← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 121

Sashe 31

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk abin da take yi Aafia tana jinta, kawai É—agowa ta kalleta ne tana ganin kamar bata kai wannan matsayi ba, ta fi karfi kula irinsu Bahijja, dama idan baku mance wace ce Aafia ba, kun san ta akwai ta da jiji da kai, abin da ya faru da ita ne ma yasa ta yi sanyi, ta dawo kamar ba ita ba.

Cikin girmamawa Bahijja ta miƙo mata cup ɗin tea ɗin bayan ta kammala haɗawa kenan, bata karɓa ba, sai ta nuna mata saman table ɗin a kan ta ajiye a wajen, hakan ma sai da ta ɗauki ƴan sakanni kafin ta nuna mata ɗin.

Haushi tamkar Bahijja ta yanka mata mari, wata Æ´ar siririya da ita kamar bulala Æ´ar yarinya da ita Dr ya kawota tana yi masu iskanci, cewar Bahijja a cikin zuciyarta.

Ba yadda zata yi, haka ta ajiye mata tare da komawa mazauninta, ta zauna tana mai huci, ko kala Aafia bata ce da ita ba.

Suna a haka har aka yi sallar mangariba da isha, a cikin office ɗin Aafia ta yi sallah kasan cewar akwai komai a ciki, ita kuma Bahijja nata office ɗin na P.A da yake kafin ka shigo cikin office ɗin Nawid ɗin, to a nan nata office ɗin yake, a nan ta je ta yi sallah ta dawo, domin Nawid ya ce ta kula mashi da mata sai ya gama aikinsa ya dawo sannan ta wuce, kada ta kuskura ko ƙuda ya taɓa mashi mata............... To fa🤔

Suna zaune shiru kamar kura me, Aafia ta jingina kai da jikin kujerar tare da lumshe idanu kamar mai barci, ita kuma Bahijja tana ta kare mata kallo, tana son taga dame Aafia ta fita ne?. Mata kenan matsalar mu kenan, kowa so take a ce tafi kowa, da zarar mata sun haÉ—u zasu fara kallon junansu dan suka da me wata tafi su, kowa da irin rayuwarsa, kowa da kalar baiwar da Allah ya yi Mashi, naki baiwar daban, ita ma tata daban, wata kilama baiwarki ta fi tata tsada, kowa da abin da yafi a halitta da kuma rayuwarsa, so bai kamata ki haÉ—a kanki da kowa ba, ki sanya a zuciyarki ke fa ta dabance, ke kaÉ—ai ce babu irin ki, sai ki zauna lafiya, kada ki duba kowa, ki sanya kawai ko kin duba ba irinki bace, ki kasance mai duba rayuwarki kullun ba na wasu ba, hakan ne zai baki damar ki zauna lafiya cikin kwanciyar hankali, Allah yasa mu gyara.

Suna a haka har Dr ya shigo, jin shigowarsa yasa Bahijja ta É—ago kai tana bin shi da kallo, ita kuma Aafia bata motsa ba.

"Mrs Nawid kin yi barci ne?". Sai lokacin ta waro idanunta a kansa. Cool murmushi ya sakar mata "Am sorry na barki zaune ko? Amin afuwa ba zan kara ba, aikin ne ya bani wahala yau, yanzu dai muje gida ko? Dan naga har karfe 9 ta yi". Ya kai karshen maganar yana zame hand gloves da suke hannayensa.

"Yaya Nawid jikina ya mutu barci nake ji, ba zan iya tashi ba fa". Tayi maganar cikin sanyin murya.

Tamkar wasu Tv haka Bahijja ta mai da su, abin haushi kamar ta shaƙe Aafia har sai ta mutu sannan ta saketa take ji, shi kuwa tamkar bai ga Bahijja ɗin ba, ta matarsa kawai yake yi.

"To idan ma ba zaki iya tashi ba, ai ni zan iya ɗaukarki cak ko?". Yana magana yana nufar in da take. "Yaya Nawid ina da nauyi fa". Ƴar dariya ya yi kafin ya ce "A hakan? Yadda kike yar siririyar nan? To idan ma kina da nauyi, ni kuma ina da karfi" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e tana da nauyi duk da take ƴar siririyar.

"To bari na gwada maki ki gani ina da karfi". Hannu yasa yana ƙoƙarin ɗaukarta, cikin sauri ta ce "Wasa nake yi, zan iya tafiya". Girgiza kai ya yi yana faɗin "A'a ni ban yarda ba, dan haka kawai ɗaukarki zanyi gara ma ki tsaya". Yau Bahijja dai taga ikon Allah, tambayar kanta take yi, dama Dr haka yake? Dama yana dariya? Dama yana magana har haka? Wato sune dama yake ɗaurewa fuska kenan? Lallai yau taga abin mamaki.

Shi kuwa É—aukarta ya yi kamar yadda ya faÉ—a suka nufi waje, daidai zai fita ya ce da Bahijja ta rufe mashi office da duk abin da ya dace shi ya wuce gida, daga haka ya fice da ita a kafaÉ—arsa. Da Ido kawai Bahijja ke binsu da shi har suka fita.

Tun da ya fito duk in da ya wuce nurses sai sun kalle shi sun sake waigawa, ba ƙaramin mamaki ya basu ba, sai tambayar kansu suke yi akan yaushe ya yi aure, dayawa daga cikinsu dai sun san bashi da kanwa, shi kaɗai ne wajen Umminsa, to a ina ya samo wannan yarinyar kuma?.

Shi kam bai bi ta kan kowa ba, kai tsaye motarsa ya wuce da ita, sai ɓoye fuska na rashin kunya take yi. A gidan gaba ya zaunar da ita, ya zagayo mazaunin driver ya shiga.

Kasancewar parking space ɗin akwai ɗan duhu, babu haske sosai, sai bai kunna hasken motar ba, ya lallaɓa a cikin duhu ya jawota jikinsa, sosai ya matseta tare da zura hannunsa ta samar wuyar rigarta zuwa ciki.

Bata hana shi ba, kuma bata tashi daga jikin nasa ba, breast nata ya kama ya fara shafasu a hankali yana wasa da su, hannayenta tasa dukka biyu ta rungumo shi, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mashi ba, yanzu ta yi accepted na shi kenan, nan take ya fara wasa da ita sosai son ranshi, bata hana shi ba kuma bata taya shi ba, ta yi shiru tana sauraronsa.

Har sai da agogon hannunsa ta buga masu karfe 10 ya yi, sannan ya saketa yana mai da numfashi tare da lumshe idanu, ita ma sauke numfashi take yi a hankali hankali, alamar ta karɓi saƙon nasa.

Sun É—auki Æ´an mintoci a haka, wadda a kalla zasu kai 10mins. Da kyar ya iya jan motar suka nufi gida.

WANNAN KENAN A ƁANGAREN SU A'AFIA, BARI MU LEƘA ƁANGAREN SU LION WATA KILA KAFIN MU DAWO SU AAFIA SUN ISA GIDA.

GIDAN LION💋

Yau dai Akila da Rimsha sun sha hira kamar ba gobe. Sai misalin karfe 2 da rabi Rimsha ta ce da Akila ta shiga ɗaki ta kwanta ta jira ta, bari ta kaiwa Lion abinci, to ta amsa mata da shi tare da miƙewa ta nufi cikin ɗakin.

Ita kuma ta nufi Kitchen dan É—aukar abincin. Kamar kullum, wanke hannayenta ta fara yi kafin tazo ta É—auki abincin, tana tafiya tana addu'ar Allah yasa ta kai lafiya ta kuma dawo lafiya.

A bakin kofar ta tsaya ta yo sallama, daga ciki Areef ya amsa sallamar tata tare da bata izinin shigowa, tattara dukkan natsuwar da Allah ya bata ta yi, ta kutsa cikin É—akin tana kara yi mashi sallama.

Imran, Areef, kwance suke a saman gadon Lion suna hira, while shi kuma oga yana zaune saman sofa yana bincike a cikin laptop nasa.

In da ta saba ajiye mashi abincin ta nufa, a nutse ta ajiye mashi tare da É—agowa ta gaida Areef da Imran, da fara'a suka amsa, dirowa kasa Imran ya yi yana faÉ—in bari ya je ya É—auko mata abincinta daga gidan Akil, dan tun É—azun AKil ya yi mashi massage akan Umaisha ta gama abinci ya zo ya É—auka mata.

Cikin zolaya Areef ya ce zai bishi domin yau ya kalli bakin Æ´an uwan Prof da bai sani ba, a zafafe Lion ya É—ago da dara daran blue eyes nasa, tare da wurga mashi wani mugun kallo, alamar baka da hankali ne zaka fita?. Dariya ya kwashe da shi, dama dan saboda Lion É—in ya É—ago ya yi maganar, yasan ba ta yadda za'ayi ya fita da wannan ciwon nasa haka, amma kuma kafarsa na bala'in kaikayi, yana burin fita, har tausayawa kansa yake yi akan idan ya samu lafiya kalar yawon da zai yi, sai ya kewaye gabaÉ—aya States na Naija, zai je wajajen tarihi da saurasu, har ya gama tsara kalar yawon da zai yi, addu'ar samun lafiya kawai yanzu yake yi........( To fa lallai Areef ya shirya karewa kasarmu kallo)

Shi dai Imran bai ce komai ba, ya sa kai ya wuce abinsa, ita kuma Rimsha zama ta yi tana jiran Oga ya sauƙo ta zuba mashi abincin.

Sai da ya ɗauki almost 30 mins yana latsa laptop ɗin, ita kuma tana zaune shiru. A hankali cikin natsuwa ya ɗaura laptop ɗin saman hannun sofa tare da miƙewa ya sauƙo kasa, a in da ya saba zama ya zauna.

Ta kasar ido ta saci kallonsa, pajama ce launin fara tas a jikinsa, ya kulle gashin kan nan nasa a bayan wuyarsa, wannan fitinannen daddaÉ—ar kamshin nasa dai kamar kullun take, ba canzawa.

Yana zama shima Areef ya sauƙo daga saman gadon, ya kariso in da suke yana Murmushi. Abincin ta fara zuba mashi kamar yadda ta saba.

"Our Queen zuba mini nima, amma tare zaki zuba mana dake". Cewar Areef, ya yi maganar yana zama kusa da É—an uwan nasa, shima dai pajama ash color ce a jikinsa.

"Yaya Areef ni ai ban iya cin kalar abincinku ba". Ta yi maganar tana turawa Lion abincinsa da ta gama zuba mashi.

Kwaikwayon voice nata ya yi yana faÉ—in "To ai koya miki ci zanyi my Rimsha". Bata san time da dariya ya kubce mata ba, ba iya basajan wajen aiki kawai ya iya ba, ashe har da kwaikwayon murya ya iya, dan kuwa sak siririn voice É—in nan nata ya yi, shi dai Lion tamkar babu shi a cikin É—akin, abincinsa kawai yake ci cikin kwanciyar hankali.

"Dariyar me kike yi mini? Dan na kwaikwayi zazzakar muryar nan taki ko?". Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a. "Kinsan me my Rimsha?". A'a ta bashi amsa.
Chapter 31 · 0% Book details