← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 121

Sashe 52

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya kammala ya wuce dressing room nasa, ita kuma tana kwance a saman bed nasa, yau gata a bed É—in Lion a matsayin budurwar Areef, lallai akwai cakwakiya ba É—an karami ba wai.

After some hours💋

Shirye cikin wani shegiyar wandon jeans mai bala'in kyau da tsada Aseef ya fito, wandon launin blue, sai kuma riga launin ash color, ya yi matukar kyau sosai kamar ba shi ba, sai tashin kamshi perfume ɗin ɗan uwansa yake yi, yanzu saboda tsiya perfume ɗin Lion yake sakawa, tun da ya sami lafiya shikenan ya koyi takurawa Lion shima, ya bi kafar Areef, diamond watch nasu na TRIPLETS yau ya ɗauko ya sanya a hannunsa, dama idan baku mance ba Lion ya karɓe watch ɗin gabaɗaya ya ajiye, to ya je ɗaukar agogon Lion ɗin sai ya ga diamond watch nasu, hakan yasa ya ɗauke shi kawai, glass kuma, baki ya ɗauko wadda baka iya ganin kwayar idanunsa, kuma glass ɗin ba ƙaramin kyau ta yi mishi ba, sarkansu na nan a wuyarsa ko in ce a wuyoyinsu.

Bayan ya kammala shiri tsab ya fito daga dressing room ɗin zuwa cikin ɗakin, babu kowa a cikin ɗakin sai Rimsha dake sume, saman gadon ya hau tare da shafa fuskarta yana ambatar sunanta kasa kasa, shiru bata farka ba, sauƙowa kasa ya yi tare da buɗe fridge ya ɗauko ruwa mai sanyi, kaɗan ya tarfo a hannunsa tare da shafa mata a fuskarta, da yake a nitse ya yi mata, sai ta farka a nitse, ganin shi da black glass ya rufe kwayar idanunsa ba zata iya tantancewa ba sai ta yi zaton Lion ne, abin da mamaki yadda mutane ke kallon fuskokin mutane da dama a fuskar Aseef, dama akwai irin mutanen nan, sai dai basu da yawa a duniya, wadda idan ka kallesu dole sai sun yi maka kama da wani naka, haka halittar fuskarta ke.

Kokarin sauƙa kasa ta yi dan ta gudu kada ya yi mata hukunci, riƙo hannunta ya yi yana mai ambatar sunanta, jin muryarsa yasa ta tsaya tare da ambatar sunansa yaya Aseef, shi kuma mamaki take bashi yadda take banbanta voice nasa dana Areef, ta yi musu farin sani yarinyar nan, ko bata ga face nasu ba, tana iya banbanta voice nasu, akwai ta da kwakwalwa over.

"Waye ya ce miki ni ne? Areef ne fa". Ya faɗa cikin zolaya, dariya mara sauti ta yi ba tare da ta yi magana ba, yana riƙe da hannunta ɗaya cikin nasa ya ciro wayarsa da ɗayan hannu ya fara kiran number daddynta video call.

Bugu ɗaya daddyn nata ya ɗauka, yana zaune kusa da pool yana karatun husnul Muslim, ganinta yasa ya saki wani ƙayatattacen murmushi har sai da dimples nasa suka lotsa sosai, ita ma murmushi take yi sosai tamkar ta shiga ta jawo daddyn nata ra rungume haka take ji.

Sai binsu da ido Aseef yake yi yana murmushi, cikin harshen Hausa suka gaisa tare da fara hira, sai dariya take yi ta manta ma a ina take, almost 30 mins suna hira haka kafin Aseef ya ce "Uncle zan kira anjuma yanzu zata rakani wani waje ne". Da turanci ya yi maganar, okey Musharraf ya amsa da shi, diff ya katse kiran tare da cewa "To tashi muje ki rakani unguwa", ɗan zaro idanu ta yi, "Unguwa kuma yaya Aseef?". Gera ɗaya ya ɗaga mata alamar e, okey ta amsa mishi tare da miƙewa ta sauƙo kasa, har lokacin bai saki hannun nata ba, tamkar wasu mata da miji haka ya riƙe hannunta suka fita waje.

A palon sama ya cikaro da Areef yana ƙoƙarin shiga bedroom ɗin. "Kai, kai, kai, Aseef ina zaka je haka?" Ya yi maganar yana kare mishi kallo, ba karya ya yi kyau sosai. "To sarkin sa ido ina ruwanka da ni, ni dai yanzu bani saƙona ka gani". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce Okey, bai wani damu ba, dan yasan Aseef da Musharraf babu ɓoye ɓoye a tsakaninsu, wata kila Musharraf ne ya gaya mishi in da wasu ƴan uwansa suke zai je duba su.

Juyawa ya yi a tare suka sauƙa palon kasa, Lion yana garden zaune, Aseef da Rimsha suka wuce zuwa garden ɗin, shi kuma Areef ya wuce cikin bedroom nasa.

A ɓangaren Lion ɗin ma haka ne, da ya ce mishi zai je unguwa Rimsha zata raka shi, ya yi tunanin wajen wasu daga cikin ƴan uwan Musharraf zai je, tun da ɗan Kaduna ne Musharraf ɗin, sai bai hana shi fita ba.

Riƙo hannunta ya yi suka koma cikin gida Imran da jelly kuma basu nan sun tafi gidan Abbi, dama tare zasu fita da Rimshan, ganin tana barci a ɗakin Lion yasa ya tafi abinsa, dan shi bai ɗauka a sume take ba, ya yi zaton barci take yi.

ÆŠakin dake kusa dana Areef a palon kasa ya wuce da ita, har lokaci bata É—aura É—ankwalin nata ba, dan bata iya ba, lokacin da suka yi rayuwa da daddynta bata sanya atampha, sai blouse da sauransu, hakan yasa bata iya ba.

"Yaya Aseef ina zamu je?" Ta tambaya tana kallon uban akwatin da yake ƙoƙarin jawowa da hannu ɗaya. "Sarkin tambaya, ki bari idan muka je zaki gani, yanzu dai idan mun dawo wancan akwatin shi ne tsarabarki, sai ki zo ki ɗauka dan ni bani da karfi". Dariya ta yi, akwatin da yake hannunsa yake ja yanzu ma ai tafi tata da ya nuna girma, amma wai bashi da karfi, shima ya iya abin dariya.

Harabar gidan suka fito, da sauri wani soja ɗaya daga cikin shabiyu da Lion ya karon nan, ya nufosu ya karɓa mishi akwatin zuwa bayan motarsa, har lokacin kuma bai saki hannunta ba, yana rike da ita kamar an ce mishi zata gudun mishi ne. Yana isa wajen motar da zai fita da ita wadda Lion ya saya tun farkon zuwansa, sai ga Areef ya fito da wata kwali mai ɗan girma a hannunsa, a gidan baya na motar kusa da akwatin ya sanya mishi kwalin yana faɗin idan ya je ya gaishe mishi da ƴan uwan Musharraf, shima idan ya sami lafiya zaizo ya gansu har gida, okey kawai ya amsa mishi da shi, shi kaɗai ya barwa kansa sanin in da zai je, ya ɓoyewa ƴan uwan nasa, shi kaɗai yasan dalilin ɓoyewar tasa.

Gida gaba yasa Rimsha shi ma ya shiga mazaunin driver, Mark ya yi ƙoƙarin cewa zai raka shi, ya tuƙa su, amma yaki yarda, da su Areef suka tambaye shi yasan wajen ne, sai ya ce e ya sani shi dai su kyale shi, kada su sake tambayar shi ai shi ba yaro bane, haka suka kyale shi dan tun da Lion bai saka baki ba to sun san komai normal ne.

A hankali ya ja motar suka bar gidan, ita dai Rimsha ta zuba idanu tana ganin ikon Allah, sai tafiya yake yi yana kallon wayarsa kamar ya san hanya, da alama kuma ya kunna goggle map ne.

Sai da suka yi tafiya mai É—an nisa lafin su kai kofar gidansu Akila, da mamaki ta juyo tana kallon shi, wai a ina kuma yasan gidan su Akila?. Shiru dai bata ce mishi komai ba, dan tana tunanin daddynta ne ya ce yazo ya gaishesu tun da Abban Imran yayan daddy É—in ne. Shi ma bai yi magana ba sai É—ayar wayarsa da ya É—auko ya kira number Akila É—in, bugu É—aya ta É—auka.

"Hello My Heartbeat". Ya faɗa yana kallon anguwar ta cikin black glass ɗinsa. Shagwaɓe murya tayi tamkar zata yi kuka ta ce "Wai Heartbeat har yanzu baka iso bane? Nifa wlh na gaji". Ta kai karshen maganar idanunta sun ciko tap da kwallah, tana tsaye a kusa da gadonta, ta ci kwalliya sosai da sosai tamkar ba ita ba, atampha ta sanya ɗinkin riga da skit, abin kuma kamar haɗin baki, sak irin kayan jikin Rimsha, da yake tare Imran ya yi musu ɗinkin, ta yi kyau fiye da tunanin mai tunani, kun santa dama da iya tsara make up ba'a magana, sai dai bata yi make up irin na hauka da zai mai da ita kamar aljana ko bebin roba ba, mai kyau ta yi, tana ta tashin ni'imantaccen kamshi.

"Sarkin rigima, ni kada ki yi mini kuka, kada ki ɓata mani kwalliya, yanzu dai abin hawa nake nema, nan da 1 hour zan iso". Cikin sauri ta ce "No ni ka gaya mani a in da kake, zan sanya driver ya ɗauko ka kawai". "Ina bakin gate ɗin gidanku". Ya bata amsa a takaice. Wani irin tsalle ta yi ta dire a tsakiyar gadonta, yau zata ga zaɓin zuciyarta, wayyo Allah daɗi kasheta, zata gan shi ido da ido, tunani ta fara yi ya zasu yi ido huɗu da shi, anya kuwa zata iya? Amma dole ta je su ga juna ko dan taga ya zai yi da ya rinƙa nuna mata bai gane ta ba jiya har da cewa baya jin Hausa, abin da bata sani ba shi ne, yes Areef baya jin hausa kamar yadda ya gaya mata, maganar da ta yi a garden ko baka jin yare zaka fahimci me take nufi tun da a kan hakan suke maganar, bare kuma shi da yake babban jami'i, haka shi ma Aseef ɗin bana jin Hausar, akwai dai wani abu, amma basu jin Hausa, kuma abin ne ma ya haɗe mata ya birkita mata kwakwalwa ta yadda ta ɗauka yes Areef ɗin ne.

Mayafinta ta ɗauka ta nufo waje, a palo ta sami Ammie, ba ɓoye ɓoye ta gaya wa Ammie in da zata je wajen saurayinta, da farko Ammie ta hanata fita, daga karshe kuma da ta ga ƴar tata ta damu sai ta ce to ta je kada ta jima, sai murna take yi ta fito waje.
Chapter 52 · 0% Book details