← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 121

Sashe 118

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren Dr ma, da kyar ya iya yin sallah dan ɓacin rai, shi da tun farko ta gaya mishi ita ba budurwa bace ai da ya fi mishi, matsalar kuma da aka samu shi babban likita ne, duk wasu matsaloli na mata ya sani, dole zai gane ita ba budurwa ba ce, idan kuma da kansa ya gane dama dole a sami irin wannan matsala, farkon abin da zai fara tunani ma to da waye ta kwanta? Wani irin mutun ne? Yana ɗauke da wani ciwo or not? Ita ɗin lafiya take or not? Koma dai akwai karamin ciki a jikinta? Tambayoyi dai kala kala zai yi ta yi wa kansa wanda kuma daga haka babu samun yarda kenan a tsakaninsu, dan zai yi ta tunanin ai bin maza take yi, ya Allah ka tsare mana imaninmu mutincinmu da martabanmu, masu yi wa yaran mutane fyaɗe ku dubi girman Allah ku daina, ku daina lalata ƴaƴan mutane, kuna cutar rayuwarsu, kuna ruguza musu duk wani farinciki, kuna rusa musu jin daɗi kamar sauran mata, kusa su fiskancin tsangwama wajen mijinsu da sauran ƴan uwa, ku ji tsoron Allah ku dai'na, akwai kiyama, akwai lahira ranar da zaku biya duk abin da kuka ci, akwai mutuwa, sannan ko baku mutuba akwai tsufa, bugu da kari kuma zaku haifi ƴaƴan nan ko ba jima ko ba daɗe, kuma maza kuji tsoron Allah ku rinƙa jin kan ƴaƴan da aka zalunta aka yi wa fyaɗe idan kun auresu, ku sani ba laifinsu bane, ku tausaya musu Allah zai biya ku, Allah ka bamu dacewa.

Sai misalin karfe 9 ya shigo gida abin da bai taɓa yi ba, a ko da yaushe idan ya je masallaci burinsa kawai ya yi sallah ya dawo wajen matarsa da mahaifiyarsa, sai ga shi yau kuma ko da ya yi sallah ya yi zamansa a masallaci har karfe tara sannan ya dawo, ta shiga damuwa sosai na ganin bai dawo ba, har kamar zata kira shi a waya, sai kuma ta fasa ta danne ta cigaba da kwanciya kawai tana jiransa.

A palo ya isko Ummi tana ƙoƙarin shiga bedroom nata dan lokacin barcinta ya yi, da mamaki take kallonsa na fitowa daga waje da ya yi, sannu tare da barka da dare ya yi mata kafin ya nufi bedroom nasu, da mamaki ta bishi da kallo. "Nawid lafiya kuwa? Ya A'afia bata fito ba yau, na yi tunanin bari naje na dubata sai kuma na tuna kila kana ciki ne, amma ya ka fito daga waje kuma? Ga dukkan alamu kuma kana cikin damuwa, lafiya me yake faruwa? Ko dai A'afia ɗin ce bata da lafiya?". A rikice take jera mishi tambayoyin nata.

Ƙaƙalo murmushi dole ya yi yana faɗin "Ummi ki kwantar da hankalinki babu komai, A'afia ce take ɗan jin zazzaɓi kuma nayi mata allura tana barci, dan haka babu komai, ki je ki yi barci". Murmushi ita ma ta yi a cikin zuciyarta tana faɗin Allah yasa cikine da surukuwar tata, kullum tana yi musu addu'ar Allah ya basu ciki mai albarka, Nawid shi kaɗai Allah ya bata, tana yi mishi addu'a shi kuma ya haifo mata ko dozen ne haka, zata riƙe su baki ɗaya, sai hamdala take ga Allah ta wuce bedroom nata bayan ta yi wa Aafia ɗin addu'ar samun sauki cikin gaggawa.

Shi ma wucewa ya yi nasu bedroom ɗin yana amsawa da Amin ya Allah, kwance ya iskota saman bed, sam bai bi ta kanta ba ya wuce saman sofa ya zauna tare da jawo takardunsa da laptop nasa ya fara aiki, cike da tsoro ta ce mishi ta zuba mishi abinci, ko kallon in da take bai yi ba bare ta sa ran zai amsa mata, cigaba da abin da yake yi kawai ya yi har zuwa karfe 11, bata yi barci ba, shi kuma bai ci abincin ba, ita ma bata ci ba saboda tare suka saba ci, sai 11:30 ya tattare komai ya wuce toilet, wanka ya yi tare da shirin kwanciya ya zo saman bed ɗin ya ɗauki pillow da bargo ya koma saman sofa ya yi kwanciyarsa, yana jin yunwa sosai haka ya kwanta, ita ma tana jin yunwa sosai haka ta kwanta, sai misalin karfe 2 na dare ta samu barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, shi kuma sai karfe 4 ya iya yin barci, nan ma da kyar, sai tunani yake yi a kan waye A'afia ta baiwa mutuncinta, kishi ya hana shi barci, abin ya tsaya mishi a ransa sosai, rashin sani ya fi dare duhu.

A ɓangaren gidan Lion kuwa, yau gabaɗaya Network sai rawa yake yi, shi kuma Lion yana son ya yi magana da Tyrone dan ya ɗauko mishi daddyn Rimsha su taho tare, jikin TGA har yanzu akwai sauran ciwo jikinsa da tafiya zai yi mishi wahala, shi kuma Lion yana bukatar daddyn Rimsha da wuri dan yana tantanma a kan wanda ya kama, ƴan biyu ne masu kama ɗaya, daddyn Rimsha ne kawai zai iya rabe wanene daga cikinsu abokin faɗan nasa, bayan haka akwai wasu abubuwa da yake son tasa daddyn Rimsha a gaba ya yi mishi bayani a kai, magana ce da ta shafi Na'urat mahaifiyarsu, yana son kammala case ɗin da wuri ya koma kasarsu dan ya ɗauki lokaci a nan, hakan kuma sam bai yi mishi ba, so yana son kashe komai ya shafe rikicin dan daddyn Rimsha ya dawo cikin family'nsa su yi zaman farinciki.

Bayan ya yi sallar mangariba da issha ya dawo, ya yi ƙoƙarin samun Tyrone a waya amma abin ya ci tura, rai a matukar ɓace ya nufi wajen gate baki ɗaya dan ya nemi wajen da akwai Network, dan shi dai dole sai ya yi wannan call ɗin tana da mahimmanci, baya son daddyn Rimsha ya wuce kwana biyu bai shigo Naija ba.

Haushi Brady ya fara yi mishi a kan lallai sai ya bishi, É—aure fuska sosai ya yi tare da cewa Mark ya kwance mishi karen sa, waye zai wani É—aure mishi sweetheart É—insa dan iskanci, bai san cewa Areef yasa Aseef ya É—aure shi ba dan kada ya takurawa Rimsha, shi ne suka É—aure shi.

Kwance shi Mark ya yi, da gudu ya taho ya rungume Lion É—in yana wani kuka kasa kasa, shafa jikinsa ya fara yi alamar rarrashi tun da an yi mishi ba dai'dai ba, an kama an wani É—aure shi an hana shi jin daÉ—in duniyarsa, ya sha alwashin Allah duk wanda ya sake É—aure mishi sweetheart É—insa dai ya hukunta shi, ko da kuwa Aseef ne, akan me su suna jin daÉ—in rayuwarsu suna sake wa shi kuma zasu takura mishi? To wlh ba zai yiwu ba, dole ya taka musu birki.

Lion da Brady mutuka raba, akwai kauna da amana ba kaɗan ba, wanda yake son mutuwa cikin sauki to ya yi ƙoƙarin cutar da wannan sweetheart Bradyn ya ga ikon god, cikin sauki kuma cikin sauri zai wuce lahira.

Waje ya nufa da shi yana cigaba da shafa jikinsa, lafewa ya yi a jikin Lion É—in alamar ya hakura kenan, kai Brady duniya, ya samu horo iya horo, wani lokaci idan yana abu kamar mutun.

Sun ɗan yi tafiya mai nisa tsakaninsu da gidan nasu kafin ya tsaya kusa da wani restaurant yana duba Network ko ya zo, Brady na manne a kirjinsa kamar wani yaronsa, ya kuwa yi Sa'a wajen akwai Network, number Tyrone ya kira, bugu ɗaya ya ɗaga, ba tare da ɓata lokaci ba ya sanar da shi on Monday ya taho mishi da daddyn Rimsha Nigeria, okey ya amsa cikin girmamawa, yana katse kiran nasa Brady ya diro kasa daga jikinsa ya nufi wasu guys dake tsaye su biyu ta gefensu ta ɗan baya kaɗan, da yake Lion ya rungume shi a kirjinsa ne shi yana iya kallon abin da yake bayan Lion ɗin, shi kuma Lion yana kallon gaba ne, shiyasa ya kallin guys ɗin.

Da farko zai kira Brady É—in, sai kuma ya fasa dan ya san horon da ya bawa karen nasa, na farko baya kwaÉ—ayi, na biyu baya bin mutane a hanya, shi baya yarda ma da kowa kamar ogan nasa, sannan baya yin abu babu dalili, ko Rimsha da yake takurawa ita ce take gudunsa, take yin abu kamar mara gaskiya, to a irin hoton da ya samu kuma idan ya kalli mara gaskiya dole zai bishi, shiyasa idan ta gudu yake binta.

Zuba mishi ido Lion ɗin ya yi yana kallon ikon Allah bayan ya ɗan juyo garesu kenan, yana zuwa ya yi tsalle ya sanya bakinsa ya kwace wayar dake hannun guy ɗin, yana kwacewa ya nufo Lion da gudu ya kawo mishi wayar tare da hayewa jikinsa, karɓa ya yi tare da juyo screen ɗin wayar dan ya gani menene Bradyn ɗin ya gani, yasan dai haka kawai ba zai kawo mishi wayar mutane ba.

Hoton Rimsha ne tana tsaye sanye da wani wandon jeans baki mai bala'in kyau sai ƴar t-shirt fara tas mai ratsin baki a jiki, ta saki dark black curly hair nan nata har gadon baya, ta yi kyau over kamar ka saceta ku gudu, ka je ka ajiyeta kayi ta kallo, ga shi ta ɗan ɗaga idanunta sama, sleeping eyes ɗin sun fito sosai a hoton, ta ɗan motsa laɓɓanta kaɗan dimple nata ya bayyana, da alama hoton bata jima da yin shi ba suka rabu da iyayenta, dan a gidansu na Abuja ta yi hoton tsaye wajen pool nasu.

Zubawa hoton idanu ya yi sai haushi a hankali hankali Brady yake yi mishi, Abin da ya faru shi ne, guys É—in suna tsaye ta bayansu shi kuma Brady yana kallonsu, ya kalli lokacin da suka buÉ—e hoton, shi kuma kare baya mantuwa, musamman ma irin Brady da ya samu horo, so ya san Rimsha sosai, ya san a gidansu take, dole idan ya ga hotonta zai ganeta, dan su karnika akwai rike mutun, in dai sun san mutu wlh ko shekara zasu yi basu gan shi ba, to duk ranar da suka haÉ—u sai sun gane shi, haka zasu yi ta hawa jikinsa suna nuna murnar ganinsa da suka yi.
Chapter 118 · 0% Book details