← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 121

Sashe 17

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani cool murmushi ta saki, an sosa mata in da yake yi mata kaikayi, sosai Malika ta ji daÉ—in ganin wannan murmushi nata, dama kuma abain da take nema kenan. "Malika dan Allah ina son in tambaye ki". Tsareta da idanu Malika ta yi ba tare da ta yi magana ba.

"Malika dan Allah ko kin san ta ya ya aka yi Ayla ta baro Daular Mutuwa? Abin ya tsaya mani a raina, dana tambayeta a waya kuma, ta ce mini ta manta, to dan Allah idan kin sani ki gaya mini".

Shiru ta É—an yi na tsawon lokaci kafin ta fara magana a nutse "E Ayla ta baro Daular Mutuwa ne da taimakon wani daga cikin Daular Mutuwar, sun sha faÉ—a sosai kafin ya samu ya fito da ita, bayan ya fito da ita kuma, akwai wani ruwan tsafi da ya bata, ni ban san faÉ—ar da suka yi a ciki ba, na dai ga lokacin da ya fito da ita, ya bata ruwan tsafin domin ta sha, tana sha kuma ta zube a wajen sumammiya, bata sake farkawa sai bayan kwana É—aya, a in da kuma ta farka a kusa da wannan kauye da kuka haÉ—u, shi kuma wadda ya bata ruwan tsafi ya kuma fito da ita, yana ganin ta suma ya juya ya koma cikin Daular Mutuwa, to kin ji abin da ya faru kenan, abin da yasa kuma ki ka ji cikin Ayla na kumbura a lokacin, wannan ruwa da ya bata ta sha ne, shi ne yasa hakan ta faru kafin ya saketa".

Rimsha zata sake magana sai ga Mark ya fito daga cikin Kitchen, karo na farko yau da ya sauƙe idanuwansa a kanta, baya iya ganin Malika, ita kaɗai ce a wajen a idanunsa, ba karamin mamaki ya sha ba ganin irin kyanta, sosai ya kare mata kallo daga sama har kasa, ga idanun nasa dara dara, sai dai suna cikin bakin glass, hakan yasa bata gane yana kallonta ba.

"What is your name?" Shi ne abin da ya tambayeta da wata fasasshiyar muryarsa a wajen, mamaki ne ya kamata, dama wannan mai fuskar ɓaunan yana magana? Ai ita ta zaci ma kurma ne wlh.

RIMSHA ta bashi amsar, kokarin kiran sunan ya yi a cikin zuciyarsa, amma ya kasa, a maimakon Rimsha, sai ya ce Rishma, ganin sunan ba zata maimaitun mashi bane yasa ya ce ya ta je ta É—auki abincin oga ya gama haÉ—awa.

Okey ta amsa mashi da shi, ta miƙe cikin natsuwa, yau dai bai tafi ba, ya tsaya binta da kallo, ƴar karama da ita sai shegen kyau kamar ita ta yi kanta, Malika dai ta zuba idanu tana ganin ikon Allah, tare kuma da dariyar mugunta, kome take yi wa dariya oho, ita kaɗai ta barwa kanta sani.

Yana tsaye a wajen har ta fito É—auke da abincin, zata yi wa Malika magana, cikin sauri ta É—aga mata hannu alamar ta je kawai, idan ta yi magana Mark zai ce ta haukace, tun da shi baya kallon Malika É—in.

Sama ta wuce, shi kuma ya wuce ya koma cikin Kitchen É—in, dan ya É—auko abincin Areef, yau kawai ya ji yana son tayata aiki ne, shiyasa zai kaiwa Areef nasa abinci. TO FA YANA SON TAYATA AIKI KUMA? SHI DA BAYA KO MAGANA? HMMMM.

A bakin kofarsa ta tsaya kamar kullum, kasa kasa ta yi sallama a nutse, kamar dai kullun shiru, a hankali ta zuro kafafunta cikin daɗin. Daddaɗar kamshin perfume nasa ne ya fara kai mata karo a kofofin hancinta. Shaƙa ta yi ta lumshe idanu, har wani nishaɗi take ji.

Babu kowa a cikin daɗin, yau dai taƙi ɗago idanu gudun kada ta ga wani abin mai razanarwa, har sai da ta ajiye mashi abincin nasa a in da ta sa ba ajiye mashi, sannan ta fara ƴan waige waigen ko zata ga ta ina yake.

Ganin babu kowa ne yasa ta yi zamanta a wajen tana cigaba da kallon É—akin, sai dai ta É—an yi kasa da kanta.

Jin kamshin perfume É—in nasa ya karu a É—akin ne yasa ta É—ago kanta, ya fito daga dressing room nasa, ya bata baya yana kallon fusataccen fuskarsa a jikin mirror, da alama akwai abin da yake yi, jikinsa na sanye da jallabiya fara tas, kai.... shi dai yana bala'in son farin color a rayuwarsa.

Sai satar kallonsa ta kasan ido take yi, duk da bata ga face nashi ba, bata ganshi ta gaba ba, tabbas tasan ya yi wa kayan kyau over, da alama ya rage tsawon gashin kansa, domin yau da ya É—auke ta, jelar bata da tsawo sosai, ba kamar ko da yaushe ba.

Sai bayan ya gama abin da yake yi ne, ya dawo kusa da ita a in da ya saba zama ya zauna, cikin sauri ta fara zuba mashi abincin, can cikin ƙwaƙwalwarta zazzakar sexy voice nasa ya daki dodin kunnenta har cikin ƙwaƙwalwarta.

"Give me my photo". Shi ne abin da ya faÉ—a mata, yau ta tattara natsuwarta sosai, bata son ta cigaba da yi mashi laifi, a bayanan da Imran ya yi mata ta fahimci cewa yes tabbas yana yi wa Imran kara sosai da har take yi mashi irin waÉ—an nan laifuka ya kyaketa, kuma tana cin albarkacin har da daddynta da yake matukar taimakon ASEEF.

Cikin natsuwa ta amsa mashi da okey, sannan ta miƙe ta ɗauko mashi wayar, sai dai jikinta sai kerma yake yi, lokacin da ta zo miƙa mashi wayar hannunta sai kerma yake yi, kallo ɗaya ya yi wa hannun nata ya karɓi wayarsa ya fara aikin latsawa, tun da ya fahimci tana mutsuwar bala'i tsoronsa, sai ya ji a ransa bai kamata ya yi mata magana da karfi ba, zata iya mutuwa idan hakan ta faru, dama kuma magana da karfi ba halinsa bane.

Abincin ta zuba ta tura mashi, sai daÉ—i take ji, yau bata yi mashi laifi ba, ita kaÉ—ai sai murmushi take yi, Allah ma yasa baya ganinta, da sai ya ce ta haukace.

Da yake yau ya ji yunwa sosai, bai wani tsaya ɓata lokaci ba, tana tura mashi abincin ya fara ɗeba yana kaiwa ɗan bakinsa a nutse, ita kuwa zama ta yi a gefensa tana tunanin da ace yanzu kawai ya fara bata abincin nan a baki mana, ai da ta ji daɗi.

(Kai Rimsha duniya)

Shi kuwa tamkar ma bai san da mutun a cikin ɗakin ba, laptop nasa dake a ɗaure saman gado ne sauti dariyar Aseef ya fara fitowa dafa ciki, ba tare da ya ɗago kai ba ya ce ta miƙo mashi laptop ɗin, okey ta amsa mashi da shi, a nutsu ta miƙe ta ɗauko mashi.

Saman sofa ta gefensa ya É—aura laptop É—in, ita ma tana iya kallon screen É—in, saboda tana gefensa É—an nesa da shi, kusan a jere suke za'a ce.

Zuba ma laptop ɗin ido ta yi, shi kuma yana cin abinci yana sauraron shirmen Aseef da Musharraf, wai Aseef na koyar Hausa, shi ne suke ta dariya, idan Musharraf ya faɗi wani word Aseef ya kwashe da darita kamar zautatce, wai kalmar ta bashi dariya, idan kuma Musharraf ya ce ya maimaita kalmar, to fa idan ya faɗeta sai Musharraf ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya, domin kuwa harshen Aseef a naɗe take, ba yarensa bane, so baya taɓa faɗa daidai, komai sai ya canza mata muhalli.

Rimsha kuwa, daddynta kawai take kallo, yadda yake ta dariya abinsa, suna zaune a wajen basket ball na gidan nasu, Aseef na sanye da wando three quarter, sai farar singlet, shi kuma Daddy, yana sanye ne da full dressing ba ƙanana kamar Aseef ba, sun yi kyau ba kaɗan ba, daddy fa ya kara haske sosai, ainahin hasken fatarsa ta kara bayyana, saboda yanayin kasarsu, akwai sanyi sosai.

A ɓangaren Lion kuwa, har cikin ransa yake jin matukar daɗin abin da suke yi, ko ba komai cikin kaso 100 na damuwar da Aseef yake shiga na ciwon nan nasa, daddy na rage mashi kaso 80 daga ciki, a zahirin gaskiya Aseef yana jin matukar raɗaɗi idan har ya tuna cewa ƴan uwansa dukka sun gama karatu, shi babu abin da ya sani, wani lokaci har hawaye yake yi, sai dai daddyn Rimsha yana ƙoƙari wajen nuna mashi ya yarda da kaddararsa, kowa da yadda kaddara take zuwa mashi, hakan kuma yasa daddyn yake zama ya ɓata lokacinsa da komai da komai, ya zage dantse yana koyawa mashi abubuwa, harta assignment idan a ka basu, daddy na kula da shi, domin daddy degree ne ke fareshi shi, so sai ya zama tamkar uncle nashi mai yi mashi lesson, hakan kuma ba ƙaramin daɗi da farinciki ya sanya Areef da Saif ba, abin da yasa ma kenan Lion bai hukunta Rimsha ɗazun ba, ya daure ya yafe mata sabida Imran da kuma babanta.

Tana ta kallon Daddynta har ya kammala cin abinci bata sani ba, zazzakar sexy voice nasa ta ji yana faɗin ta bashi ruwa, ta shagala da kallonsu ta mance kula da shi, a hanzarce ta zuba mashi ruwan ta miƙa mashi, karɓa ya zo yi hannunsu ya gogi na juna, ai bata san time da ta saki ruwan ba, Allah dai yasa shi ya riƙe cup ɗin, badan haka ba, da ta yi mashi wanka da ruwan. Bai bi ta kanta ba, ya kai cup ɗin saitin ɗan bakinsa.

Sai da ya sha rabin ruwan, sannan ya ajiye, bata gaji da ganin daddynta ba, amma haka ba dan ta so ba, ta tattare kayan ta nufi waje, miƙewa ya yi ya koma saman sofa set mai zaman mutun 2 yana mai matukar jin ƙoshi, ga shi yana cikin farinciki dariyar da Daddy yake sanya Aseef, tamkar Tv haka ya mai dasu yake kallon shirmen nasu, sai dai fa duk da wannan daɗi, fuskarsa a turnuƙe kamar kullum.

Ita kuma kitchen ta mayar da kayan abincin kafin ta fito ta wuce wajen Areef dan su ɗan yi hira, daidai zata shiga ɗakin nasa, Malika ta jata baya tana faɗin kada ta shiga, da mamaki ta tambayi dalili, hannunta Malika ta riƙe suka koma saman sofa suka zauna dan su tattauna.
Chapter 17 · 0% Book details