← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 121

Sashe 24

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Miƙewa shi ma Lion ɗin ya yi tare da dirowa kasa ya nufi wajen abincin, sai dariya Aseef yake yi masu, idan Aseef da Areef suka haɗu, kamar wasu tom and Jerry suke komawa, su na wasa da dariya da juna over, kamar wasu ƴaƴan kawu nai, sun haɗe kai sosai, shi kuma Saif sai dai ya yi ta binsu da ido kawai yana jin daɗin yadda suke farinciki.

Zama ya yi tare da ɗaukar spoon zai fara cin abincin, karɓe spoon ɗin Areef ya yi tare da ɗebowa ya kai mashi saitin ɗan bakinsa yana faɗin "Ni zan baka first spoon". Kallon gefen ido mai kama da hararar wasa ya wurga mashi kafin ya buɗe ɗan karamin bakin nasa. Zuba mashi abincin Areef ya yi, sai murmushi Aseef yake yi, karɓar spoon ɗin shi ma Lion ɗin ya yi, ya ɗebo abincin ya kawowa ɗan uwan nasa a saitin bakinsa, buɗe baki Areef ya yi ya karɓa, a tare suka fara taunar abinci, Aseef ji yake tamkar ya yi tsuntsu ya zo ya same su, wayyo yana wani irin mahaukacin kewarsu.

Abin gwanin burgewa, dama idan suka haÉ—u, tsantsar kula da nuna kaunar juna suke yi wa kansu, É—auko wani spoon É—in Areef É—in ya yi suka fara cin abincin a tare, sai hira Aseef da Areef suke yi, shi kuma abincin kawai yake ci yana saurarensu.

A tare suka cire hannu daga abincin, sun ƙoshi, kusan kuma a tare suka sha ruwa. Miƙewa Areef ya yi tare da kwashe kayan abincin ya fitar, lokacin da ya dawo, Saif ya koma gado ya kwanta tare da ajiye wayarsa a saman bedside drawer yana sauraren Aseef tare kuma da kallonsa.

Hayewa gadon shi me ya yi, suka cigaba da hirarsu mai cike da so da kuma kaunar juna, sai zolayar juna suke yi, har Lion ya yi barci ya barsu, daga ƙarshe dai suka yi sallama har da yi wa wayar kiss kamar wasu masoya, tare kuma da furta kalmar i love you wa junansu, abin gwanin burgewa da ban sha'awa, kowa zai yi fatan samun ƴaƴa irinsu masu bala'in kaunar juna haka koma fin hakan.

Kashe wayar Areef ya yi tare da É—aurata saman bedside drawer kusa da lamp, daga nan ya kashe musu wutar É—akin tare kuma da kara gudun Ac ya kwanta, yau dai a É—akin É—an uwansa zai kwana kenan.

Yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.

A ɓangaren Imran kuwa, bayan ya maida ita bedroom nata, na shi bedroom ɗin ya wuce, ya ɗauko ɗayar wayarsa ya kunna domin ya kira Abba, dama ya kasheta ne kawai dan baya son damuwar kiraye kirayen jama'a, shiyasa Ammie ta yi ta neman numbersa bata shiga.

Bugu É—aya ya yi wa Abba ya É—aga, a lokacin kuma Ammie ta yi nisa cikin barci, akwaita da nauyin barci sosai.

Cikin girmamawa ya gaida Abban nasa, bayan sun gaisa ne ya ce "Abba dan girman Allah ka gaya mani menene ya haÉ—aku da bappa Hosain da har ya yi fushi da ku ya baro gida". Shiru Abba ya É—an yi na Æ´an mintoci. "Imran babu komai kawai fushinsa ya yi, kasan shi da bala'in zuciya kamar babanmu, to fa Æ´ar karamar faÉ—a ce ta haÉ—asu da mata a cikin gida, shikenan dan munbi bayan matan munyi mashi faÉ—a ne ya zuciya ta baro gidan".

Tabbas Imran yasan ba haka bane, domin a iya zaman da ya yi da daddyn Rimsha a baya, ya fahimci mutun ne shi mai zurfin tunani da kuma sanin yakamata, haka kawai dan faɗa na mata a cikin gida ba zai yi fushi ya bar ƴan uwansa ba, dole dai akwai wata a kasa, da alama kuma babbar al'amari ce a kasar da yasa suke ɓoyewa, dole akwai abin da suka yi wa daddyn Rimsha da har ya zuciya haka.

Jin ya yi shiru yasa Abba ya ce "Imran ka fara barci ne?" "A'a Abba ban yi barci ba". "Okey ai naji ka yi shiru ne, to dai shikenan sai da safe ni barci nake ji, da safe ka kirani mu yi magana akan Æ´ar wajen Maik". Yana kai karshen maganar ya katse kiran domin ya ga Ammie ta fara motsawa, kada ta tashi ta tsayar masu da bala'i, dama kunsan ido rufe take neman Imran É—in.

A ɓangaren Imran kuwa, ɗaura wayar saman bedside drawer ya yi yana tunanin menene gaskiyar abin da ya faru, waye a cikinsu Abba zai gaya mashi gaskiya? Menene yake faruwa a cikin wannan family'n? Ko dai na tambayi gwaggo Batula ce? No tun da Abba bai faɗa mani ba, ita ma ba zata gaya ba, waye ya kamata na samu ya gaya mani wannan magana.

To masu karatun na san zaku so jin me ya haɗa su, tun da Imran bai sani ba, bari ni na gaya maku, a shekarun baya kusan shekara 35 zuwa da 37 baya, mahaifin su daddyn Rimsha, wato kakansu Rimsha........❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E9-10

To masu karatun na san zaku so jin me ya haÉ—a su, tun da Imran bai sani ba, bari ni na gaya maku, a shekarun baya kusan shekara 35 zuwa da 37 baya, mahaifin su daddyn Rimsha, wato kakansu Rimsha, Dr Salman Sultan yana da rai a idanun jama'a, domin a yanzu ya zama gawa a idanun kowa da kowa, an rufe babinsa, sun shafe shi, shararren likita ne wadda ya shahara a duniya ta fannin surgery, mutun ne mai É—unbi dukiya ga kuma tarin masoya ta ko'ina da ina na bugawa a jarida, yana bala'in kaunar ahalinsa, wato family'nsa, mutun ne mai fara'a, saukin kai, mara son hayaniya, son jama'a, kyakkyawar gaske ne kamar dai Æ´aÆ´an nasa, fari ne tas tamkar balarabe, mutumin jahar Bauchi state ne mazauni KADUNA.

GARIN KADUNA.💋

Tampatsetsen gida ne wadda ya amsa sunan sa gida, two-storey building ne, wato gidan sama hawa biyu, gate ɗin gidan ma kawai abin kallo ne, gida ne wadda ake wa laƙani da aljannar duniya, gabaɗaya abubuwan da aka yi amfani dasu wajen inganta wannan gida da kawata shi white color ne, da alama mai gidan yana son farin color sosai, tsakar gidan yana da girmar gaske, akwai garden, fillin kwallo, katafaren pool, da kuma parking space, sai wajen wasan yara.

Wasu kyawawan fararen samari ne ke wasa a wajen wasan yasa dake a cikin gida, gabaɗaya wajen white color ne, kama da pentin waje, kayan wasan da aka zuba, kujerun lilo na wajen, dokunan wasa, ƙananan motoci da mashuna masu amsani da charji, wadda yaro yana iya hawa ya yi tafiya mai nisa, ke kunar hawa, da sauran abubuwan wasa na yara.
Chapter 24 · 0% Book details