← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 121

Sashe 28

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da tazo sun kasa motsawa ko nan da chan, sun baje a saman gado har sai da aka yi sallar azahar, a sannan ne suka yi wanka tare da sallah, yau Rimsha baki ya ki rufuwa, kuma ga shi yau gidan nasu a cike tab da bakin sojoji, idan ba ka kai zuciya nesa ba, to ba zaka iya zama a cikin waƴan nan jibga jibgan ba, wlh kallonsu ma kawai ya isa ya rinƙa razanaka har rai ya yi halinsa, gasu kamar wasu gumaka, basu magana ko kaɗan.

Shiryawa suka yi dukkansu cikin riga da wando, da yake Akila ta fi Rimsha cika sai kayan sam basu dace ta fita da su a haka ba, gara Rimsha, duk da ita É—in ma bai dace ba cikin zaratan mazan nan ba, musamman yanzu da aka karo wasu, ita zuciya bata da kashi, da Allah yasa mazan ma dukka turawa ne, irin wannan shiga ba bako bane a wajensu, shi ne ma dama shigar matan kasarau, to amma ai yanayin jiki da halittar diri daban daban.

Palo suka fito, babu kowa a palon sama, dan haka sai suka nufi kasa, dukkansu suna sanye da ƙaramin hijabi please call me, sai murna suke yi, baki ma ba zai iya faɗen farincikin da bayin Allahn nan suke a ciki ba.

A palon kasa suka zauna suna hira, Mark na kitchen yana ta faman aikinsa, sai kallonsa Akila take yi, taga farin Bature tas babu mix.

A ɓangaren Gidan Abbo kuwa........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E11-12

A ɓangaren Gidan Abbo kuwa.

Bayan kwana biyu. A cikin wannan kwana biyun sun yi muguwar sabo a tsakaninsu, Aafia ta saki jiki sosai da shi, ya mantar da ita abin da yake damunta a ranta, har wa yau kuma Abbo dai shiru, ba shi ba labarinsa, kuma su dukka ba wanda ya sake tunawa da zancensa, abin kamar almara, ya rufe masu babinsa a bakunansu da kuma zuƙatansu.

Soyayya mai tsabta suke gudanarwa a tsakaninsu, sai dai fa tun daga wannan sumbata É—aya da ta yi Mashi, ba wani abin da ya sake haÉ—a su, sai dai ya zauna ya yi ta zuba mata hira yana sanyata nishaÉ—i, Ummi na matikar kula da Aafia tamkar ita ta haifeta, ko ban faÉ—a ba kunsani, ta fi Hjy Hadiza sau dubu, dan ita dai Hjy Hadiza bata kula da Æ´aÆ´an ba, kenan abin da nake nufi a nan shi ne, Ummi tana kula da Aafia fiye da uwar da ta haifeta.

Ba laifi Aafia na ƙoƙarin shiga kitchen ta taya Ummi aiki, suna yi suna hira, wani lokaci Nawid yana shigowa ya taya su, Ummi ta yi ta tsokanar shi wai yanzu kam ya san hanyar kitchen kenan, da sai dai ya zauna yana isar mutane da Ummi kaza zaki dafa mana yau, yanzu kuma har da shiga kitchen dan ya yi mata, kamar wani jikarta haka Ummi ke tsokanar shi, sai dai ya yi ta Murmushi dan bai san me zai gayawa Ummi ɗin ba.

Rayuwarsu abin burgewa da ban sha'awa, sun mai da Ummi kakansu, idan suna wani wasan ba zaka so su dai'na ba, saboda burgewa da ban sha'awa.

Kwance take a saman gado da misalin karfe huÉ—u na yamma, Nawid baya nan, ita kaÉ—ai ce, Ummi na É—akinta, gabaÉ—aya ko'ina a gyare tsab, sai kamshi yake tashi.

Sanye take da doguwar riga mai shegiyar kyau, launin pink color, duk kuma kayan jelly ce, Ummi ta ce sai sun huta, su shirya zuwa sayan mata kayan lefenta, shiyasa take amfani da na jelly tun da suna yi mata daidai.

Tayi simple make up a face nata, sai tashi wani irin fitinannen kamshi take yi, ta É—aga kai sama da alama wani abin take tunani, karar ringing É—in wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faÉ—a.

A nutse ta miƙa hannu saman bedside drawer ta ɗauko wayar. Umaisha itace mai kirar tata, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ɗauki kiran. "Hello Umaisha". Ta faɗa tana miƙewa zaune a tsakiyar gadon.

"Aunty Afi ina ta jiranki tun shekaran jiya baki kirani ba, Allah ma yasa bamu samu damar zuwa gida ba, amma kuma naji yaya Akil ya ce yau zamu je, shi ne na kiraki in ji hukuncin da kika yanke, in É—aukawa Ommu kuÉ—in ne ko yaya? Wlh ina jin tsoro sosai". Tana magana tamkar zata yi kuka.

"Umaisha shi ne ko sallama babu bare gaisuwa? Ki natsu mana". Kamar zata saka ihu ta ce "Kiyi hakuri Aunty Afi, ina cikin matsananciyar damuwa ce, shiyasa ma na manta da wata gaisuwa, to ina wuni yasu yaya Nawid?".

"Lafiya lou ya yaya AKil?" "Yana nan lafiya". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kina ji Umaisha? Magana ta gaskiya dama ina son in kiraki, kasan cewar kwana biyun nan Yaya Nawid yana nan bai fita bane yasa ban kiraki ba, dama ina Allah Allah kada ki ɗauki kuɗin, to Alhadulillah da Allah yasa ma baku je gidan ba, yanzu dai abin da nake so da ke shi ne, idan kunje gida ki gayawa Ommu yaya Akil bashi da kuɗi, bai ajiye a gida ba, amma duk ranar da ya kawo kuɗin gida, zaki ɗebo mata ko nawa take so, kinga idan kika gaya mata haka ba zata ce kinki ɗauko mata bane, ba zata ɓata rai ko ta yi fushi dake ba, kinga bata isa ta ce a ciro mata a account nashi ba, dole ta hakura ta jira sai ranar da ya kawo kuɗin gida, kafin lokacin kuma zamu nemo wata shawara, amma ba Ommu ba kome zai faru kada ki kuskura ki saci kuɗin mijinki, kai bana mijinki kawai ba, na kowa da kowa ma, kada ki yarda ki ɗauki abin da ba naki ba, duk wanda ya roƙe ki abu, idan ya fi karfin aljihunki, sai ki bashi hakuri babu wani zancen ɓoye ɓoye, kuma duk wani abu idan ya taso kada ki kuskura ki yi gaban kanki, ki gaya mani ko ki gayawa yaya Irfan, idan ba zaki iya gayawa Abbi da yaya Akil ba, kina ji na ko?".

Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali. "Aunty Afi na ji daɗi sosai, kuma ina godiya ga Allah daya bani ƴan uwa masu ƙaunata, nagode da shawararki a gareni, zanyi amfani da ita In Sha Allah".

"To shikenan mummyn Abbi in ji yaya Akil na ba, zan ji daÉ—i fa sosai idan yaya Akil ya cika alkawarinsa ya yi wa Abbi takwara". Dariya sosai Umaisha ta yi, tana matikar kaunar cikin nan nata, ko in ce suna matikar kaunar kayansu ita da mijin nata.

Da sallama É—auke a bakinsa ya shigo cikin É—akin, ganin shi yasa ta ce da Umaisha za su yi waya anjima, da haka suka yi sallama.

Ɗaura wayar saman bedside drawer ta yi tare da miƙewa da sauri ta nufe shi tana murmushi, sai wani lumshe idanu yake yi alamar a gajiye ya dawo, sanye yake da kayan aikinsa, daga ta ciki kuma suit baki ne kafin ya ɗaura rigar tasu ta likitocin, hannunsa na riƙe da bakar jaka mai shegen kyau, while kafarsa na sanye da cover baƙa, daga ciki kuma bakar safa ce a ciki, ya fito a cikakken likitansa.

Karisawa wajensa ta yi tana kara faɗaɗa murmushinta, shi ma murmushi yake sakar mata tare da buɗe mata hannu akan ta yi mashi oyoyo, kin yi mashi tayi, tana zuwa ta karɓi jakar hannunsa, zata juya ya yi maza ya riƙota.

"Ina zaki je ba tare da kin yi mani oyoyo da kuma sumbata na welcome back ba?". Kasa ta yi da kanta bata ce mashi komai ba.

"Haba matata, na fa gaji sosai, kuma nasha wahala, amma shi ne zaki zo ki karɓi jaka kawai, ba wani ɗan sumbata? Baki san cewa idan kika sumbace ni zan ji gajiyar ta gudu mani ba? please mana". Ya kai karshen maganar a ɗan shagwaɓe.

Bata san lokacin da ta juyo ta rungume shi ba, ya iya magana sosai, ta haka kuma yake bi da ita, har ya sanya ta ta yi abinda bata yi niya ba, ta haka yake kore mata duk wata damuwarta, ya mantar da ita komai.

Sosai ya sanya hannu biyu ya riƙota da kyau, tare da kara matseta a jikinsa yana mai jin tsantsar farinciki yau ta rungume shi.

Sun ɗan jima kaɗan a haka, kafin nan ya sanya hannu ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, idanunta a lumshe.

"Kinyi kyau over my mata". Ya faÉ—a kasa kasa. Duk da idanunta a rufe, sai da ta saki haÉ—aÉ—É—en Murmushi, da yawan mata suna son ace sun yi kyau, shi kuma ya kware wajen iya yabon mace, shiyasa ma ta yi saurin kware mashi haka.

"Saura sumbata, ko dai yau za'a bani har da kiss ne?". Ya yi maganar cikin sigar zolaya.

"Ni fa yaya Nawid ban iya ba". Ita ma cikin sigar zolaya ta yi maganar. "In koya maki ne? Kin bani dama?". Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e.

Wani irin daɗi ya ji sosai tare da sakin haɓar tata ya saketa yana faɗin "Bari na yi wanka to, ko dai zaki tayani yi ne?". Da sauri ta juya ta bar wajen tana faɗin "A'a zan dai fitar maka da kayan sakawa, daga nan kuma na ɗauko maka abincinka". Murmushi ya yi tare da karisawa ciki ya fara rage kayan jikinsa.

Ita kuma bayan ta ajiye jakar a mazauninsa, sai ta wuce ta fice daga É—akin ta nufi Palo, binta da kallo ya yi yana mai jin kaunarta na ninkuwa a ransa.

Abinci ta ɗauko mashi, da yake yanzu a ɗaki take kawo mashi abinci su ci a tare, Ummi ce ta ce su rinka ci a ɗaki, dan ta lura da shi Nawid yana son suna cin abinci suna wasa da dariya tsakaninsu na masoya, ita kuma Aafia tana jin kunyar yin hakan a gaban Ummin, da yake Ummi mace ce mai adalci, ga lura, sai ta gane hakan, dan haka sai ta ce A'AFIA ta rinƙa kai masu abincin cikin ɗakinsu suci a tare.
Chapter 28 · 0% Book details