← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 121

Sashe 96

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya kunna wuta ya zo ne ya wuce ciki, yadda ya barta haka ya dawo ya sameta, alamar abin ya yi mata mugunciwo sosai, sai kuka take yi, ko kallon in da take bai yi ba ya haura sama abinsa, ya ji daɗi da ya kona mata rai ba tare da ya taɓa lafiyar jikinta ba, zaman dirshan ta yi a wajen tana kuka tana jan Allah ya isanta a cikin zuciyarta,

Fridge na ɗakin daddy ya fara kunnawa kafin ya sake saukowa kasa zuwa wajen mota ya kwaso kayan drinks da suka sawo ya dawo, a cikin fridge ɗin ya zuba su, har lokacin tana zaune a palo tana kuka, tamkar bai san da zaman ta a wajen ba, toilet ya nufa ya yi wanka tare da shiryawa cikin pajama ya fito zuwa balcony dan ya duba mattress ɗin, ya jike sharkaf da ruwa, ɗagawa ya yi ya tsayar a tsaye tare da jingina shi da jikin karafunan wajen, sannan ya nufi bedroom ɗin mum, nata mattress ɗin ya ɗauko zuwa bedroom ɗin dad, da yake girman gadon nasu ɗaya, kunna Ac ya yi sannan ya shinfiɗa bed sheet ya haye ya kwanta tare da ɗauko wayarsa da ya ɗaura a saman bedside drawer tun shigowarsa, da yake wayar tasa wata Prof ce sai bata yi komai ba da ruwan sama ya jiƙasu, ɗan latsa wayar kaɗan ya yi kafin barci ta yi awon gaba da shi, ita kuma sai da ta gama cin kukanta har sai da idanunta suka kumbura, sannan ta miƙe zuwa bedroom nasu ta yi wanka tare da shiryawa cikin wasu shegun riga da wando, jeans ne baki mai bala'in kyau, ya kamata sosai duk da yake na Jehan ce, amma ta ɗan yi kiba shiyasa ya matseta sosai, sai ƴar riga mai karamar hannu fara, hand dryer ta ɗauko tare da junawa ta busar da gashinta, cike da tsoro ta fito ta nufi ɗakin daddyn nata, dan wlh ko za'a kasheta ba zata kwanta ita kaɗai a ɗaki ba, salon wasu karti su shigo, gara mata shi ɗin dai duk da tana jin haushinsa, ga shi baya rufe gidan, sai ya bari a buɗe kayansa, ko alamar tsoro babu a tattare da shi. Da sallama ta shiga cikin ɗakin, sai faman kumbure kumbure take yi, already lokacin ma ya jima da yin barci abinsa, harararsa ta yi tare da kara jan Allah ya isa a cikin zuciyarta kafin ta kwanta saman sofa tana mai jin kuna a cikin ranta, ga bala'in yunwa.

A ɓangaren gidan Hajiyar daɗi kuwa, bayan sun dawo daga super market ɗin, sun sha sayayya ba karya, Jehan sai murna take yi ba kaɗan ba, a hankali Hjy ta turo kofa ta shigo cikin ɗakin nasu, daga ɗan bakin kofa ta tsaya tana faɗin "Jehan". "Na'am mummyn". Ta amsa tana miƙewa zaune, "Ki shirya, ki tsantsara kwalliya mai shegen kyau kina da bako". Cool murmushi ta saki, ita da bata murmushi a baya, "To mummy wani irin kaya zan saka?". Shiru Hajiyar ta ɗan yi kafin ta ce "Baƙon na musamman ne, ɗaya ne daga cikin jigo na wannan gida, kusan zan ce miki shi ya kafa mu da har muka kai izuwa yanzu, ya nuna ra'ayinsa a kanki sosai, dan haka ki saka short zuwa gwiwa, da kuma riga mai karamin hannu ma it's okey". Da fara'ata ta amsa da to tare da miƙewa ta shige toilet, ita kuma Hajiyar ta nufi waje, Maryam Adiva duk suna baje a sama gado sun yi ɗai'ɗai daga su sai guntayen wando zuwa cinya da ƴar riga da bata wuci cibiya ba, sai taunar chewing gum suke yi.

Wanka ta yi ta fito ta shirya kamar yadda suka yi da Hjy, sai murmushi su Adiva suke yi suna yaba kyan da ta yi, wayar Adivar ta É—auka tare da nufar waje, sai sheki gashin kanta yake yi, ya sha gyara sosai a fitar da suka yi É—azun, ta yi kyau kam ba karya, office É—in Hjy ta nufa, sai murmushi take yi, ba sallama ta afka ciki, Hjy na zaune a saman dankareren lallausan kujerarta, ga sanyin Ac na bugata, Hamshakiya mandiya, sai wani washe baki take yi taga ruwan kuÉ—i.

Ganin Jehan ɗin yasa ta kara washe baki tana faɗin "Jehan ga alhajin da yake bukatarki, ya ce ma tafiya zaku yi da shi sai jibi zai dawo da ke". Ba musu ta amsa da okey mummy tare da juyawa ta kai kallonta kansa, wani irin bugu gabanta ya bada, zaro idanun nan nata ta yi tana kallon shi da mamaki, ko mutuwa ta yi ta dawo ba zata manta da wannan fuska tasa ba a rayuwarta, ganin face ɗin nasa kuma yasa ta tuna da wace ce ita, me ya kawota gidan, menene yake faruwa, da ni daku munsan addu'ar da iyayenta suke yi mata ne ya yi sanadiyar dawowarta cikin hayyacinta, amma ita bata sani ba, bata kuma nuna musu ta dawo cikin hayyacinta ɗin ba, sai ta ce to su je ta shirya, magani Hjy ta bata akan idan taje kafin su kwanta da alhajin ta sha dan gudun ɗaukar ciki, ba musu ta karɓa tare da wucewa ta yi gaba tana tunanin yadda zata ɓullowa lamarin, duk sai ta ji wani irin, dressing nan da ta yi sam bata ji daɗin shi ba, amma saboda akwai abin da ta kudurta a ranta, sai ta daure ta shanye, bata nuna kamar kayan sun sanyata bakin ciki ba.

Shi kuma alhajin ya miƙe zai bi bayanta Hjy ta tsayar da shi tana yi mishi magana a kan dan Allah kada ya bari Jahan ta ɗauki ciki, wani irin shu'umin murmushi ya yi, dan shi yasan me ya shirya a kan Jehan ɗin, yasan Nawazudden sosai, akwai ƴar tsama a tsakaninsu, so amfani da Jehan ɗin zai yi ya zuba mata tsafi a ciki ta mutu dan babanta ya yi mishi wani laifi da ta shafe su can, sai dai bai nunawa Hjy hakan ba, ya ce mata ba komai zai kula, da haka suka yi sallama ya bi Jehan suka fita.

Tun da suka É—auki hanya barin gidan ta kurawa hanyar idanu sai kallo take yi, shi kuma Alhajin bai lura ba yana tuki, da haka har suka fita garin Abuja suka É—auki hanyar Kaduna. Sai karfe 8 na dare suka shiga garin Kaduna, kai tsaye wani katafaren gidansa dake unguwar su Lion ya nufa da ita, guest house ne, akwai Æ´an'sanda biyu dake tsaron gidan, da kuma Æ´ar aiki guda É—aya, hakan zai nuna maka babban mutun ne sosai, da alama kuma ya aminta da waÆ´an da suke cikin gidan ne. Ciki suka shige, tana biye da shi babu musu kamar wata rakumi da akala.

Cikin wani tampatsetsen bedroom ya shiga da ita, sai kallon hanya take yi, duk in da suka bi ta gani kuma ta haddace, suna shiga ya fara cire kayan jikinsa, ya rage daga shi sai shot kafin ya shiga cikin toilet dan yin haɗe haɗensa na tsafin nasa, tana zaune tana tunanin me mafita, me yakamata ta yi? Can wani idea ya faɗo mata na wani labari da ta taɓa cin karo da shi a Media, wata ta yi wa mijinta, shiru ta yi tana jiran fitowarsa, tsabar ma mugunta ya shirya mata sai bai ce ta yi wanka ba, sauri sauri kawai yake yi ya aiwatar da abin da yake so, saman gado ya hau tare da cire shot nasa yana faɗin ta zo mana, tsirara haihuwar uwasa ya yi a gabanta, yau shi ne karo na biyu da ta ga wannan tashin hankali, amma ta daure ta danne bata nuna mishi zata tirje ba, cikin dakiyar zuciya ta ce "Ina son shan ruwa mai sanyi da fruits kafin mu yi komai, kai baka ga hanyar da muka sha bane? Ai ina jin yunwa".

Ɗan kwaɓe fuska ya yi kafin ya ɗauko waya ya kira mai aiki a kan ta kawo mata, "Yauwa Alhaji bana son a yanka mini fruits ɗin dan ina da kyankyani sosai, ni zan yanka da kai'na dan bana son datti". Dariya ya yi yana faɗin "Ai dama baki yi kalar datti ba". Murmushi dole ita ma ta yi tana mai duba time a wayar Adiva dake hannunta, shi kam ko a jikinsa, dan yasan sai Hjy ta saye imaninsu ta yadda basu yi wa mutun musu kafin ta fara ɗaurasu a network, Jehan kuma akwai basira, ta fahimci hakan ne shiyasa ma bata nuna musu ita ta fita daga tarkonsu ba, tana ciki ba zata yi musu musu ba ta nuna.

Ba kunya ba tsoron Allah mutumin nan yana kwance tsirara har mai aikin nan nasa ta kawo mishi abin da ya bukata, da alama shi da mai aikin ma suna sheke ayarsu tun da bai rufe jikinsa ba har ta shigo. Saman bedside drawer ta ɗaura tray ɗin tare da yi wa Jehan sannu ta juya ta fita, fruits ne irinsu Apple ayaba lemu da sauransu, sai wata ƴar madaidaiciyar wuƙa mai kaifin bala'i tare da robar ruwa mai sanyi da glass cup kwara ɗaya a saman tray ɗin.

Natowa Jehan É—in ta yi tare da fara É—aukar ruwa ta yi bismillahi ta buÉ—e robar ta sha, dai'dai lokacin kuma a ka kira shi a waya, da yake wayar tana kusa da shi sai ya É—aukota yana faÉ—in "Bari ma na sanyata a airplane mode dan kada a takura mana da kiraye kiraye muna tsaka da jin daÉ—in mu, mutane basu san lokacin da ya dace su kira mutun ba, su dai idan bukatarsu ya taso shikenan........" Bai kai karshen maganar ba ya ji wani bakin azaba ya ziyarcesa, da iya karfinta ta sanya wukar da aka kawo mata dan yanka fruits ta yanke mishi gabansa wato bananarsa, daga tushensa ta yanke ba ma sama sama ba.

Tana yankewa ta yi wurgi da wukar tare da É—aukar wayarta ta fisge nashi dake hannunsa ma ta haÉ—a dukka biyu ta nufi waje da uban hudu,. Ihu ya kurma tare yunkurawa, amma ya kasa tashi, nan take jini ya fara gangarowa, ihu ya cigaba da waje muryar nan tasa yana kurmawa.
Chapter 96 · 0% Book details