Sashe 116
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gefenta Ameera ta zauna tana tambayarta a kan me ta aikata da har aka kawo ta nan, ba musu ta gaya mata ga abin da ta yi, daga Raliya har Asiya sai da suka ce eh!! Da karfi, wato ta yanke gabansa gabaɗaya, Jehan da iya shege har da iya gaya musu gabaɗaya ta cire bata rage ba, dafe kirji Ameera ta yi tana jinjina mata irin wannan aiki, ita da take da 21 years a duniya ma yaushe zata iya kallon namiji babba zindir ba kaya bare har ta kama ta yanke, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ai gani da ido ma kawai babbar bala'i ce, duk wata mace a ranar da ta fara kalla sai ta shiga tsoro bare ita Jehan da take ƙaramar yarinya, kuma abin mamaki idan tana magana hankalinta a matukar kwance, tamkar ba ita ta aikata ba, to yau dai sun ji labarin da ya goge musu hadda, daga haka ɗakin ya yi tsin kowa da abin da yake tunani a cikin ransa.
A ɓangaren Rimsha kuwa, bayan ta shiga ɗakin da sallama ɗauke a bakinta, Aseef ne ya amsa mata sallamar tata, kusa da Lion ɗin ta zo ta tsaya tana faɗin "Good morning Yaya Saif and yaya Aseef". Bai amsa ba kuma bai ɗago ba, Aseef dai ya amsa amma bai ɗago ba. Miƙa mishi rigar tasa ta yi tana faɗin "Ga shi nan Nagode". Sai lokacin ya ɗago da kallonsa kai tsaye sai saman idanunta, dan suke yake son kallah, yanzu gabaɗaya ma haushin family'n Nawazudden ɗin ya fara ji, dan suna jefa mishi TRIPLETS nasa cikin haɗari, ya kuma sanya a ransa sai an yanke hannun wannan ɗan'sanda da ya mari Aseef ɗin, dan ba zai barshi ba, bai ga wanda ya isa ya taɓa masa TRIPLETS nasa kuma ya kyale shi ba.
Kallonsu na ƴan sakanni ya yi kafin ya dawo da kallonsa saman rigar da take riƙe da shi ɗin, shiru ya ɗan yi, ya kalli rigar kafin ya mai da kallonsa kan abin da yake yi, bai ce da ita komai ba, kuma ba shi da niyar yin maganar ma baki ɗaya. Shiru ta tsaya tana jiran ta ji me zai ce.
Ganin Lion ɗin bai da niyar yin magana ne yasa Aseef ya karɓi rigar yana faɗin "Sarkin rigima me kuma kika je ki ka taɓo ya shiga miki idanunki? Ko kuka kika yi ne?" Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "Barci dai nake ji". "Daren jiya baki yi barci bane?". Ɗan satar kallon Lion ta yi kafin ta ce "Nayi amma dai ina jin wani ne sosai". Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "To jeki kiyi ko?". Okey ta amsa mishi tare da juyawa ta nufi waje da sauri dan ta je wajen Areef su tafi wajen Jehan, duk da tsananin barci da take ji tana son kallon ƴar uwanta, dole ta danne ta je wajenta.
Cikin bedroom nata ta koma ta kwasanwa Jehan ɗin kayan sakawarta wajen kala biyar, ta haɗa mata da hijabin sallah har kasa, guda biyu, ta ɗauka mata daddumarta ta haɗa, duk dai abin da ta san ƴar uwar tata zata buƙata sai da ta ɗauka mata ta zuba a cikin school bag nata ta ɗauka ta fito waje.
A cikin mota ta isko Areef da Mark suna jiranta, tana shiga Mark ya kunna motar suka bar gidan, sai hira suke yi shi da ita har suka isa prison É—in, kamar dai jiya haka aka rakasu har ciki, in da suka zauna jiya yau ma a nan suka zauna.
Ba'a ɓata musu lokaci ba aka fito musu da Jehan ɗin, gaisawa suka yi da Rimsha kafin ta ɗagawa Areef da Mark gaisuwa, har yau tana cike fal da confidence, babu fa alamar sarewa ko karaya a tattare da ita, cike take da kwarin gwiwa, Areef bai yi mamankin ganin bata yi laushi ba, dan a bincike a kan ta da ya yi daren jiya, ya gano tun ainahinta ma mafaɗaciya ce, ga zafin rai, ga kuma taurin kai, bata magana ta canza, bata da fara'a ko kaɗan, so silent take, bata shiga abin da bai shafeta, sai dai idan taga za'ayi zalinci to fa sai in da karfinta ya kare, hakan nema ya kara karfafa mishi gwiwa a kan lallai tana da gaskiya kuma zai taimaka mata, zai tsaya mata.
"Jehan zaki iya yi mini kwantancen gidan mutumin, wato in da abin ya faru?". Cewar Areef ɗin. Shiru ta yi kamar mai tunani, can kuma sai ta girgiza mishi kai tana faɗin "No daga nan ba zan iya yi maka kwantance ba, sai dai idan naje unguwar zan gane gidan, ni ban taɓa zuwa Kaduna ba sai wannan karon, ban san ya yake ba tare na iya kwatantawa". Shiru ya zuba mata idanu yana kallon yadda take magana, shi dai kome ta yi wlh burge shi take yi, "Okey yanzu abin da ya kawo ni nan, ina son duk wanda zai zo nan ya ce yana son yin magana dake, to kada ki yarda, kada ki kuskura ki bawa kowa damar yin magana da ke, ko da an sanyaki fitowa dole, to idan kin fito ko sun yi miki tambayoyi amsa ɗaya zaki basu shi ne baki san komai ba, daga haka kada ki kara kada ki rage, nasan akwai lauyoyin da zasu buƙaci ganinki or ƴan jarida, da sauran manyan mutane, na san kamar yadda kike da makiya suma makiyan naki suna da makiya masu son ganin bayansu, so wasu zasu samu damar amfani dake dan cimma burinsu a ɓangaren siyasa, dan na ga yanzu faɗar taku ta koma ta siyasa ce, dan haka ki kula, kada ki kuskura ki buɗe baki ga kowa".
Jinjina mishi kai ta yi alamar to ta ji, miƙa mata jakar kayan Rimsha ta yi suka miƙe dan su tafi, ita ma Jehan ɗin miƙewa ta yi dan ta koma ciki. Kamar jiya har ya ɗan yi gaba, sai kuma ya sake dawowa tare da riƙo haɓarta yana faɗin "Shi ne baki tambayi sunana ba ko?" Kallon gefen ido mai kama da harara ta watsa mishi kafin ta ce "To me sunanka zai kara mini?". Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da yi mata signal da gera ɗaya yana faɗin "Wai ke jiya baki yi tunani na bane? Ni fa na kwana tunaninki". Shiru bata tanka mishi ba, dan a cewarta bata da lokacin shirmensa, dama kuma idan baku manta ba, ita haka take, bata san wani abu wai shi shauki or wasa da dariya ba, tsare gida kawai ta iya.
"Au ba zaki yi magana ba?" Nan ma shiru ta yi, tana kokarin buge hannunsa da ya riƙe haɓarta da shi.
"Sarkin faɗa, ai jiya duk naga tarihinki tun kina ƴar shekara 2 a duniya, kika rinƙa takurawa my Rimsha da masifa a baya ko? To zan rama mata ai, mai rama mata ya zo, masifaffa kawai, ni kada ki ce zaki yi mini dan maganinki zan yi, yanzu dai ki ajiye sunana dan zai yi miki amfani, sunan babyn baby kin ji ko?" Zaro idanu Rimsha ta yi tana maimaita sunan babyn baby kuma? Ga shi dai da Hausa ya faɗi babyn baby, to ko a ina ya jiyo sunan oho mishi, shi da ba jin Hausa yake yi ba, ita yanzu ta ma dai'na mamaki a kan TRIPLETS dan sun wuci tunanin mai tunani, idan ka biye musu mamaki ne zai kashe ka, wai babyn baby dan iya shege.
Harara ta watsa mishi kafin ta sa kai ta wuce abinta, juyawa ya yi ya riƙo hannun Rimsha yana faɗin "Wannan ƴar diramace, ta iya juyawa mutun idanunta fararen nan, kuma suna da kyau idanun sosai kamar na uncle na". Ita dai Rimsha ko a jikinta tun da ta zo ta ga Jehan tana nan lafiya lukui ai shikenan.
Suna barin prison É—in suka nufi gida, shiru suka yi a cikin motar Areef yana tunani a kan Jehan, shi kuma Mark yana tunaninsa na daban, ita kuma Rimsha kamar kullum ne, kun sani tunanin Lion take yi.
A É“angaren gidan Abbo kuwa waton gidan su Nawidâ¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
E49-50💋
A ɓangaren gidan Abbo kuwa waton gidan su Nawid, har yanzu dai Abbo shiru ba shi ba labarinsa, soyayya babu kama hannun yaro suke zubawa a tsakaninsu, A'afia ta saki jiki sosai da Dr Nawid, ta mance ma da abin da ya taɓa faruwa da ita a rayuwarta ta baya, ta shiga sabuwar yaruwa mai cike da nishaɗi da annashuwa, mijinta na nuna mata so, surukuwarta na nuna mata tsantsar kula, hankalinta ya kwanta over.
Yau ta kama ranar Friday, tun misalin karfe 5 ta kammala komai nata, ta Shiryawa mijin nata duk wani abin da ta san zai buƙata saboda yau da wuri zai dawo daga wajen aiki, ba zai kai mangariba ba, tsara wanka ta yi tsab ta zuba kwalliya sosai da sosai, doguwar riga baka mai kama jiki ta sanya, ta haye saman bed nata ta yi shiru tana tunane tunane yadda zata yi da batun Ommunsu na case nata ita da Umaisha, gaskiya ba zata iya barin Umaisha ta yi sata ba, idan Ommu ta cika matsawa to ita gaskiya zata sanar da Abbi da kuma Irfan sai dai duk abin da zai faru ya faru, ita ta jawa kanta da kanta.