← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 121

Sashe 66

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusa da shi ya karisa tare da kawo mishi spoon ɗin saitin ɗan bakinsa, kin buɗe baki ya yi, dan ko warinta baya son ji, ya ga kokarinsu ma da suka iya cin har two two spoon's, kuma ya jinjinawa Rimsha kamar yadda ya faɗa, shagwaɓe murya ya yi kamar zai yi kuka "Please mana my pleasure, idan baka ci bafa, ba ni ba barci yau, haba mana son ɗin daddy". Idan suka kira shi da wannan sunan na son yana tuna mishi abubuwa da dama da suka wuce, suna ne da daddynsa yake kiran shi da shi tun ranar da aka haife shi, har ya kai 13 years kafin daddy ya dai'na kiran sunan, ba kuma wai ya daina gabaɗaya ba, a'a yana kira, amma sai idan yana rarrashin shi a kan abu, sai ya rinƙa ce mishi haba my son, ka yi kaza mana, to sunan tana da matukar muhimmanci a wajensa.

Ba dan yaso ba ya buɗe baki ya karɓi abincin, a nutse ya tauna yana mai jin wani irin yanayi a tattare da shi, wai yau shi ne ya ci abincin Naija, abincin ma na Rimsha, gaskiya TRIPLETS ba su kyauta mishi ba, shi kuwa Aseef da yake gwani ne a neman magana har da wani cewa ya karo Mishi ne ko kuma ya ɗauko mishi har da plate ɗin ma baki ɗaya, buɗan bakinsa sai ya ce a'a ba iya plate ɗin ba kawai, ya ɗauko mishi har da mai abincin ne ya manta, Aseef da iya shege, yana sane sarai magana Lion ya gaya mishi, amma saboda neman rigima sai ya je ya kamo hannunta, shi dai Areef sai binsu da idanu yake yi, kusa da shi Lion ɗin ya zaunar da ita tare da riƙo hannun ta ya sanya cikin na Lion ɗin yana faɗin "To ga mai abincin nan".

Rai a matukar ɓace ya kwace hannunsa tare da kaiwa Aseef ɗin damka a wuya, ya miƙe tsaye, da karfi ya shaƙesa, Areef kuwa gyara zamansa da kyau ya yi ko ajikinsa, dan sun fi kusa, shi nashi ido ne kawai, a guje ta miƙe zata bar wajen, da hannu guda ya damkota tare da dawo da ita kusa da Aseef ɗin, shi kansa ya rasa wani irin hukunci zai yi musu, yau ransa ya ɓaci sosai tun da har ya iya shake Aseef mai gabaɗaya, wlh Areef ko a jikinsa, Tv ma ya mai dasu, har da guntun murmushi, dama yasan za'ayi hakan, shi ma Aseef ɗin ganganci ne sai kace bai san halin ɗan uwan nasu ba, zai ja a kashe ƴar mutane a banza.

ASEEF

Da kyar ya iya buɗe baki ya ce "Lion ka shake ni, ita kam ka sake ta, ai ba laifinta bane, bata san komai ba, ni nayi laifi". Sai lokacin ya dawo da kallonsa kanta dan yaga wai shi wannan wace iriyar yarinya ce, cikin tsawa ya ce mata "Me kika yi musu da har suke sonki fiye da kansu?!" Ya yi maganar tare da zame hannunsa daga wuyar Aseef ɗin ya damko nata wuyar, dama ga wuyan nata ɗan siriri, dogo zai yi daɗin shaƙa, "Ba dake nake magana bane?!" Ya sake daga mata tsawa, tamkar zata saki fitsari a wando, ta yi bala'in tsorata na karshe, ya shaƙeta sosai ba ta yadda za'ayi ta yi magana, sai girgiza mishi kai take yi, hawaye wani na bin wani daga idanunta zuwa kuncinta.

Zubawa face nata ido ya yi, wannan fuska nata a duk san da ya gani sai tsikar jikinsa ya tashi, tabbas koma wace ce mai irin wannan face ɗin tata, tana da matukar muhimmanci a rayuwarsu, ya zama dole ya san wace ce, shiru ya yi yana kallonta ba ko kyaftawa, ya kasa kawar da kallonsa, duk da hakan yana sa tsikar jikinsa gabaɗaya ya rinƙa tashi, tabbas akwai wani sirri tattare da wannan yarinya, ba'a banza su Areef suke sonta har haka ba, ga shi shima yanzu ya tashi da zafinsa zai mata hukunci, daga ganin face nata ya ji jikinsa ya mutu, dole akwai dalili.

Ganin ya yi shiru yana kare mata kallo ne yasa Areef miƙewa ya kariso wajen nasu, shi ma Aseef ido yake binsu da shi, sai mamaki yake yi na irin kallon da Lion yake yi mata, ga shi kuma ya shaketa bai sake ta ba, kamar zata mutu, shi kuma sai ƙoƙarin karantar face ɗin nan nata yake yi ko zai iya tunano wace ce mai irin shi, a ina kuma yake yawan ganinsu da Josephine, dan baya son ya tambayi Josephine kai tsaye, yafi so sai ya yi bincike a kan faɗar tsakaninta da daddynsu ya gano mai gaskiya kafin ya yi magana da ita, amma wannan mai face irin na Rimshan ta tsaya mishi a ransa, ta hana shi sukuni, duk yadda aka yi, alaƙa mai karfi ne a tsakaninsu.

"Lion ka sakar mata wuya kada ta mutu". Shi ne abin da Areef ya faɗa da ya kariso wajen, jin voice ɗin ɗan uwan nasa yasa ya zame hannun nasa da wuyarta tare da juyawa da sauri ya bar wajen, bin shi da kallo suka yi, da sauri ita ma ta bar wajen dan ta tsorata da irin kallon da yake yi mata, ba shaƙeta da ya yi bane ma ya dameta, tsoronsa ya fi wannan shaƙewa rikitata, ƙanƙame wuyar tata da hannayenta dukka biyu tayi, da kyar take numfashi ta nufi bedroom nata.

Aseef ne ya matso kusa da Areef ɗin yana faɗin "Me yake damun Lion ne? Ko dai yana son sister ne". Nisawa Areef ya yi "Ko kusa ko alama, a yanzu dai babu sonta ko ɗigo a ransa, ina ganin dai akwai abin da yake nema a tattare da ita, idan hasashena ya zama gaskiya a matsayina na jami'i, ko dai tana yi mishi kama da wata da ta tsaya mishi a rai, ko kuma akwai abin da yake bincika a kanta, akwai dai wani abin a kasa, amma ba soyayya bace, sai dai ina fatan hakan ya zama soyayya a tsakaninsu, tabbas zai bukace ta dan bincike, ina fatan hakan ya zama sanadiyar faɗawar shi soyayya da ita, ina son ganin ta cikin farinciki, ina son ganin ta sami abin da take so, ya Allah ya tabbatar mana nan ba da jimawa ba". Shiru Aseef ya yi, ya shiga duniyar tunani, ko Amin ɗin ma bai iya amsawa da shi ba, to wace ce Lion zai rinƙa gani tana yi mishi kama da sister? Aseef ne ya yi wa kansa wannan tambayar a cikin zuciyarsa.

Sun jima tsaye a wajen suna tattaunawa, daga bisani Areef ya É—aukawa Rimsha abincinta ya bi bayanta da shi, dan yasan yunwa take ji, shi kuma Aseef É—akin Lion É—in ya nufa bayan ya É—auka mishi laptop nasa da wayarsa da ya bari a garden É—in.

Kwance ya iskota a saman bed nata, ta yi shiru tana tunanin yadda ta ga fuskarsa kusa da kusa yau, sai taga ya yi mata kama da wani wadda ta sani, sai dai ta rasa wanene, yau kewar ƴan uwanta ya dawo mata sabo, tunani take yi ko a wace duniya suke yanzu Oho. Gefen bed ɗin ya zauna tare da ɗaura mata abincinta a saman bedside drawer, rarrashinta ya fara yi yana bata hakuri tare da yi mata alkawarin akan Lion ba zai sake yi mata hakan ba, dan kuwa, idan ya canka daidai, mai irin wannan fuska tata tabbas ta tsayawa Lion a rai, kuma da alama a yinwa ce yake da ya san wace ce, so zai rinƙa binta a hankali.

Da kyar ta ƙaƙalo murmushi dole ta yi mishi tare da miƙewa zaune, abincin ya ɗauko ya miƙa mata, kusan a tare suka ci, dan sai da ya taya ta ci, saboda ita yau har daɗin abincin ya ji, sai da ya tabbatar da ta ƙoshi tap, ya miƙe ya nufi waje yana yi mata sai da safe.

Yana fitowa palon sama suka ci karo da Imran da jelly, cike da kulawa ya ce "Prof ina kuma zaku je a daren nan?". Ganin shi yasa jelly ta ɓuya a bayan Imran, dan mutuwar tsoron shi take yi, har wani duhu duhu ta fara gani. Ƴar murmushi ya yi yana faɗin "Jelly ta ce mini ba zata zauna a ɗakin sama ba, wai kuna nan sama, tsoronku take ji, dan haka mu koma ɗakin kasa". Jinjina mishi kai ya yi tare da wucewa ya shiga ɗakin Lion ba tare da ya sake yin magana ba.

Zaune suka isko Lion a saman gado, duk wasu kaya na mummynsa da ta bar mishi ya watsasu yana dubawa, da mamaki Areef yake bin kayan da kallo, kwata kwata ma shi bai san da waÆ´an nan kaya nata ba, ga shi babu hoto a ciki ko gwara É—aya da zai gani ko dai a cikin kawayenta ne mai irin wannan fuska take, wani zuciya ce ta ce mishi to ya É—auki Rimsha a hoto mana ya turawa Josephine É—in, ya tambayeta wace ce mai irin wannan face É—in, nan take ya É—aure fuska yana faÉ—in no, shi baya neman taimakon kowa, komai da kansa yake yi, É—auko hotunan Josephine É—in ya yi daga cikin wannan É—an akwatin, lokacin tun tana budurwa, duk hotunan ita kaÉ—ai ce, babu ita da kawa ko Æ´ar uwa, a lokacin face nata sak na Aseef, ba karya Josephine kyakkyawar gaske ce, hancin nan nata kamar ita ta yi wa kanta, ga É—an karamin red mouth nata irin na Lion É—in sak.

Hotunan daddynsa ya kuma kwasowa, lokacin daddy na saurayi, yadda kasan Lion photo copynsa ne, da yana saurayi sak Lion ɗin, dama ga kalar idanunsu ɗaya, su dai su Areef zama suka yi suka zuba mishi idanu suna ganin ikon Allah ikon gaske, duk ya watsa komai da komai, sai dai babu komai a ciki da ya danganci abi da yake son sani, kwashe su ya yi ya mayar, da nufin idan ya gama bincike a kan daddyn Rimsha zai waiwayesu, koma wace ce kuma kome alaƙarsu sai ya gano, dan ba ta yadda za'ayi yana kallon Rimsha tsikar jikinsa na tashi kamar ba lafiya ba ace kuma babu wani abu a tsakaninsu, ina ba zai yiwu ba.
Chapter 66 · 0% Book details