← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 121

Sashe 4

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren ita ma Ommun, ɗaura wayar ta yi a saman bedside drawer tana faɗin "Ɗan wahala ba zan dawo ɗin ba, kuɗi ma nake nema da zan je in biya katti su kashe mani kai na samu na ɗauke yarana mu dawo gidan nan na har abada, banza shashasha".

(To fah waye shashasha a cikinsu kenan? Uhm ni dai na yin gaba sai kun zo.)

A ɓangaren Akila kuwa, yau tun safe take zubawa ɓoyayyen masoyinta kuka akan lallai tana son ganin hotonsa, da yake yau bai je school ba, suna manne da waya suna kashe juna da kalaman soyayya, ko palo taki fita bare ayi zancen yin breakfast, ta mance ma kwata kwata da ana cin abinci a duniya, ta narkewa masoyinta tana kashe shi da kalamai yana kasheta da shagwaɓar nan tasa mai rikita zuƙatan masoya.

"My heartbeat dole na yi duk wani abin da kike so, amma dai ban so baki hotona ba, na so ne na kawo maki kaina da kaina har gida ta yadda zaki sami damar ganina da kyau, na yi maki alkawarin duk rintsi duk wuya ba zan wuci daga nan zuwa 1 to 4 months ba zan kawo maki kaina har gida, amma dole zan tura maki hotona yanzu domin ki yi farinciki, but da sharaÉ—i".

Cikin shagwaɓa ta ce "Sharaɗin menene kuma Heartbeat?".

"SharaÉ—in zan sanyawa hoton kala, sannan kuma sau É—aya zaki kalli hoton".

Cike da zumuÉ—i ta ce "Na yarda, ba dai zan ganka ba?". E ya amsa mata da shi tare da cewa "To ki shiga WhatsApp yanzu zaki gani na turo maki, bari na ga action da zaki É—auka mu gani, na yi nasara ne ko na faÉ—in? Ganina ya kori jina ne, ko kuma dai jina ya kori gani na."

Ita dai bata amsa ba, cikin zumuɗi ta shiga cikin WhatsApp ɗin, hannunta har kerma yake yi wajen sauri ta buɗe saƙon da ya shigo mata da ɓoyayyen number.

Ai kuwa tana buɗewa hotonsa ne yana tsaye a gaban wani tapkeken pool mai girma gaske, mai ɗauke da ruwa sky blue, bai sanyawa hoton nasa color kamar yadda ya faɗa ba, ya turo mata ne a ainahin kalar da a ka ɗauki hoton, da alama kuma dama ya gwada ta ne da ya ce zai sanya mata kala a hoton, dogone sosai yana sanye da wandon soja a jikinsa, sai kuma farar T-shirt, ya sanya bakin glass a face nasa, while yana ɗan duƙe da kansa, a shekaru ba zai wuci 22 years ba, yana da ɗan kiba kaɗan, haka zalika yana da faffaɗar kirji, farine tas da shi, yana da gashi a kwance a hannunsa da yake hannun ne kawai ta bayyana, kafarsa na sanye da wasu shegun home sleepers masu balain kyau, launin brown colar, fuskarsa bata fita sosai ba a hoton, sakamakon ya dukar da kansa yana kallon tsadaddiyar wayar dake a hannunsa, da alama irin gayun nan ne masu ɗaukar wanka, domin zaka gane hakan ne daga yana yin irin askin dake a kansa, wani irin askine wadda shi kaɗai ma ya isa ya sanya mata tsayuwa suna kallonsa, ta ko'ina ya haɗu, amma kuma da alama kamar ba farin ɗan Nigeria bane, amma kuma ya akayi yake bala'in mugu mugun jin bushasshiyar hausa haka? Idan ya yi wata karin magana sai ka rantse da Allah a bakinsa akayi Hausa, da alama dai kamar soja ne, domin yanayinsa ya nuna hakan.

Shiru ta zuba mashi ido tana karewa kyakkywar halittarsa kallo, amma kuma a nata ganin ya yi mata mugun kama da gwaggo Batula, harta tsawonsa kusan ita ya É—auko, sannan yanayin hasken fatarsu, kunsan na gaya maku suma hasken fatarsu ba irin hasken nan Nigeria bane, kuma kada ku mance ita dai Hjy Batula kanuri take aure fari tas da shi kamar Balarabe, sannan yana kama da Abla Æ´ar autar Hajiya Batula wadda ta kasance tamkar balarabiya saboda haske, kusan a cikinsu su dukka ma, ita Ablan ta fi su haske, ko da yake ita kaÉ—ai Akila ta sani, bata san saura ba, Abla yarinya ce karama sa'anin su Jehan É—in.

Ta jima tana kallon wannan hoton nasa, domin tabbas ta taɓa ganin exactly wannan fuskar, to a ina? Duk da ma bai ɗago kan nasa sosai ba, amma dai tabbas yana mata kama da mutane da dama da ta sani, ciki kuma harda Abbanta.

(To fa lallai Akila shi kaɗai ne mai kama da mutane da yawa haka? Anya ba kyansa ne ya ruɗa ki ba kuwa? Ke wannan idan da kinga ainahin fuskar Lion or James ko Michael ina ga suma zaki yi saboda ganin tsantsar ainahin kyau, kai Akila akwai son kyau gaskiya oh ni🤔.)

"Heartbeat zuciyata sai bugawa take yi da sauri sauri, please ki gaya mani, shin nayi maki ne ko ban yi maki ba? Wannan dalili yasa nake fargaban tura maki hotona, wlh Heartbeat idan kika ce ban yi maki ba zan iya mutuwa, domin ba ƙaramin kamuwa zuciyata ta yi da sonki ba, dan Allah my heartbeat kada ki ce ban yi maki ba kin ji ko tawan?".

Sai lokacin da ta ji voice nasa ne yasa ta gane cewa ashe bai katse kiran ba, ita ta shagala da kallon hotonsa, ta mance da suna waya baki É—aya.

Yar firgita ta yi kafin ta ce "Gaskiya baka yi mani ba, bana son soja kuma bana sonka domin kai ba irin mazan da nake burin aura bane". Ta kai karshen maganar tare da fita daga kan hoton nasa ta ma fita WhatsApp É—in baki É—aya tana turo baki kamar biro.

Yana daga zaune a bakin katafaren pool daya ɗauki wannan hoton da ya tura mata, ya zura kafafunsa a cikin ruwan yayin da fuskarsa ke sanye da face mask ga uban tulin takardu a saman table a kusa da shi, daga gefe kuma drinks ne da glass cup mai ɗauke da drinks ɗin a ciki, da alama karatu yake yi, hira da ita ne tasa har ya sauƙa daga saman table ɗin ya dawo bakin pool ɗin ba tare da ya lura ba, soyayya daɗi bai ma san time da ya tsunduma kafafunsa a cikin ruwan pool ɗin ba, har sai da ta furta cewa bata son shi ne ya yi wani irin razana wadda ta sanya shi faɗawa cikin pool ɗin ba tare da ya ankara ba, sai dai ya ji shi tsulundum a cikin ruwa.

Ita kuma cikin wasa ta gaya mashi hakan bata san wannan kalma tana ƙoƙarin yin kisan kai ba.

Da kyar ya iya fitowa daga cikin pool É—in tare da mai da wayar a kunnensa da yake waterproof ce wayar ma, akwai waterproof a jikinta sai bata yi komai ba.

Magiya ya fara yi mata har da hawayensa, ita kuma sai murmushi take yi, daga karshe da ta ji yana kuka sosai sai ta bashi hakuri tare da ce mashi ganinsa da jinsa duk É—aya ne, dan haka ta ko'ina ya yi mata, yanzu burinta kawai ya gaya mata yaushe zai zo gareta ya kawo mata kanshi suga juna ido da ido.

Tsabar daÉ—i da murna bai san time da ya ce mata next week yana nan zuwa ba, haba ita ma wani irin tsalle ta yi tare da komawa saman gadon ta baje tana sauke numfashi.

Kasa kasa kamar mai raÉ—a ya ce "Heartbeat kada fa ki yi ki jiwa jikina ciwo, kada ki ragewa halitata quality, dan haka ki bi min kayana a hankali cikin kula idan ba haka ba, wlh yanzu ki ga sojoji a gidanku sun zo sun É—auko mani ke sun kawo mani ke".

Zubur ta miƙe zaune tana faɗin "Dama kai ɗan Nigeria ne? Amma ya na ganka kamar balarabe ko Bature?".

Yana ƙoƙarin cire kayan jikinsa da suka jiƙe ya ce "Meyasa kike tambayar ni ɗan Nigeria ne ko ba ɗan Nigeria ba?".

Cikin zumuÉ—i ta ce "Ai na ji ka ce za'a azo a É—auke ni ne, shi ne abin ya bani mamaki".

Cikin nuna ko in kula ya ce "Yah ni ɗan Nigeria ne kuma Yaya ne ko kani ne ga Imran Shikenan?" Shiru ta yi tana tunanin anya kuwa ba wasa da hankali zai yi mata kamar yadda ya saba canzawa ƙwaƙwalwarta tunani akansa ba kuwa? Kai ba gaskiya bane, shi ba ɗan Nigeria bane, to amma idan ba ɗan Nigeria bane a ina ya san gaba ɗaya familynta? A ina ya iya wannan busashiyar hausa da babu miss ɗin? A ina ya yi mata wannan shegiyar farin sanin? Har size na takalmarta ya sani? Breziya pant dukka ya san size nata kamar wani Aljani, daren jiya da suna hira akan aurensu da kayan lefe, shi ne take gaya mashi size na jallabiyar da take sanyawa, bai bari ta karisa ba ya rigata da gaya mata size na komai da komai nata, tasha ruwan mamaki, amma kuma bai bari ta yi mamakin ba bare ta tuhume shi ko ta tambaye shi, sai ya yi saurin canza topic na maganar zuwa hirar su AKil, kuma sau da dama haka yake yi mata dama, idan baya son gaya mata abu ita kuma ta matsa, to sai ya canza mata topic ɗin maganar ya mantar da ita wancan magana da take son sani.

Ganin ta lula duniyar tunani ne yasa ya ce "Bari na goge maki tan tama akan tabbas ni É—an Nigeria ne, yanzu dai ki shiga WhatsApp bari ki ganni cikin Æ´an uwana".

Ai kuwa da sauri ta shige WhatsApp É—in dan ta ga me kuma zai sake turo mata.

Hotonsa ya sake tura mata kusan irin na É—azun, yana tsakiyar bakaken fata tsundum, dukkansu kuma manyan mutane ne shi ne kaÉ—ai karami a cikinsu, wannan hoto kuma yana sanye da face mask, sai dai kuma ta gane shi É—in ne domin ta yi mashi kallon kurilla a hotonsa na baya, shiru ta yi tana kallon mutanen dake a gefensa, tana son tantance da Æ´an wace State a Nigeria suka yi kama, sai jin muryarsa ta yi yana cewa.
Chapter 4 · 0% Book details