Sashe 103
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Ammie ta kariso wajen tana faÉ—in "Ku nuna mini wace ce Æ´ar Maik a cikinsu?". Akila ce ta nuna mata Jelly, murmushi kaÉ—an ta yi dan idan baku manta ba, bata da yawan fara'a sosai, "A dole Æ´ar Maik ta zama haka ai, Maik namu, kai amma ina kewarsa wlh, ya ce Ammie idan kika kuskura yau kika yi mana irin miyar rannan sai na yi miki saki uku". Tana magana tana É—an murmushi.
Kallon juna Akil da Imran suka yi suna mamakin mahaifiyar tasu, ya akayi yanzu kuma take son family'n Abbansu? Anya Ammie sune kuwa? Kai akwai dai wani abin, ita kanta Akila ta sha ruwan mamaki, kashe musu ido Abba ya yi akan kada su yi mata wata magana da bata dace ba, kada su kuskura su tuna mata ta taɓa cewa bata son family'nsa, dan idan suka tuna mata za'a iya samun matsala tun da yanzu ne ta sami lafiyar ba'a jimaba, to tana iya komawa ruwa idan suka mata wata magana. Ganin abin da Abban nasu ya nuna musu na su yi shiru ne yasa suka yi shiru suka danne mamakinsu.
Hannun jelly ta riƙo tana faɗin "Tashi na ganki, ai ƴar Maik ƴar ɗakina ce, babanki a hannuna ya zauna tun yana ɗan shekara 10 zuwa 18 sanan ya koma wajen Deen, saboda Deen ya matsa lallai dole ya koma wajensa, ban so rabuwa da shi ba a lokacin, amma ba yadda zan yi ne, Deen ya kureni a lokacin, sai dai ko da ya koma wajen Deen ɗin yana yawan zuwa wajena mu wuni dan ya fi son zama da ni shi ma". Miƙewa Jellyn ta yi da nufin ta bita zuwa saman nata kujerar, ƴar kara ta saka lokacin data fara ɗaga kafarta.
Cikin sauri Imran ya ce "Ammie bata da lafiya fa". Yana magana yana sunkuyar da kai kasa, tuna abin da Abba ya gaya mata na yaronta ya angwance ne yasa ta kalle shi tana watsa mishi harara, tare da riƙo hannun Umaisha dake ta binsu da kallo, mamakin Ammi ya hanata yin magana, ganin abin take kamar ba gaske bane, dan idan baku manta ba, ita ta gasu ba kaɗan ba a hannun Ammie, sai dai kuma ita Ammie bazata iya tuna cewa ta wahalar da ita ba, Allah sarki rayuwa kenan, yanzu ga shi Umaisha ɗin ta riƙeta a ranta sosai.
Rungumosu dukkansu biyu ta yi a gefe da gefen kafadarta tare da karisawa da su zuwa saman sofa mai zaman mutun uku a hankali, tare da su ta zauna tana mai tsananin jin kaunarsu a ranta, wai surukunta ne waÆ´an nan, matan Æ´aÆ´anta, kai farinciki ba'a magana.
Zama saman sofa mai zaman mutun 2 Abba ya yi yana binsu da kallo, Akila dai ta lula duniyar chatting da sahibinta dan tun ɗazun yake ta tura mata saƙonnin soyayya da su flowers ta WhatsApp.
"Abban Imran bari mu haura sama da matar Imran ina zuwa". Cewar Ammie, ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta riko hannun jelly'n dan ta mikar da ita, bayan ta miƙe ta ɗan rungumota suka nufi sama, dan ta san matsalar, Jellyn bata shiga ruwan zafi mai kyau bane, daga ita har Imran ɗin ba wanda ya yi tunanin idan ta shiga ruwan zafi tana gasa gaban nata da kyau zata sami sauƙi. Suna haurawa sama su kuma su Imran suka fara gaishe da Abban.
Bedroom nata ta wuce da ita, saman bakin gado ta zaunar da ita kafin ta nufi toilet, sai sannu take ce mata, ruwa mai zafi daidai ta haɗa mata tare da zuba mata wasu sinadarai nata da take amfani da su, ciki har da man zogale, da man zaitun, na tane wadda ta jima take amfani da su tun kafin ta sami wannan matsalar, bayan ta samu matsala bata amfani dasu, jiya Abba ya sake sayo mata su tun da ta dawo cikin hayyacinta, sai ta cigaba da amfani da su kamar da, suna gyara mace sosai, bayan ta kammala, daga karshe ta zuba mata ruwan jikakken sassaken mangoro da take jiƙawa, dan yana matikar kashe sanyin gabar mace ba kaɗan ba, bare ma ita jelly da take yanzu aka buɗeta, tana buƙatar ire iren su dan kada a sami wata matsala.
Dawowa cikin ɗakin ta yi, da kanta ta cire mata kayan jikinta, Jellyn bata yi mata kaddama ba, dan idan baku manta ba, ita jelly rainon namiji ne, duk da daddyn ya tsawatar mata a kan wada ta yarda wani ya taɓata ma bare ya cire mata kaya, amma ta san wannan maman Imran ne babu damuwa, kuma ita jelly bata da kunya ko kaɗan, shi ne yasa bata yi wani gardama ba, ta tsaya ta cire mata komai tas, ya rage daga ita sai pant ta kama hannunta zuwa cikin toilet ɗin, Allah sarki duniya kenan, yau ta sami sabuwar uwa, Allahu Akbar Allah mai yin yadda ya so da bawansa, ya bashi a lokacin da yake so, ya kuma karɓa a lokacin da yake so, ya karɓi mahaifiyarta tun ranar da ta zo duniya, yau kuma cikin ni'imarsa ya sake bata wata uwar, ba abin da zamu ce sai dai Alhadulillah.
Sai da suka isa bakin baf É—in ne ta tsaya ta cire mata pant É—in nata kafin ta ce to ta shiga, da yake jikin nata dai ba kwari, bata musawa Ammie ba, sai okey kawai take binta da shi, da yake da turanci Ammien take yi mata magana.
Da kyar ta iya zama a cikin ruwan saboda zafin shi, sai Weldon Ammien take ta ce mata, ganin ta É—an jima ruwan yana ratsata sosai ne yasa Ammien ta fita zuwa palon kasa, hira ta samesu suna ta zubawa.
"Akila ta shi ki kawo mini kayanki ɗakina yanzu". "Okey my Ammie" . Ta amsa tare da miƙewa ta nufi saman. Dawo da kallonta a kan Akil Ammien ta yi tana faɗin "Son kar dai ka gaya mini abin da nake hasashe gaskiya ce?". Da sauri ya ɗago yana kallonta da mamaki "Ammie me kike hasashe kuma?" "Matarka ciki gareta mana". Ɗan kasa ya yi da kansa yana faɗin "E Ammie gaskiya ce, zai kai wata wajen biyu ma yanzu". Zaro idanu ta yi tare da nufar in da Umaisha ɗin take zaune tana faɗin "Wayyo shi ne a rasa wanda zai yi mini albishir a cikin ku? Ni yau ina zan saka kai'na saboda tsantsar farinciki, Allah nagode maka, ya Allah Alhadulillah". Tana magana ta rungume Umaisha ɗin sosai tana mai jin tsantsar farinciki, ita kuma Umaishar ta kasa sakin jiki da ita, sai ɗan murmushi da take yi, a zahirin gaskiya tsoron Ammie take yi kamar ta mutu, dan ma tafiyar Ammie sama da ta yi da jelly Abba ya ɗan yi musu bayani a kan abubuwan da suka faru a baya Ammien bata cikin hayyacinta ne, amma duk da haka ita ta kasa sakin jiki da Ita.
Ammie kuwa yau murna a wajenta ba'a magana, Imran ya angwance, ya kawo mata jinyar amayar tasa, shi kuma Akil ya kawo mata tsarabar yaron ciki, kai abin sai godiya, yau murmushi bakinta yaki rufuwa, sai godiya take zubawa Allah tare da kirari mara adadi, haka ta tasa Umaisha a gaba a kan me zata ci? Me take jin ƙoɗayi? Me baby yake so? Ta faɗi koma me ne yanzu aiki da gamawa za'a kawo mata, to da yake na gaya muku Umaisha ta kasa sakin jikinta, sai ta rinƙa nokewa tana faɗin babu komai, babu abin da take so, kuma a zahirin gaskiya tun da suka shigo da ta ji kamshin girkin Ammien take haɗiyar yawu, cikinta har wani kulle mata yake yi saboda yadda daddaɗar kamshin yake dukan hancinta, burinta kawai ta ci wannan girki, sai dai kash ta kasa sanar da kowa abin da yake ranta, ta so su keɓe da mijinta ta gaya mishi, amma ba hali, yanzu kuma an tambayeta me take so ta kasa faɗa ta ce babu komai.
Sai da Ammie ta yi maya tambaya yafi baki goma, amma amsa ɗaya, shi ne babu komai, sai da Abba ya ce wai ta kyaleta mana ko dole sai ta cusa mata sha'awar abu ne, sannan ne ta kyaleta ta koma wajen jelly dan ta dubata. Kamar yadda ta barta haka ta dawo ta sameta, ruwan ya yi sanyi, riƙo hannunta ta yi tare da taimaka mata ta fito daga cikin baff ɗin ta tsaya a gefe guda, buɗe ruwan Ammien ta yi ya fita tare da haɗa wani mai ɗan ɗumi ta ce ta shiga bari ta yi mata wanka, ba musu ta shiga, Ammie da ƙoƙari tas ta kwanketa, dan ita gani take Akila ma bata wuce ta kamata ta yi mata wanka ba, kunga Akila kuma ai ta girmi jelly wajen da shekaru uku kenan.
Bayan ta kammala ta tsaneta da toilet tare da ɗaura mata mai ɗan girma a kirjinta ta ja hannunta zuwa cikin ɗakin, gaban mirror ta tsayar da ita a in da ta shafe ta da mayuka masu kyau da tsada, sannan ta zuba mata turaruka masu kyau da daɗin kamshi kafin ta ɗauko kayan da Akila ta ajiye mata a saman gado ta dawo gaban mirror, har da bra Akila ta kawo mata, dan haka sai ta shirya ƴar tata tsab tare da sanya mata bra ɗin, dama suna nan tula tulan ba a sanya bra bama, da aka sanya ba'a magana, sai suka kara cika waje, simple make up ta yi mata tare da kara fesa mata turare a saman doguwar rigar tata da ta sanya mata, ba karya ta haɗu iya haɗuwa, yafa mata gyalen rigar ta yi tare da riƙo hannunta suka nufi palo, Masha Allah yanzu kafan nata ya sake mata, gaba nata ma ya dai'na yi mata zafi, ya dawo dai'dai.
Tun daga suka sako kafarsu a saman benen Imran ya zubawa tauraruwar tasa idanu, ta yi kyau ba karya, ji yake yi tamkar ya tashi ya rungumo kayarsa, amma ina ba hali, dole ya danne dan saboda su Abba, kuma ya ga ma sai harararsa ta gefen ido take yi, da alama zasu sha dirama ba kaÉ—an ba, dan fushi take yi da shi.