← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 121

Sashe 29

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da ta ɗauko abincin ta dawo ɗakin, har ya cire kayansa ya shiga toilet, saman Chinese carpet dake tsakiyar ɗakin ta ajiye masu abincin tare da miƙewa ta nufi drawer kayansa dan fitar mashi da kayan sakawa.

Kananan kaya na shan iska ta fitar mashi, a saman bed nasu ta É—aura kayan, ita ma ta kwanta a gefen kayan tana jiran fitowarsa.

After some minutes ya fito É—aure da towel a kugunsa, tsayuwa ya yi a wajen drawer kayansa tare da zuba mata ido, ita kuwa tana jin fitowar shi, amma taki É—agowa ta kalle shi.

"Mrs Nawid yanzu dai ba za'a taya ni sanya kaya ba?". GyaÉ—a mashi kai ta yi tana daga kwance, har lokacin kuma taki É—ago kai.

Bai sake magana ba ya kariso wajen gadon, kayansa da ta ajiye mashi ya É—auka yana mai bin kayan da kallo, har cikin ransa ya ji daÉ—in kayan da ta fitar mashi, hakan ya nuna lallai tana da kula sosai, a É—an zamansu kwana biyun nan, har ta fahimci irin kayan da yake son sanyawa idan yana gida, abin ya sanya ya kara jin sonta a ransa.

Toilet ya koma dan baya son yin duk wani abin da bata so, yasan ba zata ji daÉ—i ya sanya kaya a cikin É—akin tana ciki ba, tun da ba sabawa sosai suka yi ba, hakan yasa ya wuce toilet abinsa, kuma shima a yanzu dai ba zai iya sanya kaya a gabanta ba.

A yadda ya barta a haka ya sake fitowa shirye ya sameta, gaban mirror ya tsaya domin ya shafa mayukansa.

"Mrs Nawid ki zo ki taya ni shafa mai, idan ba haka ba, Allah zan yi maki alluran barci, dan tun da ba tayani aiki zaki nayi ba, gara kawai idan na dawo na rinƙa yi maki alluran barci sai nayi aikina ni kaɗai, kuma bayan haka zan ɓata dake tun da kina da son kai, ni in tayaki aiki, ke kuma baki son tayani ko?". Cikin zolaya ya yi maganar yana mai taje gemunsa.

Miƙewa ta yi tare da zuro kafafunta kasan gadon, kafin nan ta miƙe gabaɗaya, gabansa ta isa ta tsaya tana mai ɗauko Lotion da yake amfani da shi.

Da mamaki yake kallonta, bai yi zaton zata shafa mashi É—in ba, ya zolayeta ne kawai, ashe dai zata yi mashi É—in, a lallai yau rana ce ta Sa'a a gare shi.

"Zan iya rungume matata?" Ya faÉ—a kasa kasa, shiru ta yi Mashi, mamaki ma yake bata, wai komai zai yi mata sai ya tambayeta sai ka ce ita ta aure shi ba shi ya aureta ba.

ÆŠan shafa gefen fuskarta ya yi yana mai kara faÉ—aÉ—a murmushin kan fuskarsa, ita ma sai murmushi take yi ta wani yi kasa da kai tana murza mai a hannunta.

Jawota jikin nasa ya yi, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. "Dama kin ce na koya maki kiss da sumbata ko?". Shiru ta yi mashi tana runtse idanunta. "To buɗe idanu mu kalli juna sai na koya maki daki daki ta yadda zaki fi iya ɗauka da kyau".

Ƙin buɗe idanun nata ta yi, har lokacin kuma tana Murmushi. A hankali ya rankwafo da kansa tare da haɗe fuskokinsu waje guda, jin tana iya shakar numfashinsa ne yasa ta razana sosai, nan take abin da ya faru a baya ya dawo mata sabo, a kiɗime ta fara ƙoƙarin kwace kanta daga gare shi, kara kankameta ya yi, dan shi bai kawo komai a ransa ba, ya yi zaton bata saba bane yasa take son guduwa.

Ba tare da ya yi magana ba ya ɗaura bakinsa a saman tata, a nutse ya fara kissing nata, tun tana mutsu mutsu tana neman kwace kanta, har ta hakura ta natsu tsit a jikin nasa, shi kuwa lafiyayyar kiss yake bata tare da kara matseta a jikinsa, sai faman sauƙe numfashi da sauri sauri yake yi, hankali ya kwanta, abin nema ya samu.

Sun ɗan jima a haka, ta natsu shiru, duk wasu ƙofofi da gaɓɓai na jikinta suna karɓar wannan daddaɗar saƙon da yake aika masu da shi, tuni ya sanya ta fara fita a hanyacinta. Can ta yi nisa bata jin shi sosai, kamar daga sama ta ji sauƙar hannunsa a kirjinta, wani irin bugu kirjinta ya bada, ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi.

Can kasa kasa ta jiyo muryarsa bayan ya zame bakinsa daga nata. "Please kada ki hanani taɓawa, na yi maki alkawari ba zan kai hannuna ciki ba, a iya rigar kawai zan shafasu, bana son ɓacin ranki, idan har baki son na taɓa to na hakura". Allah sarki shi kuma yana ƙoƙarin saka ta farinciki ne dan yana tunanin tana cikin kunci anyi mata auren dole, auren da bata shirya ba, bata san shi ba rana ɗaya kawai aka haɗa auren, ranar da ta fara ganin shi, a ranar ta zama mallakinsa, hakan yasa yake binta a hankali dan ya koya mata son shi, a nasa tunanin fa kenan, abin da bai sani be shi ne, ta jima tana dakon soyayyarsa.

Jin abin da ya ce yasa tayi shiru ta natsu, dan kyautatawa iya kyautatawa yana yi mata, koda yaushe bashi da wata burin da ta wuce ya ganta tana murmushi tana farinciki, dole ita ma ta yi ƙoƙarin sanya shi farinciki.

Kamar yadda ya faɗa hakan ya yi, bai saɓa maganarsa ba, suna daga cikin rigar ya rinƙa matsasu yana wasa da su, ya kankameta sosai a jikinsa, Allah kaɗai yasan me yake ji, shekarunsa 28 to 29 a duniya yanzu.

Sun jima a haka kafin ya saketa ya juya ya nufi toilet ba tare da ya bari sun haɗa ido ba, da alama kunyarta yake ji. Ita kuma, da kyar ta koma saman gado ta kwanta tare da lumshe idanunta tamkar mai yin barci, ban da ajiyar zuciya babu wani abu da take sauƙewa.

After some minutes.

Wanka ya sake yi tare da shiryawa cikin wasu kananan kayan, sai dai a wannan karon ba ita ta fitar mashi da kayan ba, shi ya zo ya fitar da kansa, ita tun da ta kwanta ta kasa sake motsawa.

Bayan ya kammala shirinsa tsab, ya kariso gaban gadon, a hankali ya zauna kusa da ita tare da sanya hannunsa ya fara shafa gashin kanta, da yake kwanciyar da ta yi yasa É—an kwalinta ya zame kasa, gashinta ya bayyana.

"Tashi muje na baki abinci ko matata?". A nutse ya yi maganar, har lokacin taki buÉ—e idanunta, dan bata san da wani ido zata kalle shi ba.

"Yaya Nawid naƙoshi". "Ban yarda ba, kiyi hakuri kin ji? Na san abin da nayi maki ne yasa kika ce haka, to na tuba bazan sake ba, yanzu dai yinwa nake ji, please ki tashi muci ko?".

Shiru ta ɗan yi Mashi kafin ta ce "Yaya Nawid da gaske ba zan iya ci ba, kai kaci kawai". Ɗan kwantowa kaɗan ya yi tare da ranƙwafo da kansa daidai saman tata, har suna iya jiyo numfashin juna. "Idan baki ci ba, wlh nima ba zan ci ba, dan Allah kiyi hakuri, na ce maki ba zan kara ba kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana mai gangaro da hannunsa zuwa saman wuyarta.

"To yaya Nawid ai kunyarka nake ji ne, ni gaskiya ba zan iya buɗe idanuna na kalleka ba" Murmushi ya yi tare da cewa "To tashi kizo, nayi alkawarin ba zan kalleki ba, zan rufe idanuna ko kuma na kawar da kaina a duk lokacin da na kawo maki spoon ɗin abincin bakinki". To ta amsa da shi tare da miƙewa zaune, shima miƙewa ya yi suka sauƙo daga saman gadon zuwa kasa.

Ita ta zuba masu abincin, sai kallonta yake yi, ya kasa cika alkawarin da ya É—auka na ba zai kalleta ba, ita kuma taki yarda ta kalle shi.

Bayan ta gama zuba masu, sai ta zauna a gefensa kamar yadda suka saba zama.

ÆŠaukar spoon ya yi tare da É—ebar abincin ya kai mata saitin bakinta yana mai tsareta da ido.

"Ni yaya Nawid zan ci da kaina". Ba musu ya juya abincin izuwa bakinsa, É—aukar nata spoon É—in ta yi suka fara ci a tare, abin gwanin ban sha'awa da burgewa.

Bayan sun kammalaci, ta miƙe ta kwashe kayan abincin zuwa Palo, lokacin da ta dawo, ta samu yana waya, shiru ta tsaya kusa da shi tana jin muryar macen da ke fitowa daga cikin wayar tasa, wani irin kululun bakin cikine ya turnuke mata maƙoshi, bata bari ya kammala wayar ba ta fusge tare da bin screen ɗin wayar da kallo.

Bata kai ga kallon sunan da ya rubuta ba, sai gani ta yi ya miƙe yana ƙoƙarin kwace wayar, da gudu ta nufi waje bata bari ya kwace wayar ba.

Ba ƙaramin daɗi ya ji ba, ta fara kishin shi, kenan ta fara son shi, dan shi idan baku manta ba, yana ganin kamar dole aka yi mata, kuma hakan ya sa ya zage yake koya mata son shi.

Da sauri ya bi bayanta, a palo ya sameta zaune kusa da Ummi, tamkar ba ita ce ta karɓe mashi waya yanzu ba, kai kallonsa ya yi izuwa kan hannayenta, babu wayar mamaki ne ya kama shi, ko'ina ta kai wayar oho.

"Zo mu tafi ina da magana dake". Ya faÉ—a yana satar kallon Ummi, make kafaÉ—a ta yi alamar ba zata zo ba, kashe mata ido É—aya ya yi tare da É—an karkata mata kai alamar ta yi hakuri ta zo suje.

Gyarawa ta yi ta kwantar da kanta a saman cinyar Ummi tana mai da kallonta izuwa saman Tv da Ummin ke kallo, ba zata zo É—in ba kenan.

"To shikenan bani wayata fita dama zan yi, kiran da ki ka ga anyi mani nan, wata patient a ka kawo a asibiti, abin na gaggawa ne, kuma ni kaɗai ne zan iya dubata, dan haka zan je wata kila na dawo yau, wata kila sai safiyar gobe". Ya kai karshen maganar yana miƙa mata hannunsa akan ta bashi wayar.
Chapter 29 · 0% Book details