← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 121

Sashe 50

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Lallai da kuwa Lion ya tabka babban kuskuren da ba zai iya gyarawa ba a rayuwarmu, yanzu idan ma ban da shi da neman magana, ko in ce da san gallazawa rai, ai yasan wannan zane daga ido ma ba ta yanzu bace, kowa ya ga wannan zane yasan ta jima, abinda har ta fara bin fatar jikinki, amma ba komai ina mai baki hakuri a madadinsa, kuma In Sha Allah daga yau kin dai'na zuwa in da yake, Aseef yana nan zuwa gobe, dama shi ne mai kai mishi abinci, zaki huta my sister, rabu da shi Allah yana ganin mu ai". Ya kai karshen maganar yana jawo mata zip ɗin rigar tata sama, sam bai ji daɗin abin da ɗan uwan nasa ya yi ba, yasan da cewa yana sane zanen ya jima, kawai bakar mugunta ce sai ya gallazawa ƴar mutane Baiwar Allah, amma ba komai zai gane kurensa, zai ɗanɗani ƙuɗarsa ne.

Bayan ya gama ja mata zip ɗin rigar ya goge mata hawaye tas kafin ya miƙe tsaye yana mai dawo da kallonsa a kan Akila da ta tsare shi da idanu. "Heartbeat sarkin rigima, yanzu kuma wani sabon rigima zaki yi mini?" Ya yi maganar cikin zolaya, kuma duk cikin harshen turanci suke magana.

ÆŠan rufe fuska ta yi da hannunta tana murmushi bata ce komai ba, wucewa ya yi ya fice daga É—akin ya koma wajen É—an uwan nasa.

Yana fita ta koma ta kwanta ƙwaƙwalwarta na tariyo mata abin da ya faro, kwayar idanunsa kawai take gani cikin nata, matsowa kusa da ita Akila ta yi ta shiga rarrashinta tare da bata baki.

A ɓangaren Areef kuwa, abinci ya je ya zubawa ɗan uwan nasa, a tare suka ci suka ƙoshi, da kansa ya tattare kayan ya fitar tare da dawowa ya ɗauki chemical ɗin ya mai da shi mazauninsa, a lokacin shi kuma Lion already ya koma saman bed nasa ya kwanta, abu biyu suka tsaya mishi a zuciya tun zuwan shi NIGERIA, na farko Yarinyar da ta kira sunansa kai tsaye a ranar da ya sauƙa gidansu Imran, har cikin ransa yanzu da ya ga sunansa a kirjin Rimsha zuciyarsa ya bashi ita ce wannan yarinya, abu na biyu kuma fuskarta, tabbas ya taɓa kallon mai irin wannan fuska sak a tare da Josephine, to waye kenan? Wan can dai ba yarinya ba ce tare da Josephine, dattijuwa ce, kada ku mance kowa da yadda yake kallon mutum, wani zai ga kayi mishi kama da wani na shi, kai kuma ba zaka ga kamannin ba, to shi dai tabbas ya ga mai irin wannan fuska tata sak a tare da Josephine, sai dai ya rasa a ina ne ya taɓa ganin nasu tare, shiru ya yi yana faɗaɗa tunaninsa a ina ne ya ga hakan.

Gefensa Areef ya zo ya zauna tare da ɗan taɓa shi, juyo da dara daran blue eyes nasa ya yi izuwa kan Areef ɗin, shiru bai ce komai ba, cikin natsuwa Areef ya fara magana. "My blood na san kana son farincikin mu fiye da naka, na san kana son abin da muke so, na san baka da wani burin da ta wuce ka ganmu a cikin farinciki, duk in da muka je muna alfahari da hakan, muna jin daɗin hakan, dan Allah yau ina neman Alfarma a wajenka, ba dan ni zaka yi ba, please and please dan girman Allah zaka yi, ina son ka rinƙa danne zuciyarka a kan sister, wlh tana da problem a kanta, ta shiga ta shin hankali, ko in ce taga tashin hankali da ya wuce shekarunta, ya wuci girman ƙwaƙwalwarta, hakan yasa take da yawan razana, to please tana tsoronka kamar ta mutu, tana tsoron ganin kwayar idanunka, idan har ka cigaba da kallonta ma kawai wlh kana iya ɗaukar gawarta, ni zaka yi wa, ina kaunarta, ina kaunarta fiye da tunaninka, idan tana farinciki nima ina yi, idan ta yi kuka, ko ban yi a zahiri ba, ina yi a cikin zuciyata, kasan dai bawa baya sanyawa kansa soyayya ko? To ba ni na sanyawa kaina sonta ita da mahaifinta ba, Allah ya jarrabeni da hakan, ka taimaka mini tun da Aseef zai zo gobe, ina son sister ta daina kawo maka abinci, ta daina zuwa kusa da kai, yanzu haka dole Prof ya ɗauketa zuwa asibiti, idan ba haka ba, akwai gagarumin matsala". Ya kai karshen maganar cikin wata iriyar murya mai ɗauke da damuwa ainun, tabbas duk abin da yake damun Rimsha ya sani, baiwar Allah bala'in da ta rinƙa gani na Daular Mutuwa ya birkita mata kwakwalwa, ko shi Dr Nawid bai gano ainahin damunwanta ba, wlh bala'in dake Daular Mutuwa ya fi karfin ƙwaƙwalwarta ya ɗauka, hakan ya haifar mata da razana, Areef ya gano hakan ne ta hanyar dubata da ya taɓa yi da bata da lafiya, hakan yasa take yawan suma, kuma Areef ya yi gaskiya idan ta cigaba da zama inuwa ɗaya da Lion to wata rana za'a iya ɗaukar gawarta a wajen.

Shiru ya yi bai tanka É—an uwan nasa ba, shima Areef É—in shiru ya yi, almost 30 mins suna haka kafin Lion ya ce "Haka kake so?" GyaÉ—a mishi kai ya yi alamar e, jinjina kai ya yi alamar to ya yi accepted, wani irin farinciki ne ya dira mishi a cikin zuciyarsa, da sauri ya rungumi É—an uwan nasa yana zuba mishi ruwan godiya tare da ruwan Albarka, shikenan yanzu Rimsha ta tashi daga Æ´ar aiki, ta yi free wow abin ya yi daÉ—i, yau saboda Areef Lion ya canza magana, saboda faricniki TRIPLETS kai abin ya kayatar.

Sun jima suna hira, ko da sunan wasa Lion bai sanar da Areef face ɗin Rimsha ya yi mishi kama da na wata da ya taɓa gani tare da Josephine ba, ya bar abin a ransa zan yi bincike a kan idan ya sami lokaci, yau dai kwanan faricniki Areef ya yi, shi kuma Saif mafarkin Josephine kamar kullum ya kwana yana yi.

A ɓangaren Rimsha da Akila kuwa, Rimsha dai barci ɓarawo ne ya yi awon gaba da ita, ita kuma Akila sai da suka yi waya da Umaisha kafin ta raba dare da sahibin nata suna hira, sai Misalin karfe 2 na dare suka hakura ba dan sun so ba, ko kaɗan a hirar tasu bata kawo mishi zancen cewa ta gane shi ko makamancin haka ba, shima bai kawo mata zancen ba, sun dai zuba soyayyarsu kamar yadda suka saba.

Wayar da suka yi da Umaisha ba komai bane face magana a kan yajin da Akil ya yi, mu koma baya kaÉ—an mu ji tattaunawar tasu kafin mu cigaba da tafiya.

Kiranta Umaisha ta yi, tamkar zata yi kuka ta fara magana "Hello Heartbeat". Cike da kulawa Akilar ta ce "Aunty Umaisha ta yaya Akil, to ya ake ciki ne? Ya naji muryarki haka? Ko dai babyna ne yake addaba miki? Kin san nina yi mishi huÉ—uba ai, na ce ya tabbatar yana takura miki sosai, ya yi ta naushinki a ciki har sai kin yabawa aya zakinta". Tana magana tana murmushi, turnuke fuska Umaisha É—in ta yi, tamkar zata yi kuka ta ce "Ni Heartbeat ba wannan ba, dan girman Allah wata alfarma nake nema daga gare ki". Da sauri ta ce "Wace alfatma kuma?"

"Dan Allah heartbeat ki kira mani shi a waya, ki ce mashi wlh na tuba bazan kara ba, tun fa da safe ya yi fushi ya fita, kuma wlh kafin ya fita sai da ya ce mini ya yi yaji sai ya yi sati biyu ko wata ɗaya zai dawo, na ɗauka wasa yake yi kuma raina a ɓace na ce mashi kada ma ya dawo ma in yana so, ashe wlh da gaske yake yi, yanzu na kirashi yafi miss call hamsin ya ki ɗagawa, kuma wlh ni nasan yana ganin kirata, ɗauka ce kawai ba zai yi ba, na yi mashi massages har na gaji babu reply, dan girman Allah ki kirashi nasan zai ɗauki kiranki, ba zan taɓa iya yin barci ba har sai ya dawo". Kwashewa da dariya Akila ta yi har da riƙe ciki, iskanci Umaisha da Akil ya wuce misali.

"Heartbeat ki tausaya mini ko dan saboda babynki". Tana magana murya a dashe taci kuka ta ƙoshi, ita kuma Akila tsabar shakiyanci tana binta da to na iyashege, sai da Umaishar ta gama maganarta tas, sannan Akilar ta ce "Kai amma yaya Akil ya iya, wato ma shi ne ya yi yaji kenan? Wayyo cikina, ai kaɗan ma kika gani, ba ke duk abin da na gaya maki baki ɗauka ba, wlh yaya Akil ustadz ne, koyi da annabi yake yi, shiyasa shi ya yi yaji ya bar miki gidan, nasan yana masallaci a yanzu, ya tare a can, abin da zai faru kawai ki jira sai ya cika wa'adinsa da ya ɗebe". Ta kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariyar shakiyanci, katse kiran kawai Umaisha ta yi, dan ta lura Akila zata kara mata zafi a kan zafi ne.

Bayan ta katse kiran ne Akilar ta jawo bargo ta shiga kafin nan ta rubutawa Akil massage a kan halin da Matarsa ke ciki, bayan ya tura mishi ne bai fi da minti goma ba masoyin nata ya kira, shi ne suka fara hira har karfe biyu na dare, to kun ji yadda a ka yi.

Washegari karfe 8 na safe, Akil ya zo ya É—auki Akila ya mai da ita gida, kamar yadda Imran ya faÉ—a, sun sha kukan rabuwa da Rimsha kamar ba gobe, sai da Areef ya ja Rimsha zuwa cikin gida, ita kuma Akila Imran ya turata cikin motar Akil suka nufi gida.

Ɗaki Areef ya mayar da Rimsha tare da yi mata albishir a kan daga yau ta bar aiki, school kawai zata rinƙa zuwa ta dawo, sai wanka da tsala kwalliya, sai kuma barci, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, dama kamar zata yi kuka, daurewa kawai take yi tana yin wannan aiki, amma badan haka ba, Allah ne kaɗai yasan yadda take ji a duk san da ta ɗauki abincin da nufin ta kai wa Lion.
Chapter 50 · 0% Book details