Sashe 81
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin ba zata fahinci abin da take nufi bane yasa tai amfani da ƙwaƙwalwarta da basirar da Allah ya bata, tun da ta fahimci tabbas Anaya ɗin ta tsorata da jin babu mace, to bari ta yi amfani da hakan ta tsoratata dan ta kare mutuncinta, idan ta ce zata tsaya yi mata nasiha da bayani a kan me ake nufi da budurci, to tabbas ba zata fahinci komai ba a cikin ƙaramin lokaci haka, dan babu komai a kanta sai boko, dan haka sai ta ce mata "Tabbas Anaya, idan akwai abin da ya fi mutuwa ma mace zata yi, kuma idan kika yarda wani namiji ya taɓa ki ba ɗan uwanki na jini ba, zaki fara rashin lafiya mai tsanani, ko an kai ki asibiti ba zaki warke ba, kuraje zasu fito su ɓata miki jiki, daga nan sai ki mutu, idan kuma kika bari wani namiji ya yi zina dake, to a wajen ba sai kin motsa ba zaki mutu, ba zaki sake kallon su mummy ba, dan haka kada ki yarda Mr Emmanuel ya taɓa ki, kinga shi krista ne ma, yana taɓaki kaɗan dodansu na church zai shanye jininki ki mutu, dan haka sai ki kula sosai, kada ki yarda kowa ya taɓaki".
Zaro idanuwan nan ta yi tamkar zasu faɗo kasa, muryarta har rawa yake yi, ta gama tsorata, har wani zufa ta fara haɗawa, hankali a tashe ta ce "Yanzu Rimsha ita ma Fadila zata mutu?" "Kwarai kuwa, nan bada jimawa ba, dan haka kema idan kina son ki mutu to ki yarda wani ya taɓaki". Narai narai ta yi da idanu tamkar zata yi kuka, duk ta rasa me yake yi mata daɗi a duniyar baki ɗaya, yanzu shikenan idan wani ya taɓata zata mutu, Allah ya sota ma ita ba wanda ya taɓa taɓata sai yaya Feroz ɗinsu da daddy, ko Uncle Shitu bai taɓa taɓata ba, yau ta shiga uku ta lalace, duk wannan a zuciya take zantukan nan.
Ganin ta tsoratata sosai ne yasa Rimshar ta fara rarrashinta tare da kara mata karfin gwiwa da shawari ta yadda zata kula da kanta, daga karshe ta ce mata dama idan kana yaro wani ya taɓaka hakan ba zai faru da kai ba, sai ka girma ka fata period ne idan wani ya taɓaka zaka mutu, da yake ta san Anaya ɗin ta fara period, sai ta fito mata ta wannan hanyar, shiru ta yi tana tunanin tabbas last period ɗin da ta yi lokacin mummyn Rimshan sun zo gidansu sun ɗan yi kwana biyu, tabbas da ta gane tana yi ta tsawatar mata a kan kada ta yarda wani namiji ya taɓa ta, tuna hakan yasa ta kara gasgata zance Rimshar, bayan mummyn Rimsha ma, mai aikin gidansu ta yi mata faɗa sosai a kan kada ta kula maza, ita kuma mummynta tana can wajen Aiki, idan ta fita da safe sai karfe 6 na yamma take dawowa, dan haka bata sanin me ma yake wakana a cikin gidan, ranar da Anaya ɗin ma ta fara period ɗin, mummyn nasu bata sani ba, bata nan, mai aikinsu ne ta taimaka ta nuna mata komai, da mummyn ta dawo, iya always da sabbin pant ta bada aka sayo mata, daga haka ba wani bayani da ta kara mata, da alama ita ma mummyn babu ilimin addini sai zallar boko ne a kanta, irin waƴan nan iyaye na Anaya su suka fi yawa a duniyar mu ta yau, dan girman Allah mata mu kula, ƴaƴa hakki ne a kanku da Allah zai tambaye ku ranar gobe kiyama, amma wasu sai su zaɓi abin banza na duniya su yi watsi da tarbiyar ƴaƴansu, idan kuɗi ya bugasu sai su wani ɗebo ƴan aiki, Allah ba ƴan aiki zai tambaya ba, iyaye zai tambaya, ƴarki mace ki jata a jiki ku zama kawaye, duk wata matsalarta ya zama ke zata fara gayawa kafin kowa, kada ki yarda ace ƴarki tana da wata Aminiya da zata rinƙa gayawa sirrinta ba ke ba, ko da sunan wasa kada ki yarda da hakan, dan Allah iyaye a gyara, kada kuɗi da jin daɗin duniya su ruɗeki, akwai mutuwa a tafi a bar duk wani kuɗi da jin daɗin, Allah ya kyauta yasa mu dace ya kuma sa mu gyara, kuna dai ganin mummyn Rimsha baiwar Allah, dalilin tarbiya da ta basu yau ga shi nan anwayi gari al'umma da dama suna amfanuwa da ƴaƴa nata, badan Rimsha ba ya kuke tunanin rayuwar Anaya zai tafi? Ba dan Jehan ba ya kuke tunanin rayuwar Hanan, Maryam, Adiva, zasu kare? Ku duba irin kasadar da Jehan ta ɗauka a kan Maryam, duk dan me? Dan ta kare mata mutuncinta, da mummynsu bata gaya musu mahimmancin shi ba zasu matsa su shiga kasada dan kula da nasu har wanda ba nasu bane? Da ba'a gaya musu amfaninsa ba za su damu da kula da shi har haka ne? Da bata basu tarbiya ba, ya kuke tunanin rayuwarsu zai kasance? Ku duba yadda suka gogi wahalar rayuwa, Rimsha ta sha zullewa maza ga irinsu boda jamiu, duk dan me? Dan an gaya musu mahimmancinsa, so yana da kyau tun yara basu girma sosai ba, da sun ɗan fara hankali, ki zaunar da su, ki nitsar dasu, ki gaya musu amfaninsa, idan ta kama ki haɗa musu da tsoratarwa, duk dan rayuwarsu ne, a raba yara da kawaye, zina ta yi yawa, lesbian, wannan abu yana yi mini ciwo, yana damuna a cikin zuciyata, kaga yarinya ƴar 15 to 16 years ta san lesbian tana kuma yi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allahumma ajirni fi musibati, kuma duk abin da yarinya zata yi idan kuka bincika sanadiyar kawayen banza ne, ku duba rayuwar Aafia, dan Allah kirana a gareku iyaye, ku kula da ƴaƴa, ban da kawaye na kara faɗa, a rabasu da kawaye, tun tana karama ki cusa mata tsanar kawaye, idan ta tashi da shi shikenan kin huta, dan Allah a ja yara a jiki, waƴan nan bala'i na yanzu sun yi yawa, saɓon Allah ya yi yawa, Allah yasa mu gyara amin.
Anaya dai duk ta firgi ce ta tsorata, da kyar Rimsha ta shawo kanta ta yarda zata je office ɗin Mr Emmanuel ɗin, da farko ta ce ta fasa zuwa, ta hakura ta karɓi zero ɗin, sai da ta yi ta bata baki sannan ta miƙe jiki ba kwari duk a mace, tayi ligis ta nufi office ɗin nasa, ita kuma Rimsha ta gyara zama tana jiranta ta dawo su je top shop.
Baki É—auke da excuse ta shiga office É—in, yana zaune ya É—aura kafa É—aya bisa É—aya, ganinta yasa ya saki cool murmushi yana faÉ—in "I knew dama zaki zo, me matsalar?". Saman kujera ta zauna, jikinta sai kerma yake yi, murya a sanyaye ta fara magana "Mr Emmanuel i came to complain about my test results". Kafeta da shegun idanun nan nasa masu kama dana mujiya ya yi, yana kallonta tare da lashe baki kamar wani tsohon maye, idan baku manta ba na gaya muku, bayan halittar dara daran idanu da suka gada har da breast and hips, to ita ma fa Anaya akwai shi, sak Jehan É—in ne ba maraba, duk lafiyayyen namiji idan ya gansu sai ya kyatsa.
Miƙa mata hannu ya yi akan ta bashi paper ya gani, ba musu ta miƙo mishi hannunta sai rawa yake, karɓa ya yi tare da ajiyewa a gefe, a maimakon ya buɗe ya duba, sai bai duba ba, cike da maitarta ya fara magana da wata shegiyar muryarsa kamar an tada injin niƙa, tamkar wadda ya jima a cikin harkar shaye shaye. "Anaya Azharuddeen Bature, na sani, nasan kinci questions naki dukkan, amma kuma ai ni baki ci nawa rajarabawar bane yasa na baki zero a can".
Ɗan zaro idanu ta yi tana tambayarsa wani jarabawa kuma bayan wadda ya rubuta musu suka yi, ko dai ya yi wani bata sani bane? Da yake babu Allah a zuciyar bare ayi zancen kunya, sai ya fito kwaro kwaro ya gaya mata irin abin da yake da buƙata su yi kafin ya bata result mai kyau, a razane ta ce mishi ba zai yi wu ba, kai tsaye shi kuma ya ce mata to ba zata taɓa cin test na shi ba, kullum idan ta yi zero zata samu, idan dai har bata bashi kanta ba, to wlh ta shirya karɓar zero kullum, idan kuma ta shirya bashi kanta ko yanzu ne, to ta shiga toilet na shi dake cikin office ɗin zai zo ya sameta, tsabar rashin kunya har da ce mata ya yi ba zata jima ba, ba zai fi minti 20 ba anyi an gama, kuma kada ta damu ba wanda zai gane, dan ba zai yi mata yadda wani zai gane ba, da gudu ta miƙe ta yi waje dan ma kada ya ce zai taɓata, sai dukan uku uku kirjinta yake yi, har wani sara mata kanta yake yi, yanzu me zata cewa daddy da mummynta akan wannan test ɗin?.
Amma fa yadda Anaya ta yarda da boko ta ke kuma so, da Rimsha bata yi mata hakan ba, da tabbas dan ta ci test nata zata yarda mishi da abin da yake nema, dan dai kunga, da farko da Rimshar ta gaya mata, ba ta É—auki abin a wani matsala ba, Allah dai ya sota da rahma ya kuma tsareta a yau kam, sai dai bamu san me gaba zata haifar ba.
Kuka ne mai karfi ya kubce mata, a ɗari ta shiga class ɗin nasu, Rimsha na ganinta ta miƙe a razane tana ambatar sunanta tare da tambayarta lafiya, zuwa ta yi ya rungumeta tana kuka ba tare da ta yi magana ba, jijjigata Rimsha ta fara yi tana ambatar sunanta, "Anaya lafiya kuwa? Ki yi mini magana mana, dan girman Allah ki gaya mini kada ki saka na suma, kin ɗaga mini hankali sosai, wani abin ya yi miki ne?".