← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 121

Sashe 77

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can wani abin ya faÉ—o mishi cikin tunaninsa a in da ya saki cool murmushi kafin ya haye saman gadon tare da sanya hannu a hankali ya zame pillow dake a tsakanin kafafun shi, sai guntse dariyar mugunta yake yi domin yasan yau za su kwashi Æ´an kallo ba kaÉ—an ba, idan ya yi mishi abin da yake da niyar yin nan.

Yana ƙoƙarin kai pillow saman fuskar ɗan uwan nasa ya toshe mishi numfashi, cak ya riƙe pillow da hannu ɗaya idanunsa a rufe kamar mai barci. Guntun tsaki ya ja kafin ya ce "Dama in the first place dana shigo na yi tunanin baka yi barci ba, oya stand up". Wani kayatatcen murmushi ya saki ba tare da ya buɗe ido ba ya fara magana tamkar mai sambatun magagin barci "Heartbeat i really love you so much, kada ki manta ki rufe kofa kada Areef ɗan gulma ya leƙo, kin san...." Bai barshi ya karisa ba, ya kai mashi duka yana faɗin "Waye kuma ɗan gulma?".

Wani irin miƙewa ya yi ya rungume shi yana faɗin "Kai mana, muna tsaka da soyayya da heartbeat zaka tashe ni ko? To yanzu ba gulmar ka zo yi bane?" Hararar wasa ya watsa mishi tare da sauƙowa daga gadon ya nufi waje, "Ka shirya by 7 zamu kai sister school, zan je naga school ɗin, bari nayi magana da Prof ina zuwa". Okey ya amsa mishi da shi tare da komawa ya kwanta yana murmushi kamar wadda aka cewa ga amaryar ka can ana kawo maka ita.

A ɓangaren Lion kuwa, yau ya zuba kwalliya ta musamman, da alama akwai in da zai je, ya yi wani azababben kyau na wuce misali, kananan kaya ne a jikin nasa kamar kullum, sai dai waƴan nan daga ganinsu kasan sun amsa sunansu kaya ba karya, masu shegen tsada ne, yanzu yana yawan barin sarkarsa a waje samar sigarsa mai mai kon a ta ciki, da alama hakan ta fi yi mishi daɗi, Brady na goye a bayansa, sun fito tsakiyar palo sama kenan Brady ya yi tsalle ya diro kasa yana daka haushi, zuba mishi idanu Lion ɗin ya yi yana kare mishi kallo, cikin harshen turanci ya yi mishi magana a kan su tafi komai na gidan nan kamshin perfume nasa yake yi, saboda ya gane me Brady ɗin yake yi wa haushi, kamshin perfume nasa ya ji yo a ɗakin Rimsha na wancan rigar sanyi, to shi ne yake haushin shi ba zai tafi ba sai ya fito da rigar, tamkar rigar sane ɗan kaniya.

Da kyar ya yarda ya biyo Lion ɗin suka sauƙa kasa, babu kowa a palon kasan sai Mark dake kitchen, jin kamshin perfume ɗin ogan nasa ta karu a palon ne yasa ya gane ogan nasa ya fito, ɗauko kayan abincin da ya gama haɗawa ya yi izuwa palo, a saman dinning table ya shirya su kafin ya juyo izuwa wajen ogan nasa, shiru suka yi dukkansu biyu, dama already kun sani, dukkansu sarakan zama shiru ne, zasu iya shekara su biyun nan ba tare da sun ce da junansu uppan ba, kuma suna tare waje guda, hakan suke kamar wasu kurame, ga Mark kullum cikin bakar glass yana rufe sexy Hazel eyes nasa, dan idanun nasa zaka tara turawa 1000 baka sami biyu masu irin idon ba, idanun yana nan tamkar green eyes ne, sai dai bai kai green eyes shiga color ba, combination ne na green da brown, sune suka bada Hazel, yana da bala'in kyau sosai, ga shi shima akwa mangan idanu ga karfin gani, kullum yana cikin black glass abinsa, sai ka rantse baya kallon komai, saboda sau ɗaya yake kallon abu baya kuma mai da kallonsa sai in an sami kuskure, to shi ogansa ma baya kallon abin, Lion zaku jima tare da shi ba tare da ya ɗago ya ganka ba, daga motsin mugun yake iya zayyana shi a ransa, idan kuna tare yau da gobe, yanayin yadda mutun yake motsi a kusa da shi, ta hakan ya gane Rimsha tana da bala'in rawar kai, bata da natsuwa.

Sun jima tsaye a haka kafin Lion ya yi gaba ba tare da ya ce da Mark É—in uppan ba, rufa mishi baya Mark É—in ya yi, motarsa ya je ya shiga, sai tsalle Brady yake yi, da alama daÉ—i yake ji zasu je yawo, gidan gaba Mark ya shiga tare da yi wa motar key suka bar gidan, tana tsaye a jikin window É—akinta tana kallonsu, tun É—azun ta tashi daga barci dan zata je school, makarantar yana ranta, shiyasa bata yi wani barcin kirki ba ta farka, yau Lion ya yi mata wani masifaffe kuma azababben kyau ba kaÉ—an ba, ta kafe shi da idu har suka bar gidan, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya zuwa toilet.

A gurguje ta yi wanka tare da fitowa ta shirya cikin uniform nata, ba ƙaramin kyau ta yi ba, a palon kasa ta isko Areef yana tsaye yana waya, da alama da daddynsu yake magana, gefensa ta zo ta tsaya tana jiran ya kammala, after some minutes, ya Kammala wayar tare da riƙo hannunta cikin nasa yana faɗin "Kyakkyawar gimbiyar TRIPLETS ya aka yi ne?". "Good morning lovely brother". Ɗan leƙo face nata ya yi, ta yi kyau sosai da sosai, "Shikenan an gama shiri muje ko?" Kai ta gyaɗa mishi alamar e "To yanzu dai zo muje saman table na koya miki cin abincin kasarmu kafin mu tafi ko?". Ba zata iya yi mishi musu ba, kai ta gyaɗa mishi tana faɗin Okey.

Abincin da Mark ya shirya musu ya fara zuba mata ɗaya daga ciki, sai bin shi da ido take yi, "Me yasa ki kuka daren jiya kuma?" Ɗan zaro idanu waje ta yi, tana mamakin waye ya gaya mishi ta yi kuka kuma, "Ki dai'na mamaki idanunki suka nuna mini kin yi kuka, yanzu dai gaya mini dalili, da daddare dai nasan ba wanda zai shiga ɗakin ki har ya yi miki wani abin, to me matsalar?". A maimakon ta gaya mishi halin da take ciki na ɓatar ƴar uwarta, dan ko banza ba zai yarda ba sai ya nemota, amma sai ta ɓoye mishi tare da ce mishi karatun Alqur'ani mai girma ta yi ya sanyata kuka, ya gamsu da maganarta, dan ko shi idan yana karatu, yana tuna girman Allah, da wasu bayi dake bijirewa umarni Allah sai ya yi musu kwallah, sai dai a jikinsa yana jin tamkar tana da damuwa, bai cika son matsa mata a kan abu ba, dan haka sai ya kyaleta tare da tura mata abincin da ya zuba a plate ɗin a gabanta a kan ta ci.

"Yaya Areef ina tare zamu ci?" "Haka kike so?" Gyaɗa mishi kai ta yi, okey ya amsa mata da shi tare da ɗauko spoon ya ɗabo first spoon ya kai mata saitin ɗan bakinta yana faɗin "Buɗe baki ki karɓi first spoon na". Bata kai ga buɗe baki ba Aseef da ya fito yanzu ya yi maza ya zo ya cinye yana murmushi, harararsa ya yi kafin ya sake ɗebo mata wani abincin, zama shi kuma ya yi a ɗayar gefenta ya zamana sun sakata a tsakiya, a shagwaɓe ya ce "Sister saura first spoon naki, ɗebo ki bani naci". Ba musu ta ɗebo mishi, dan tasan halinsa sarai, yanzu ba ƙaramin aikin shi bane ya sanya musu kukan shagwaɓa a nan, bayan ta bashi sai ya ɗauko spoon nasa shi ma, ita ya fara bawa kafin Areef, daga nan suka fara ciki a tare, wasa wasa Rimsha bata san time da cikinta ya cika tap da abincin nasu ba, sun mantar da ita me ma take ci, sai hira suke yi mata gwanin ban sha'awa.

To mu É—an koma baya kaÉ—an, a daren jiya, ba iya Rimsha ce kawai ta yi mafarkin Jehan na cikin wani hali ba, har ta daddynsu, mummynsu, Gwaggo duk sun yi, hakan yasa gabaÉ—ayansu suka kwana a saman dadduma suna kaiwa Allah kukansu, musamman ma daddynsu da yafi kowa shiga tashin hankali, dan shi nashi mafarkin a tsantsar mummunar yanayi Jehan É—in ta zo mishi, ya tsorata sosai, wai gata nan tana kuka an mata fyaÉ—e, tana kwance cikin jini, ga sarka a hannu da kafa an É—aureta ana zaneta da wasu irin dogayen bulalu masu shiga jiki, duk in da aka zana mata sai wajen ya yi jajir ya tara jini, da yake ita fara ce tas, kunsan duk Uba na gari ya ga yarsa cikin wannan hali ko a mafarki ne ma dole hankalinsa ya yi mummunar tashi ba kaÉ—an ba, hakan yasa yau ya tashi da azumi a bakinsa dan ya roka mata Allah da ya tsareta a duk in da take, yasan in makamancin haka ya faru da ita zai iya mutuwa saboda bugawar zuciya, wlh bawan Allah nan har wani Æ´ar rama ya yi, duk ya yi sanyi jikinsa ya mutu, kuka ne kawai bai yi ba.

A ɓangaren mummy da gwaggo ma hakan ne, da azumi a bakinsu suka tashi, duk da su mafarkinta da suka yi bai kai na daddy muni ba, bayin Allah basu kaiwa kowa kukansu sai ubangijin taliƙai, da abu ya damesu zasu ɗauro alwala su kaiwa Allah damuwarsa, shiyasa a kullum suke cin nasara a kan makiya, badan suna addu'a ba ai da an rufe bakinsu, da Rimsha ba zata iya fitowa daga Daular Mutuwa ba, karfin addu'a ya fito da ita, shi ya juyar da hankalin duna har ya taimaka musu suka fita, suka yi breaking na record ɗin Daular Mutuwar, haka shi ma daddy, badan karfin addu'a ba da an jima da kashe shi, su ma su mum ɗin hakan ne, uncle Shitu, dukkansu karfin addu'a ke cetarsu a ko da yaushe, to yanzu ga Jehan ma sun dukufu a kanta, yadda suka dukufan nan kuwa wane uwar Hajiyar daɗi dan ubanta, tsafinta ya yi kaɗan, masu kai kara wajen Ubangiji sun fi yawa, karfin addu'ar bayin Allah ya fi karfinta, Allah dai ya basu Nasara, Amin. Mu cigaba da labari.
Chapter 77 · 0% Book details