← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 121

Sashe 93

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Kina so mu zo ne my Rimsha?" Cewar Areef, da sauri ta gyaɗa mishi kai alamar e, "To shikenan zamu zo, amma ke da kike tare da Lion me abin tsoro? Kada ki damu, ni nasan waye ɗan uwana, yana kaunarmu kuma yana kaunar dik abin da muke kauna, muna kaunarki ya sani, ba zai yaɓa watsa mana kasa a idanu ba, yana son gamin mu cikin farinciki fiye da kansa, so ki kwantar da hankalinki, dole zai baki farinciki dan yasan idan ya yi hakan kamar mu ya yi wa, in kin yi farinciki tamkar mune muka yi, akasin hakan ma, mune muka yi"......... A nan wajen Areef ya yi amfani da basira ne ya ɗaure Lion da magana, ya gayawa Rimsha Lion yana sonsu fiye da kansa, dan haka zai kula da ita, ya san cewa idan ya faɗi hakan, kenan suna da kwarin gwiwa sosai a kan shi, hakan zai sa Lion ɗin ya bata kulawa dan kada ya watsawa ƴan uwan nasa kasa a idanu, Areef ba dai basira ba, akwai basirar na wuce misali.

Zata yi magana Lion ya miƙa mata waƴar tare da miƙewa ya bar wajen zuwa ɗakin daddynta, yana tafiya Areef ya ce "Kina ji sister?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e tana ji, "Lion ba ya cin abincin restaurant, ba ma zai taɓa ci ba komai wuya komai daɗi, duk in da zai je in dai ba mai yi mishi girki, to Maltina da kyau sune kawai suke zama abincinsa, dan su hannun baya taɓa cikinsu a cewarsa, kinga kwai ma ko an dafa ai ba'a taɓa cikin ba sai bayan, bayan kuma ɓarewa za'ayi a zubar, dan haka ki rinƙa dafa mishi kwai, dan Allah kada ki bari ɗan uwana ya zauna da yunwa, wlh bashi da juriyar yunwa, sai dai baya cin abinci sosai, iya Maltina idan ya sha, yana iya ƙoshi, amma idan lokacin cin abincinsa ya yi zai shiga damuwa dan baya jure yunwa, ki rinƙa bashi Maltina da kwai, na san ba zai iya cin abincinku na Nigeria ba, dan haka ba sai kin sha wahalar girkawa ba kin ji ko?" "To yaya Areef amma yanzu da na bashi tea namu na nan ya sha wlh, ka ga cup nashi ma har ya kusa shanyewa, kaɗan ya rage".

Ba Areef kawai ba, har ta Aseef sai da ya zaro idanu waje, anya kuwa,? Aseef ya tambayi kansa da kansa a cikin zuciyarsa, Areef kuwa cewa ya yi "Ba abin mamaki bane dan ya sha, na san yunwa yake ji shiyasa ya sha, na gaya miki baya da juriyar yunwa ko kaɗan, dole zai sha dan bashi da mafita, ba zai iya cin abincin waje ba duk wuya duk daɗi, yanzu kuna da Maltina a gidan naku ne ko babu?". Ɗan waigawa ta yi tana kallon shi yana nufota ya fito daga bedroom na daddynta, "Yaya Areef babu, babu Maltina kuma babu wuta a gidan". Zai yi magana Lion ya miƙa mata hannu a kan ta bashi wayarsa, babu musu ta miƙa mishi cikin girmamawa a kuma nitse.

"Areef zan fita ne, sai na dawo". Ya kai karshen maganar tare da katse kiran ba tare da ya jira amsarsu ba, pistol gun da ya ajiye daren jiya ya ɗauka ya nufi hanyar palon kasa dan ya sauƙa fita zai yi zuwa unguwa. Zazzaƙar muryarta ne ya katse shi tare da sanya shi juyowa babu shiri. "Yaya Saif tsoro nake ji, dan Allah kada ka fita ka barni, ina jin tsoron gidan sosai". Ta yi maganar a nutse, a shagwaɓe, can kasa kasa kuma, sannan ta yi maganar tana sunkuyar da kai katsa dan bata son kallon face nasa bare ma taga action ɗin da zai ɗauka.

Shiru ya ɗan kalleta na ƴan sakanni, maganar Areef ne ta dawo mishi kunnansa, yana son mu fiye da kansa kuma yana son farincikinmu, ba zai taɓa bari ki shiga kunci ba, dan yasan idan kin yi farinciki to tamkar mune muka yi, tuna hakan yasa ya juya ya cigaba da tafiya, binshi da kallo ta yi idanunta sun ciko tab da kwallah, tana bala'in tsoron zaman gidan ita kaɗai, bai juyo ba kuma bai yi mata magana ba har ya sauƙa ya fita daga palon baki ɗaya, juyowa ta yi ta balcony tana kallon shi ya zo wajen motarsa, shiru ya ɗan tsaya bai shiga ba, can kuma sai ya ɗago kansa sama kamar yasan tana kallon shi, da hannu ya yi mata alama a kan ta zo su tafi, da sauri ta miƙe, tsabar murna bata ma san lokacin da hawayen da suka cika mata idanu suka zubo ba, ɗakinsu ta koma ta ɗauko ɗan ƙaramin farin hijabi ta sanya a saman kanta, ta yi kyau over, baiwar Allah ko tea ɗin ma ita bata sha ba, kuma tana jin yunwa sosai kamar ta mutu, amma ba halin ta ce zata tsaya shan tea ɗin, dan ba zai jirata ba.

Ta wutsiyar idanunsa yake kallonta tun da ta fito, sai da ta kariso gabansa, calmly ya ce ta buÉ—e musu gate, da okey ta amsa mishi tare da wucewa ta je ta buÉ—e gate É—in, shi kuma ya shiga motar ya tada ta, waje ya nufa, bayan ta fita ne ya tsaya yana jiranta, sai da ta rufe gate É—in sannan ta zo da sauri ta shiga gidan gaba, sai tashin kamshi take yi.

Da gudu ya ja motar, bayan sun kusa kaiwa babbar gate ne ya ciro face mask ya sanya a face nasa, dan yasan idan sun isa gate ɗin sai ya sauƙe glass ɗin motar, miƙa mata face mask ɗaya ya yi a kan ta saka, dan baya son su tsayar da su tambayarta yaushe ta dawo da sauransu, dan ba wanda bai san ƴaƴan Nawazudden ba a wajen, suma masu tsaron babbar gate ɗin sun santa tun da kullum daddy na kaisu school.

Haka kuwa aka yi, da suka zo sai da aka tsayar da su, suka yi binciken da zasu yi sannan suka fice, suna fita ya kunna goggle map a wayarsa ya ɗauki hanya kawai abinsa, sun yi nisa da tafiyar da suke yi sai ya lura ana bin bayansu, wata bakar mota ce ta fara biyo su tun ɗazun, ɗan juyowa ya yi ya kalleta ta cikin mirror, sarkin tsoro sai kallon hanya take yi, kasa kasa ya ce ta ɗaura seat belt nata, okey ta amsa tare da ɗaura wa, shi ma ɗaurawa ya yi tare da canza hanya daga kan hanyar da yake ya sauƙa izuwa ɗayar hanyar ya kuma kara gudun motar sosai, bata wani damu ba, dan dama bata san ina zasu je ba.

Gudu ya yi ta shararawa har suka fita bayan gari, a É—an wani daji ya paka motar tasa tare da ce mata ta zauna a ciki kada ta fita, dama yasan in dai suka fita sai an bi bayansu, da gangan ya ce ta buÉ—e mishi gate, dan ta fito a waje ne ta shiga motar tasa, yana son kowa ya san ta dawo, idan suka sani kuma sai an biyo bayansu, wannan dalilin yasa ya É—auko pistol gun nasa.

Ta cikin mirror yake kallon wannan bakar motar, É—an nesa da nasu suma suka paka, suma bakar glass ce da motar tasu, baka iya ganin mutanen da suke ciki, baya son fita, dan kada su gudu, yana da tabbacin basu san shi ne a cikin motar ba, Rimsha suka biyo, dan ita ce ya shiga motar a waje, shi tun daga cikin gida ya shiga, ita kuwa sarkin tsoro tuni ta tsorata ganinsu a daji, jikinta har wani karma ya fara yi, ta manta ita Æ´ar soyayya ce, yau ga daji daÉ—in soyayya amma kuma jikinta na kerma.

Tana can tana tunani zazzakar sexy voice nasa ya katse mata tunani da cewa "Cire face mask na fuskarki ki fita ki zagaya wajen bishiyoyin ɗan bayan mun can ina zuwa". Ba musu ta cire ta kuma fita, ya yi mata haka ne, dan yana son mutanen su fito, yana son sanin ko su waye ne, tabbas idan ya fito suka ganshi zasu gudu in basu riƙe makamai ba, idan kuma suka gudu da wuya su sake biyo Rimshar ta wannan hanya, sai dai su canza salo, hakan kuma zai sanya shi ya jima a garin nan, baya son wuce kwana uku bai gama komai ya koma ba, idan ita ta fita, zasu yi tunanin bari su lallaɓa su kasheta su cika aikinsu, dan shi ɗan ta'adda kullum gani yake yi zai yi nasara, baya taɓa hangen zai faɗi, shiyasa basu nadama sai sunga mutuwa ɓaro ɓaro.

Tana fita ta nufi wasu biliyoyi dogaye da suke É—an nesa da motarsu ta É—an bayar motar amma, ma'ana tsakanin motarsu da na waÆ´an da suka biyo su, mutane huÉ—u ne suka biyosu, dukkansu fuskokinsu sanye da mask, ga kuma bakaken suit kamar zasu je church or party, suna ganin fitowarta É—aya daga cikinsu ya ce "Oga wlh ita ce, yanzu saura mu san ita da waye a cikin motar, mahaifiyarta ce ko waye?".
Chapter 93 · 0% Book details