← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 121

Sashe 43

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Garden É—in gidan suka nufa, sai satar kallon sojojin da Lion ya karo Akila take yi, ita kuma Rimsha tsoronsu ma take ji, fuskokinsu kamar wasu shanaye a É—aure, ita kuma Akila kyau take kalla, taga fararen turawa, ga tsawo ga murÉ—ewar jiki, shiyasa take ta faman satar kallonsu. A Æ´an kwana biyun nan dukka Imran ne yake yin aikin Rimsha na gyara É—akin Lion da na su Mark, dan har ga Allah Rimsha bata iya gyaran É—aki ba, bata san yadda ake yi ba, bare ma gyaran gado, sam bata iya ba, a hankali hankali dai tana koya.

Babu kowa a garden ɗin, zama suka yi, Rimsha ta ce bari ta ɗauko masu ice cream su sha, dan su ji daɗin hira, to Akila ta amsa mata da shi, miƙewa ta yi ta koma cikin gida, ita kuma Akila ta zauna shiru sai kalle kalle take yi, garden ɗin ya haɗu iya haɗawa ba karya. Daga karshe ta ɗauko wayarta ta fara latsawa.

Fitar Rimsha ke da wuya, sai ga Areef sanye yake da Army trouser, da kuma farar T-shirt, ya yi kyau sosai, yau da alama yana ji da tsiya, domin kuwa ya yi kitso guda bibbiyu ta gefe da gefen kunnuwansa, kuma ba ƙaramin kyau suka yi mishi ba, sauran gashin nasa kuma, ya tara a tsakiyar kansa ya ɗaure, hannunsa na riƙe da wani cup mai shegen kyau, sai tiririn hayaki ne ke fita daga cikin cup ɗin, da alama coffee ne a ciki, kafafunsa na sanye cikin home sleepers masu shegen laushi launin ash color, ɗayar hannunsa na riƙe da wayarsa yana latsawa, da alama kuma wani saƙon yake turawa.

Kwata kwata bai san da mutun a cikin garden ɗin ba, sai ya shiga da sallah kasa kasa ta yadda babu wanda zai iya ji, ita dai kanta na kan wayarta tana karanta saƙon ɓoyayyen masoyinta.

Bai lura da ita ba, wucewa ya yi zai zauna, kwatsam ta ɗago kai dan jin ɗan motsi da ta yi, shi ma kuma a lokacin ne ya lura da ita, a razane ta.........❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

_Dedicated to Masoyana masu yi mini comments I really appreciate gaskiya, Allah ya bar zumunci!!!_

*AISHA BAITA JIDDAH
MAMAN YASMIN
Anty rifat
Maman abba
Ruky anty
Mom affan
Hafizee Ayuba
Maman shureim
Maryam
Official Ameera
Hasina
Doctor aysha
Maryam garba
Aisha galadima
Anty safiya
Halima idris
Antyfaty
Rachel
Ummu amatullah
Yasmeen
Anty Karima
Maman sultan
Shafa'atu adam
Oum shureim
Maman amir
Daughter in law*

E17-18

Bai lura da ita ba, wucewa ya yi zai zauna, kwatsam ta ɗago kai dan jin ɗan motsi da ta yi, shi ma kuma a lokacin ne ya lura da ita, a razane ta miƙe tsaye tana kallon shi, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, shi kuma cool murmushi ya saki kafin ya zauna a in da yake son zama tare da ajiye cup ɗin hannunsa. "Why are you standing?" Ya faɗa cikin sanyin murya, ya yi maganar kuma yana ƙoƙarin fara latsa wayarsa.

A hankali ta koma ta zauna tana kare mishi kallo, tabbas wannan shi ne a hoton da ɓoyayyen masoyi ya tura mata, sai dai hoton tun yana ɗan 22 years kenan? Ta tambayi kanta da kanta, duk da bata kalli fuskarsa sosai ba a hoton, tabbas soyayyar da take yi mishi ta gaskiya ce, tabbas ko a ina zata iya gane shi, tabbas ma shi ne, TO FA BABBAR MAGANA.

"Prof sister right?" Ya faÉ—a yana mai dawo da kallonsa a kanta, da kyar ta É—aga mashi kai alamar e, mamaki take yi yadda ya nuna kamar bai gane ta ba, kenan yana tunanin ita ba zata iya gane shi bane dan ya tura mata hotonsa yana É—an 22 years ko yaya yake nufi? Ta sake tambayar kanta da kanta, tambayar kuma da bata da amsarsa.

"Heartbeat right?" Ya sake tambayarta, kara zaro idanunta waje sosai kamar zasu firfito su faÉ—i kasa ta yi, domin sai yanzu ma ta ji wannan zazzakar murya tasa, kuma wlh yadda ya kira Heartbeat É—in nan, haka yake kiranta a waya, tabbas shi ne, daddaÉ—ar muryarsa ne, kyau nasa ne, komai da komai na sa ne, ta kasa magana, sai kare mishi kallo take yi, yanzu tambaya biyu ya yi mata bata amsa ba.

Ganin tana ta kallon shi ne yasa ya kashe mata ido É—aya tare da É—aga mata gera É—aya yana faÉ—in "Nayi maki kyau ne?" Duk maganar da yake yi cikin harshen turanci yake yi, babu hausa ko É—igo a bakinsa, watakila yana tunanin bata gane shi bane yasa bai yi hausa ba, ko kuma dai ya abin yake ne? Na kasa ganewa.

"Heartbeat ki yi magana mana? Why ki ke ta kallona haka? Shin na yi wani laifi ne, ko dai kina so na ne?". Ya kai karshen maganar cikin zolaya.

Miƙewa ta yi da sauri dan ta gudu da nufin ta bar wajen, in dai shi ne ɓoyayyen masoyi to bata son shin, domin dama idan baku mance ba, ta ce bata son maza masu yin gym, kuma shi Areef tamkar Lion yake, yana yin gym sosai da sosai.

Ganin zata gudu ne yasa ya yi saurin miƙewa ya riƙo hannunta yana kare mata kallo. "Heartbeat what is the problem? Why ina yi maki magana you refuse to amsa me, and then kina ta kallona, daga karshe ki tashi zaki gudu, menene matsalar, ko dai kin fasa so na ɗin ne?" Ya faɗa yana ɗaga mata gera ɗaya alamar zolaya.

Ƙoƙarin kwace kanta take yi dan ta gudu, da karfi ya jawota jikinsa har sai da ta buge shi a ciwonsa, wash ya ɗan furta da karfi.

Zuba mashi ido ta yi tana kare mashi kallo, ya riƙera sosai, sai kare mata kallo from Head to toe shi ma yake yi, wani tunani ne ya faɗo mata, tun da bai nuna ya santa ba, ita ma ta biye mashi a haka taga karshen me zai yi, ba dai ya ce ranar Wednesday zai zo gida ba, to ai gobe ne Wednesday, ta biye a je a bai santa ba, zata ga ranar Wednesday idan ya zo gida kuma me zai sake ce mata, dan dai ita ta san wlh shi ne wannan, ko kaffara ba zata yi ba, kallon ƙurillah ta yi wa hotonsa, wannan brawn hair ɗin nasa, sannan ga muryarsa, yadda ya kirata da Heartbeat yanzu, tamkar yadda yake faɗa ne a waya, ga shi yanzu ya ce ko ta dai'na son shi ne, akwai hujjoji da dama da suke tabbatar mata da tabbas ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba shi ɗin ne.

Yin wannan tunani yasa kasa kasa ta ce "To sake ni na gaya maka". Da hausa ta yi maganar, amma kuma tamkar ya ji me ta ce, sai ya sake ta tare da komawa ya zauna a saman sofar, domin sosai yaji zafin buge mashi ciwon nan da tayi.

Komawa itama ta yi ta zauna a saman nata sofar in da ta tashi. Zuba mata waÆ´an nan shegun rikitattun dara daran ash eyes É—in nasa ya yi, duk yasa ta tsargu, sai wasu Æ´an kame kame take yi, mamaki ne ya rufe shi, wai ita heartbeat me matsalar ta ne? Ya tambayi kansa.

Ita kuma Rimsha tana barin wajen da nufi ta je ta kawo masu ice cream, a palo ta haɗu da Imran ya dawo daga karɓo musu kaya, zai fita ita kuma ta shigo palon kenan, sai ya ce ta je ta kaiwa Saif abincin rana, mamaki tayi sosai akan meyasa daga jiya zuwa yau Lion yake cin abicni akan lokaci, kuma yake barci a kan lokaci, Meyasa? Abin da bata sani ba shi ne, dama tarin tulin aiki da rashin kwanciyar hankali yasa baya samun damar cin abinci, amma yanzu Alhamdulila da mumnynsa da ɗan uwansa sun tsira daga wajen waƴan nan tsinannun matsafan, babu wata aiki da ta rage mashi fa ce aikin daddynta daya fara last week, yanzu ya samu kwanciyar hankali sosai, domin shi ƴan iskan Nigeria bai ɗaukesu a wata tsiya ba, gani case ɗin daddynta yake yi kamar cin kaza ne, dama yakin da su TAG za su je ne yasa bai mai da hankali a kan aikin daddyn nata ba, ya tattara hankalinsa a kan nasarar su TAG ɗin, yanzu kuma tun jiya bai sake duba case ɗin ba, yana ɗan busy na tura gawarwakin sojojin da a ka kashe zuwa ga iyalansu da sauran abin da ya dace a matsayinsa na babba, to a takaice dai yanzu ya sami kwanciyar hankali yana da damar cin abinci sosai da kuma samun barci akan lokaci. To kun ji abin da yasa tun da Rimsha ta bar garden bata dawo ba.

Shiru suka zauna a garden É—in, tunani kala kala ne cike fal a cikin ranta, shi kuma ya tsareta da idanu sai kallonta yake yi kamar zai cinyeta É—anye, tamkar mai son yin wata magana, amma kuma bai ce komai ba.

Ganin ta yi kasa da kai ta yi shiru ne yasa ya É—auko cup É—in coffee É—insa yana faÉ—in "Zo na baki coffee a baki to, kila idan na baki, zaki iya yi mini magana" . Har wayau cikin harshen turanci ya yi maganar.

Kara rikicewa ta yi, wlh haka yake ce mata a waya, sai ya ce ta zo ya bata coffee a baki, amma yanzu ya nuna kamar bai gane ta ba, lallai ma mutumin nan ya kware a iya basaja, shi É—in number É—aya ne.

Shi kuma ya kasa hakuri ya shareta, yana son ta saki jiki su yi hira, dan haka sai ya miƙe ya dawo kusa da ita, a saman sofar ya zauna yana faɗin "To buɗe baki na zuba maki". Yana magana yana kawo mata cup ɗin saitin ɗan bakinta.

"Na ƙoshi ni kam!" Shi ne abin da ta faɗa, kuma cikin harshen Hausa ta yi maganar, ga mamakinta sai ta ji ya ce "No open your mouth". Shi kuma dai da turanci yake magana, kwata kwata yaki furta ko word ɗaya da Hausa, amma kuma ga dukkan alamu dai yana jin yaren, tun da ga shi idan ta yi magana yana ji har yana amsa mata da English.
Chapter 43 · 0% Book details