← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 121

Sashe 9

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To meyasa kike kuka?". Sake girgiza mashi kai ta yi, bai takura mata lallai sai ta yi magana ba, domin kuwa yasan ba zata iya yin magana ba, saboda kukan da taci ta ƙoshi.

Bayanta ya fara shafawa a hankali hankali yana jin yanayi mai daɗi a tattare da shi, ita kuma tun tana sassauta kukan nata har ta dai'na gabaɗaya, sai ajiyar zuciya na wadda ta ci kuka take sauƙewa.

Sun É—an jima a haka, har barci ya fara É—aukar ta, "Muje ki kwanta a gado ko?" Can kasa kasa ta jiyo voice nasa.

Kasa miƙewa tayi daga jikin nasa, domin kuwa duk jikinta a mace, zuba mata ido ya yi yana mai jin wani irin yanayi da ba zai iya fassara shi ba a tattare da shi.

"Kanwata, a nan kike son kwanciya ne?" Ya sake magana kasa kasa kamar mai raÉ—a.

ÆŠan motsawa kaÉ—an ta yi ba tare da ta yi magana ba. "To shikenan É—an É—aga kaÉ—an bari na É—auke ki mu haura saman gado ko?".

Jin abin da ya ce yasa ta yunkura da iya karfinta dukkan, a sukwane ta miƙe daga jikin nasa, nan take wani irin muguwar tsoro ya kamata, abin da ya faru da ita a baya ne ya fara dawo mata, nan take ta birkice mashi, ta fara yin wani irin abu kamar bata da lafiya.

A wannan karon sosai ya yi mamakinta, zuba mata idanu ya yi, tana ƙoƙarin miƙewa, cikin sauri ya riƙota yana kallon face nata.

Kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ta sa mashi, sai ƙoƙarin kwace hannunta take yi, dan ta gudu, ko ina zata je?.

Miƙewa tsaye ya yi har lokacin yana kallonta, kasancewar shi na babban likita, sai kwakwalwarsa ta fara hasasho mashi matsalarta, domin kuwa wannan abin da take yi, ya yi kama da yarinyar da aka yi wa fyaɗe ta karfin tsiya, wadda hakan kuma dama yana birkita masu kwakwalwa.

Cikin sauri ya kori shaiɗan tare da kawar da wannan tunani daga ƙwaƙwalwarsa, dan dai shi yana yi wa familyn Imran kallon salihan bayi, ya yi imanin da wuya a sami hakan a cikin jinin Prof, kuma ko da an samu ma, ya yi Imani ba za su ɓoye wa mijin da yarinyar zata aura ba, abin da bai sani ba, shi ne, gabaɗaya family'n ma mutun uku ne suka san da zancen, kuma da alama suma mutun ukun nan sun mance da zancen ma baki ɗaya. BABBAR MAGANA

Jawota jikinsa ya yi ya rungume tare fara gaya mata kalamai wadda za su sanyaya mata rai, ya yi amfani da matsayinsa na cikakken namiji mai ilimi da hankali, kuma ya fita shekaru.

Tun tana tureshi har ta hakura ta lafe a jikin nashi, mamaki yake akan me yake damunta, ya san dai a shekarun tan nan kam, tasan me ake nufi da aure, sannan kuma tana da ilimi sosai, amma tana yi mashi wasu irin abubuwa da suka É—ar sa mashi ? (Alamar tambaya) a ransa.

Cikin dabara ya yi mata wayo suka koma saman gado, a tare suka kwanta tana jikinsa. Sai lallaɓata yake yi kamar wata kwai a saman tray, Bawan Allah ya rungumi kaddararsa, to amma matsalar idan ya gano ba budurwa bace ita ya kenan?.

Suna kwanciya, ba jimawa ta yi barci, sai faman sauƙe ajiyar zuciya take yi a cikin barcin nata.

Shi kuma, sai faman shafa bayanta yake yi, yana É—an bubbugata kamar Æ´ar baby.

Sun jima a haka kafin nan ya lura da uban zufar da take haÉ—awa saboda lace É—in jikinta.

Cikin dabara ya sanya hannu ya É—auko remote É—in Ac. Ya kara gudun, sannan ya mai da remote É—in, a hankali ya fara bin kayan jikinta da kallo, lace É—in ya yi mata nauyi ta kwana da su.

Cikin dabara ya sanya hannu ya zuge zip É—in rigar kasa, domin ya rabata da su, ko zata É—an ji daÉ—in barcin, har lokacin kuma, tana kwance a jikinsa.

Bayan ya zuge zip ɗin kasa, cikin dabara ya mai da ita saman gadon ya kwantar da ita, sannan ya miƙe zaune, hannunsa har kerma yake yi wajen sanya hannunsa ya cire mata rigar tata, ya ɗaura mata a saman bedside drawer, juyowa da zai yi da nufin ya cire mata zanin, karaf sai saman kirjinta idanun nasa suka sauƙa.

Shiru ya zuba mata ido yana kallonta yadda take barcinta, ga kirjin nata masha Allah. Ya É—an É—auki lokaci a haka kafin ya daure ya kawar da kansa, ya cire mata sarkar wuyarta da abin hannu cikin dabara, sannan ya kai hannunsa ya zame mata zanin jikinta tare da kashe wutar É—akin wai dan ma kada ya ganta ta É—aga mashi hankali, domin baya son kusantar ta a yau, ya lura tana tsorace da shi sosai, ya fi son ya barta har sai ta saki jiki da shi sosai, sannan duk abin da zai faru ya faru.

Kwanciya ya yi É—an nesa da ita tare da jawo bargo ya shiga domin shi sanyi yake ji, ba komai bane kuma ya ja mashi jin sanyi fa ce yanayin na sha'awa da ya tsinci kansa a ciki, juya mata baya ya yi tare da yin addu'ar barci, sannan ya juyo ya tofa mata, kafin ya yi wa kansa, daga nan ya ce asuba ta gari.

Yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.

GIDAN LION💋

Tana tsaka da barcinta, can cikin ƙwaƙwalwarta ta fara jiyo karar wayarta, a hankali hankali ta fara jiyo ringin ɗin, ɗan motsawa ta yi tare da gyara kwanciyarta, ta kara jawo lallausan pillow ta rungume a kirjinta, tana mai cigaba da barcinta.

Sake kiran wayar aka yi a karo na biyu, a wannan karon har tsakiyar kanta ta jiyo ringing É—in wayar.

Slowly ta faro dara daran fararen sleeping eyes nata waje, wadda suka É—an sauya launi saboda barci.

Cikin sauri ta miƙe zaune ganin yadda rana ta take, wani irin sara mata kanta ya yi, cikin sauri ta dafe kan nata tana karato Alhamdulilahil lazi ahyana bada ma'amatani wa ilaihin nushur....

Ta kai karshen addua'o'in nata tare da sauke idanunta akan wayarta dake saman bedside drawer yake ta faman ringing yana neman agaji.

Jikinta duk a mace, hannu ta kai ta É—auko wayar, My lovely Anaya shi ne sunan da ya bayyana a kan screen É—in wayar, É—an washe idanunta ta yi tare da É—an motsa É—an bakin nan nata kamar zata yi magana, hakan kuma yasa dimple nata gabaÉ—aya suka lotsa sosai.

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ɗauki kiran, ta kara wayar a kunnenta.

Daga ɗayar ɓangaren Anaya ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta ce "Hello Beautyn Uncle Faisal". Guntun tsaki ta ja kafin ta ce "Anaya bana son magana dake fa".

Dariya ta yi tana faÉ—in "To nima bana son maganar ai, Yanzu na dawo daga school, kuma yau wlh uncle Shitu ne ya zo ya É—auke mu, na so kiga uncle Shitun nan, saboda na gaya maki yana sonmu sosai, Musamman ni, ya ce ina mashi kama da wata Æ´arsa da ta rasu".

Wani irin bugawa Rimsha ta ji zuciyarta ya yi jin Anaya ta ambaci sunan Uncle Shitu, sai dai yarinta ya hana ta tayi tunani a kan ko dai nasu Uncle Shitun ne, domin ita ma tana tunanin Uncle Shitun nasu ya mutu, hakan yasa bata taɓa kawowa shi ɗin bane, mafiya yawan lokuta Anaya tana yawan yi mata maganar uncle Shitun wadda ya kasance shi ne yake kaisu school wata rana, haka kuma yana zuwa ɗaukarsu wata rana, shi ne yake kula da gidan Hassan, wato daddy Anaya, da yake idan baku mance ba, Hassan baya zama, sai weekend yake dawowa, to hakan yasa ya wakilta uncle Shitu dan kula mashi da gida, abin da yasa ya yi hakan kuma, saboda shi yasan waye uncle Shitu, yasan tarayarsu da Hosaini sa, shiyasa kawai bai damu ba, ya bar mashi ragamar kula mashi da gidansa, ya san uncle Shitu mutun ne mai gaskiya, kuma ita Rimsha bata taɓa cin karo da shi ba, domin kullun ana riga zuwa ɗaukarta, tana tafiya ta bar Anaya a school, haka lokacin zuwa, tana riga Anaya zuwa school ɗin, to da yake ita bata cika son hayaniya ba, da ta zo school zata wuce class nasu ta zauna, hakan yasa ko an kawo Anaya bata ganin waye ya kawota, kuma ba kowa ce Uncle Shitu yake cewa Anaya tana mashi kama da ƴarsa ba face Jehan, dama idan baku manta ba, na gaya maku ba in da Anaya ta bar Jehan a kamanni, ita Anaya bata san tarihinsu Jehan ba, amma daddynta ya sani, kuma ba wanda ya sanar da su, to shima dai uncle Shitu yana tunanin su Jehan sun mutu ne, hakan yasa yake cewa sun rasu. ALLAH SARKI, WANNAN ZALUNCI DAME TA YI KAMA? SUNA RAYE AMMA KOWA YANA TUNANIN ƊAN UWAN NASA YA MUTU, SABODA SUN SAN ABIN DA YA YI NIYAR HALLAKASU BA ABUNE DA ZA SU IYA ZULLE MASHI BA, SHI MA DADDYN RIMSHA YANA TUNANIN SUN MUTU NE YASA YA BAR KASAR BAKI ƊAYA, HAKA SU MUMMY SUNA TUNANIN YA MUTU, JEHAN NA TUNANIN RIMSHA TA MUTU, SU MUMMY SUNA TUNANIN RIMSHA TA MUTU, SANNAN YANZU SUNA TUNANIN ITA MA JENAN TA MUTU, RIMSHA NA TUNANIN SUMA SUN MUTU, WANNAN AZZALUMI DA YA RABASU ALLAH YA SAKA MASU, SABODA ABIN DUNIYA, KAI INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN, YA ALLAH KASA MUFI KARFIN JUƘATANMU. WANNAN KENAN, MU KOMA KAN LABARI.

"Allah sarki Anaya ki gaida mani da uncle Shitu É—in kin ji, In Sha Allah zamu haÉ—u"

"E mana Rimsha, ai dole ma, yanzu dai me ya sa baki zuwa school ne?".
Shiru ta É—an yi domin bata san me zata ce da Anaya ba,.

Jin ta yi shiru ne yasa ta ce "Rimsha, lafiya kuwa?". Ƴar firgita ta yi "Lafiya lou Anaya, In Sha Allah zan zo school gobe kin ji ko?". Jinjina kai ta yi sai dariya take, har ga Allah tana masifar kaunar Rimsha sosai da sosai. HMMM AI JINI BA WASA BA.
Chapter 9 · 0% Book details