Sashe 15
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka suka kasance har karfe 7 na safe, sannan ya ce ta tashi su je wajen Ummi, daga nan sai suje kitchen ya tayata yi masu girki. "Yaya Nawid ka iya girki ne?" Ta tambaya da mamaki akan face nata.
"Prof ya iya girki ne ko bai iya ba?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kamar dai bai iya ba". Kashe mata ido ɗaya ya yi. "Duk wan da ya ce maki Prof bai iya girki ba, to ya gaya maki ne kawai dan ya ji daɗin bakinsa, amma Prof ba abin da bai iya girkawa ba, sai dai kawai baya son yi ne, amma ba dai ya yi aure ba? Zai yi ne ma ba wanda ya sani, nima da ai bana shiga kitchen, ko hanyarta ma ban sani ba, ban san me da me ma a cikin kitchen ɗin ba, amma yau ba gashi saboda ke zai shiga ba". Ya kai karshen maganar tare da sakinta ya miƙe zaune.
Miƙewa ita ma ta yi, ta riga shi sauƙowa kasa, hannunta ya kamata suka nufi wajen, sai hira yake zuba mata, ita kuma sai murmushi take abinta, dama akwai tsohon soyayyarsa a cikin zuciyarta, yau soyayyar ta dawo mata sabuwa.
A palo suka isko Ummi, har ta gama haɗa breakfast, ta jere saman table tana jiransu su tashi barci. Ganinta yasa A'AFIA ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata, cikin sauri ta karisa wajenta, miƙewa Ummin ta yi, ta tarota tare da runhumeta tana sakar mata wani ƙayatatciyar murmushi, sai murmushi shi ma yake yi, bakinsa yaki rufuwa.
A tare suka zauna a saman sofar da ta tashi ta koma ta zauna, har lokacin bata saki surukar tata ba, shi ma wucewa ya yi ya zauna, sai murmushi suke yi, suka gaisa, har lokacin kuma, duk cikinsu ba wanda ya iya tunawa da Abbo, ya rufe masu baki, tamkar an goge masu shi a kwakwarsu.
A tare suka hau saman table dan yin breakfast. Bayan sun kammala ne A'AFIA ta miƙe ta tattare kwaninkan ta gyara komai, sannan ta nufi bedroom ɗin Nawid wadda ya kasance nasu a yanzu, ita da shi kenan, yanzu ta iya wasu aikace aikacen gida kaɗan, ciki har da girki, kuma zamanta da Umaisha da Akila ta ɗan koya.
Ita kuma Ummi suka cigaba da hira da shi.
Tana shiga bedroom ɗin ta fara tattare masu ɗakin dan ta gyara, sai da tattare ko'ina, sannan ta fara ƙoƙarin canza masu zanin gado.
Tana faman cire bed sheet ɗin, bata ji shigowarsa ba, sai kawai taga ya sanya hannu yana tayata, da mamaki take kallonsa, kamar AKil, domin shi ma Akil, cire kayansa yake yi, ya sanya na shan iska, ya gyara masu ɗaki, ya kuma wanke toilet, sannan ya raka Umaisha kitchen, tana aiki yana shafe mata tula tula, da yake yanzu Umaisha ɗin take yin girki, sun dai'na sayen abinci, Rimsha ta koya mata wasu, sannan shi ma ya saya mata littatafan girki kala kala, dan kawai ta rinƙa yi masu girki, to a nan Aafia ma ta ɗan koyi aiki.
"Meyasa kike kallona haka?" Ya tambaya daidai lokacin da ya karisa cire bed sheet É—in, ya É—auka ya nufi wajen zuba kayan datti.
"Babu komai" . Jinjina mata kai ya yi. "To jeki ki yi wanka, bari na shinfiÉ—a mana wani bed É—in, idan kin fito sai na shiga na yi Nima, ko dai nazo muje mu yi a tare ne?" . Ya yi magana ta karshen cikin zolaya.
Da sauri ta nufi toilet É—in tana girgiza mashi kai alamar a'a, dariya ya yi. "Matsoraciya kawai". Ya faÉ—a yana ciro masu wani sabon bed sheet daga cikin drawer kayansa.
Ko sannu ba ta sake ce mashi ba, da haka ta wuce toilet abinta, binta ya yi da kallo har sai da ta shige, sannan ya zo ya fara aikin gyara gadon, a hankali yake jin kaunarta na karuwa mashi a cikin zuciyarsa.
After some minutes ta fito wanka, sai É—ari É—arin fitowa take yi kada ta same shi a É—akin, domin kuwa towel ta É—auro, bata iya ta yi wanka ta sake mayar da kayan dattin da ta cire ba. Ta yi Sa'a kuwa, baya É—akin.
Ganin baya nan yasa ta ji wani irin daɗi ya kulluɓeta, gaban mirror ta wuce, sauri sauri ta fara shafa mayukansa da ta gani a wajen.
Tana tsaka da shafa mai ta ji saukar hannunsa a kugunta, har ga Allah bata ji shigowarsa, kofar nasa bata kara, idan an taɓata, wani irin ɗaukewa na wucin gadi numfashinta ya yi, cak ta tsaya da shafa mai ɗin da take yi.
Kwanto da kansa ya yi a saman kafadarta, tare da sanya hannunsa ɗaya, ya karɓi Lotion na hannunta da take shafawa, zubawa a hannunsa ya yi, a nutse ya murza man a hannayensa, har lokacin kansa na kwance a saman kafaɗarta, a hannunta ya fara shafa mata man, kafin ya ɗan raba jikinsu, ya fara shafa mata a suk gaɓɓan da ake shafa mai, mutuwar tsaye ta yi, ta kasa ko motsawa.
Ya zo daidai wuyarta, yana ƙoƙarin kwance towel na jikinta dan ya shafa mata man, cikin sauri ta kankame towel ɗin, ɗago ido ya yi, ya kalli face nata, cikin sauri ta kawar da kallonta, sake mata towel ɗin ya yi, ya shafa mata man a face nata yana murmushi.
"Am so sorry gimbiyata, na yi aikin da baki saka ni ba ko? To ki yi hakuri na taya ki ne kawai, tun da an hanani shafawa kirjin mai Shikenan, na bar maki, shafa masu ga kayan sawarki nan na karɓo maki daga wajen Ummi". Yana kai karshen maganar ya wuce ya nufi toilet dan shi ma ya yi wanka.
Bin shi da kallo ta yi, har sai da ya zo zai shiga toilet É—in, sannan ya É—an juyo, cikin sauri ta kawar da kallonta, murmushi ya saki kawai, sannan ya shige abinsa, yana juyawa ta dawo da kallonta kansa, har sai da ya shige ta daina ganinsa, sannan ta cigaba da abin da take yi, sai tunanin yadda ya shafa mata Lotion É—in take yi, har cikin ranta ta ji daÉ—in hakan, musamman yadda taga yana zuba irin wannan murmushi haka, abin ya tsaya mata a ranta.
Wucewa ta yi ta É—auki kayan da ya ajiye mata a saman gado, wani irin kunya ta ji lokacin da ta kalla har da breziya da pant ya kawo mata.
Ɗauka ta yi ta fara sakawa da sauri sauri, doguwar rigar Abaya ce, pink color tare da mayafinta. Tana gama shiryawa Ummi ta buga masu kofar ɗakin, cikin sauri ta karisa bakin kofar ta buɗe, miƙa mata wayarta Ummi ta yi. "Ga shi nan tun ɗazun ake ta kiran ki". Cikin girmamawa ta karɓa tare da yin godiya, juyawa Ummi ta yi ta koma nata bedroom ɗin, ita kuma ta dawo cikin ɗakin.
Umaisha ce ta kira a wayar, cike da zumuÉ—i ta bi kiran, tare da zama a gefen gado. Bugu É—aya Umaisha ta É—aga.
"Hello Umaisha!" Ta yi maganar cike da so da kuma kaunar Æ´ar uwar tata, "Aunty Afi ina kwana?" "Lafiya lou Umaisha yasu yaya AKil?" "Suna lafiya, ya Yaya Nawid da kuma Ummi?".
Nisawa ta yi tana mai kara faÉ—aÉ—a murmushinta "Wlh kowa yana nan lafiya Umaisha, amma lafiya kika kirani da sanyin safiya haka? Ya kuma aka yi yaya Akil ya kyaleki kika yi kira da sanyin safiyar nan".
Shiru kaÉ—an Umaisha ta É—an yi kafin ta ce "Wlh Aunty Afi satar hanya na yi na kiraki, yanzu haka yaya Akil yana É—aki yana kwance, nace mashi ina zuwa ne, shi ne nazo kitchen na kiraki, yanzu dai muyi magana da wuri Kinji? Dan kinsan halinsa sarai, yanzu idan ya ji na kira wani da safe haka, faÉ—a zai yi Mani, zai ce na takurawa Æ´an gida suna barcinsu.
"Okey to menene faÉ—i ina jinka?" "Aunty Afi Ommu ne ta kirani jiya, ta ce na É—auko mata kuÉ—in yaya Akil har naira million goma, to dama yau da daddare ya ce zamu je gida, kuma nace mata idan zamu zo gida zan kawo mata, dama zan É—auka mata 2 million ne a cikin kuÉ—insa da yake ajiyewa a bedroom nasa, to amma tsoro nake ji, na rasa ya zanyi, na rasa me mafita, na rasa wajen waye zan nemi shawara, dan Allah ki ceceni, wlh ina tsoron É—aukar abin da ba nawa ba!!". Ta kai karshen maganar tana hawaye.
A kule Aafia ta ce "Sai dai uban millon 10, ke Umaisha baki da hankali ko? Ta yaya zaki yarda da wannan abin? Kina da hankali kuwa? Ina ilimin naki yake? Ina karatun da kike yi kullun? Haka Allah ya ce ki yi? Allah bai ce ayi wa iyaye biyayya wajen saɓon sa ba, Ki sani naira ɗaya na mijinki, idan kika ci ba tare da ya baki ba, to fa wuta kika ci, to tun wuri ki dawo hayyacinki Kinji na gaya maki, me yasa ba zata tambayi Abbi ba? Idan ma Abbi yaki bata ai yaya Irfan kam ya zama mashi dole ya bata, to wlh kada ki kuskura ko naira ɗaya na yaya Akil ki taɓa ba tare da ya baki ba?".
Tana hawaye ta fara bawa A'AFIA É—in labarin yadda suka yi da Ommu É—in da har ta yarda zata É—auko mata kuÉ—in, jin hakan yasa jikin Aafia É—in ya mutuwa, Allah sarki uwa da Æ´aÆ´a kenan, komai lalacewar uwa, in dai tasan ta yadda zata yi magana da yaranta, to tabbas ba makawa zata yi galaba akansu, ta rasa me zata cewa Umaisha É—in kuma again.
"Aunty Afi kina jina?" Ƴar firgita ta yi jin muryar Umaisha ɗin, Baiwar Allah ta shiga duniyar tunani ne, domin ta gasgata zancen Ommu ɗin, musaman ma da ta ji an ce Abbi ya ce ba zai biya mata ba, ta san halinsa sarai, tabbas zai iya cewa ba zai biya ɗin ba, domin yana da zafin rai da saurin fushi, sai dai kuma yana da saurin sauƙowa, abin da bata sani ba shi ne, Ommu karya ta shirya masu da ciwo, domin tasan da ciwo ne kawai zata yi saurin karyar masu da zuciya.