabi yin hakan, idan kayi sallama mala'ikun rahma zasu amsa maka idan ba mutane, yanzu ma bai san da ita a cikin É—akin ba, ya dai yi sallamarsa ne kamar yadda ya saba.

Ta kasar ido ya kalli inuwarta, hakan ya tabbatar mashi da mutun a cikin É—akin, kwata kwata ya manta da ya ce zai kalleta idan ta shigo, zai kalli wacece su Areef suke so haka?, Allah sarki sabo tirken wawa, ya saba da É—abi'arsa na rashin É—aga idanu ya kalli abu, da wuya ya dai'na.

Da yake yana jin yunwa, sai ya wuce wajen da ya saba zama ya zauna, yana zama gabaÉ—aya wutar gidan ta É—auke diff tamkar dama wutar nepa ce, mamaki ne ya kama shi, ta ya akayi engine nan ya mutu? Tun da yazo Naija da aka É—auke nepa sau É—aya aka yi wajen 3 hours ba'a dawo da shi ba, daga nan ya yi watsi da nepa ya saho wani tampatsetsen engine wuta, mai matukar gudu da bada wuta mai karfi, baya shiri da zafi, Shiyasa ba zai iya zama babu wuta ba.

Wani irin mugun tsoro ne ya dira mata a ranta ganin duhu ya mayaye ko'ina na cikin É—akin, kun santa da tsoron bala'i, shi kuma jingina kansa da jikin sofar dake kusa da shi ya yi tare da waro idabunsa sosai yana kallon gabansa, ma'ana yana kallon in da yake fuskanta.

Shiru shiru wutar bata dawo ba, shi kuma bai kunna wutar wayarsa ba, yana jin ta yadda take wani jan numfashin tsoro a hankali hankali, alamar ta tsorata over.

Almost 10 mins shiru babu wuta babu labarinsa, sai raba idanu take yi, shi kuma har jikinsa ta fara haÉ—a zufa, ya tsani zafi fiye da tunanin mai tunani, Sojoji goma sha huÉ—u da su Mark a gidan amma wuta ta É—auke har tsawon minti goma basu duba me matsalar ba?.

Guntun tsaki ya ja tare da ɗago kan nasa da nufin ya miƙe ya nufi wajen, kwatsam sai ga hasken wutar ta dawo, wani mahaukaciyar ihu ta kurma tare da sulalewa kasa sumammiya.

Da mamaki ya kalleta kwance a kasar, ko me ya sumar da ita Oho, yarinya tamkar mai aljanu, tamkar kanta biyu, da yake tana kwance ne sai bai samu damar ganin face nata ba, kuma irin kwanciyar da ta yi, ta ɗaura hannunta ɗaya a saman kumatunta, dan lokacin da take kurma ihun sai da ta dafe kumatun nata da hannayenta dukka biyu, ba komai ne kuma ya sanyata ihu da suma ba fa ce ganin cikin kwanyar idanunsa da ta yi, tana fuskantarsa, ga shi da yake a duhune idanun nasa a buɗe suke sosai, kuma shima yadda ya yunkura zai tashi ita yake fuskanta, hakan yasa ta kalli tsakiyar kwayar idanun nasa, ba ƙaramin razanata suka yi ba, saboda hasken wutar yasa kwayar idanun sun kara kyalli.

Komawa ya yi ya zauna, har ya kai hannu zai ɗauki ruwa ya zazzage mata a kai, nan take zuciyarsa ta tunano mashi da irin farincikin da TRIPLETS nasa suka shiga ɗazun a ta dalilinta, har ga Allah yaji daɗin da bai taɓa ji ba na ganinsu a wannan farincikin, tuna hakan yasa ya fasa zazzaga mata ruwan sanyi, dan kada ta cutu sosai, idan ya zazzaga mata wannan ruwa mai uban sanyi, to fa a haukace zata tashi, idan ba'a yi Sa'a bama, tana iya hayewa kansa, dan fita zata yi a hayyacinta.

A na haka sai ga Areef ya shigo É—akin shima yanzu ya idar da sallah, daman sun rabu da Lion ne, shi ya wuce bedroom nasa dan yin Sallah a can, Imran, Lion kuma suka wuce masallaci.

Wajensu ya nufo dansu ci abinci, yanzu kusan gabaÉ—aya ya tare a É—akin É—an uwan nasa.

"Kai subhanallah Lion menene ya sami sister kuma?" Tamkar babu shi a ɗakin, bai amsa ba, sai ma yunkurawa da ya yi zai miƙe ya bar wajen, cikin sauri Areef ɗin ya ce "Please zauna bari ni nayi serving naka ko?". Ba musu ya koma ya zauna dan yunwa yake ji, ɗaukarta cak Areef ya fara yi yana ciza laɓɓansa alamar zafi kafaɗarsa ke mashi, dan akwai sauran ciwo sosai, ko sannu Lion bai ce mashi ba, ai shi ba ƙaramin yaro bane, yasan abin da ya dace da shi, da kuma wanda bai dace ba, idan ya yi wa kansa illah ma shi ya jiwo.

Saman sofa dake a cikin ɗakin ya kwantar da ita tare da dawowa wajen ɗan uwan nasa yana cizar lallausan laɓɓansa.

Abinci ya zuba masu suka ci a tare kamar É—azun, bayan sun kammala ya kwashe kayan abincin ya É—aura saman table dake cikin É—akin.

A tare suka miƙe Lion ya nufi toilet shi kuma ya haye saman bed, ita kuma tana sume a samar sofa.

Wanka Lion ya yi tare da fitowa ya shirya cikin kayan barcinsa riga da wando masu shegen kyau ga laushi kamar auduga, ba su da nauyi ko kaÉ—an, kamar dai kullum launin white color ne, bai É—aure kyakkyawar gashin kansa ba, ya barshi zube sai kyalli yake yi yana tashin kamshi.

Saman gadon ya dawo ya kwanta yana zuba uban kamshi, yana kwanciya Areef ya miƙe ya nufi toilet ɗin dan shima ya yi wanka, saboda ciwon dake a kirjinsa shi ba wanka yake yi kamar kowa ya yi ta zuba ruwa ba, no a hankali yake yi ta yadda ruwar ba zata taɓa bandejin dake wajen ba, har ta taba ciwon, hakan yasa idan ya shiga wanka sai ya ɗauki almost 1 hour kafin ya kammala, daki daki yake yin komai.

Shiryawa ya yi cikin kayan barcin Lion, a Æ´an kwanakin nan ma kayan É—an uwan nasa yake yawan sawa, dan kusan ya tare a ya dawo É—akin Lion É—in, idan ya shigo baya fita har sai idan zai yi wani abin, kayan barcin launin black color ya sanya, bai cika sanya farin abu ba a yanzu, sabida ciwon nan nasa, baya son ganin stain na jini a jikin kayansa, so ya fi sanya Black colar or brawn, wadda ba zasu fitar da shaidar abu ba, duk kaunar da yake yi wa white color ya hakura.

Saman gadon yazo ya kwanta kusa da É—an uwan nasa, har lokacin Rimsha tana sume kwance saman sofa, da alama shi ma Areef É—in ya mance da ita a wajen.

A kwanciyar tasu suna fuskantar juna, Lion idanunsa a lumshe, shi kuma Areef ya tsare shi da idanu yana kare mashi kallo tare da godiya ga ubangijin daya yi masu wannan kyakkyawar halittar haka, Lion kyakkyawar gaske ne kamar shi ya yi kansa, har ta Æ´an uwan nasa yaba kyansa suke yi, da yake su basu ganin nasu kyau É—in sai nashi, dama kuma haka ne, baka cika ganin abu ba idan a jikinka yake, kafi ganin kyaunsa a jikin wani, to suma haka ne sunfi ganin kyan juna, É—aya yaga na É—aya haka.

Daga karshe Areef ya juya tare da É—auko wayarsa daya É—aura saman bedside drawer ya shiga latsawa, dan kwata kwata baya jin barci, shi kuma Lion da alama barci yake ji sosai, Shiyasa ma ya yi barcinsa abinsa.

Ita kuwa Akila tana kwance tana chatting da masoyinta, bata wani damu ba dan Rimsha bata dawo ba, while shi kuma Imran yana É—akinsa yana shirin barci.

☠️DAULAR MUTUWA☠️

A YAU DAULAR MUTUWA TAKE KARA SHEKARA GUDA A KAN SHEKARUN HASSASATA DA AKA YI.
Chapter 35 · 0% Book details