← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 121

Sashe 23

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Areef ya kariso wajen, bawan Allah da yake yana cikin ciwo, sai ya kasa ɓanɓare hannun Lion ɗin daga wuyar tata, yasan idan ya sanya karfi sosai, wajen ciwonsa zata iya fara yin jini kuma, cikin sanyi murya ya ce "Saif! Saif mace ce fa, zaka kasheta, ba zata iya jurewa ba". Abin da ya sanya ya gaya mashi hakan kuma, Lion da bakinsa lokacin suna school, Aseef zai daki wata yarinya ya hana shi, bayan ya dakatar da shi ya ɗaura da cewa, ai duk mai dukan waƴan nan halittu ba namiji bane, "Idan har zata daki mace to da sauranka a mazantaka, kuma kai Aseef idan ka daki wannan abar ai ba zata saura ba, halittun da su da kansu ma suna tafiya suna faɗuwa saboda tsabar rashin quality, to ina ga kuma ka ɗaura hannu a jikinsu? Ai ka daki namiji, ka sanya namiji dakakken gwarzo kuka, shi ne ka cika namiji, amma waƴan nan halittu, ka sanya masu mahaukacin tsoron ka kawai, wadda ganinka kawai ma zai sanyasu suma". A lokacin da Lion ya yi wannan magana, yana ganinyar tashensa ne, ya ce yafi karfin ya daki mace, sai dai ya sanya kartin maza kuka, idan kuma kuka lura yana daga cikin abin da yasa yake dannewa baya dukan Rimsha, amma bata ji tana kure shi.

Ko da Areef ya yi magana, bai zame hannunsa ba har sai da ya ji yana ƙoƙarin yin kisan kai, a cewarsa yarinyar tana kure iya ɗan hakurin da yake da shi ne, rawan kanta ya yi yawa, yana son saita ta da kyau.

Yana saketa ta karisa zama a wajen tana ƙoƙarin sulalewa kasa ta kwanta, da sauri Imran ya kariso ya riƙe mata hannu tare da miƙar da ita suka nufi waje.

Gefen gadon Areef ya zauna yana mai bin ɗan uwan nasa da kallo. "Saif idan ba damuwa, zan so ka rinƙa yi wa yarinyar nan uzuri, kaga karamar yarinya ce, kuma mace ce, ƙwaƙwalwarta karami ne, kasan ko kallonka ta yi wani mahaukacin razana take yi, idan ka ɗaura hannunka a jikinta wlh daga ranar ba zata sake moruwa ba".

Shiru ya yi bai tanka ba, hannu Areef ɗin ya kai ya toshe mashi hanci da karfi yana faɗin "Har dani zaka yi wa walakancin ne?". Tsawon minti ɗaya yana riƙe da numfashinsa kafin ya sanya hannu ya damki hannun ɗan uwan nasa ya janyo shi da karfi, luuuuuuu Areef ya tafi sai saman kirjinansa, waro blue eyes nasa masu ɗauke da barci ya yi akan face ɗin ɗan uwan nasa, ido huɗu suka yi.

Wani irin kallon Saif ya bi shi da shi kafin ya sake shi. "Tashi mashi a jiki" gently ya yi maganar. Kara hayewa jikin nasa Areef ya yi. "Karfi ya ɗaga ni in gani". Lumshe ido ya yi yana jin Bala'in kaunar ƴan uwan nasa. "Areef kana kure ni ko?". "Au haba dai? To shikenan ka ɗauki mataki!". "Okey zan ɗauka ai yanzu dai tashi mani a jiki ka zuba mani abinci, am felling hungry over". Ya yi maganar can kasan maƙoshinsa. "Nifa ba zan tashi ba, karfi ya tashe ni nace". Tamkar abin haɗin baki, suna a haka sai ga kiran Aseef bawan Allah.

Da yake wayar tana a hannun Saif ɗin, sai ya kawota saitin face nasa, ganin Aseef ne yasa ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, shi ma dai Areef ajiyar zuciyar ya sauƙe, bayin Allah nan suna yi wa junansu wani irin mahaukacin kauna ne wadda baki ba zai iya faɗarta ba, duk ɓacin rai ɗin da ɗaya yake ciki, suna ganin juna zasu wastsake.

Areef ne ya sanya hannu ya yi picking call É—in, har lokacin yana kwance a jikin Lion É—in.

Wani irin ƙayatattacen murmushi Aseef ya saki lokacin da ya kalli fuskokinsu dukkansu biyu, da yake video call yake kiransu, bai cika kiransu normal call ba, kwance yake a saman gadonsa yana sanye da kayan barci milk color, ya yi kyau sosai.

Shi ma Areef ƙayatattacen murmushi ya saki, shi kuwa Saif bai yi murmushi ba, amma dai ya ɗan saki wannan ɗaurarriyar fuskar tasa, alamar ya ji daɗi kenan, amma murmushi kam, sam babu ko ɗigonta a fuskarsa.

"Wow My TRIPLETS yau kam wace iriyar Sa'a ce dani,? Naga face naku a haÉ—e waje guda, wlh ina kewarku sosai, ko yaushe na tuno ku sai na yi kuka, shi ma daddy yana kewarku sosai, ni gaskiya zan bar exams É—in nan na biyo ku, ba zan iya zama ba, i can't gaskiya". Ya kai karshen maganar tamkar zai yi masu kuka.

"My shagwaɓati ba, kai Aseef ban san ya zanyi da kai ba, yanzu dai kuka zaka yi mana kenan? To kayi bari na yi recording na ajiye tarihi, gaskiya your future wife tana da aiki, yaron nan har yanzu ba zaka canza ba ko?". Cewar Areef, ya yi maganar cikin zolaya.

"Serious kewarku nake yi, kuma ni mata mai shagwaɓa zan aura ai, ta yi ta kuka nima ina taya ta, jiya ma na haɗu da wata beb a white house, sai dai bata iya shagwaɓa ba, sai wani juya min ido kamar wata tsuntsuwa ta iya".

Dariya Areef ya kwashe da shi, shi kam Saif kamar wasu Tv haka yake binsu da ido, idan suna irin wannan wasan nasu nishaÉ—i suke sanya shi, yana son ya kallesu suna farinciki suna dariya, ga shi shi kuma bai iya dariyar ba bare ya yi masu shi ma.

"Aseef shiyasa fa na ce maka zan É—auko maka mace daga nan Nigeria in kawo maka, matan Nigeria fa the are beautiful wlh, and suna da kirki over, ba kaga Our princess ba Rimsha? Ai tana da kirki sosai, kuma tana da kyau, to irinta zan samo maka".

Ɗan satar kallon Musharraf dake barci a gefensa ya yi kafin ya ce "Idan har Gimbiyar TRIPLETS tana da sister to kawai ka ɗauko mani ita, in dai jinin Uncle Hosain ne, ina so zan aura". Zaro ido Saif ya yi yana jujjuya sunan da suka kira Rimsha da shi, da yake ya san suna kaunar Musharraf, sai ya yi tunanin hakan yasa suke kaunar Rimsha, sai bai kawo komai a ransa ba, bai taɓa kawowa cewa wai Rimsha na haukar son shi ba, dan shi kallon ƴar karamar yarinya yake yi mata, idan ma aka gaya mashi tana son shi ai sai ya sumar da ita, kuma tabbas zai tsaneta, ace yarinya yar karama har ta san soyayya, dududu shekarunta nawa a duniya? Da har zata fara soyayya, ita da ya kamata yanzu ace ta tsaya tsayin daka tana zuba uban karatu kamar ba gobe, amma wai soyayya. TAB LALLAI LION BAI SAN RIMSHA KAM TUN TANA ƳAR SHEKARA 9 TAKE HAUKAR SON SHI BAN, IDAN YA JI TUN WANNAN LOKACIN KUMA SAI YAYA, YANZU MA YA CE KAMAR HAKA BATA KAI SOYAYYA BA, ƳAR JARIRIYA DA ITA........🤣.... TO INA GA KUMA YASAN TA JIMA A CIKIN SOYAYYARSA? TAB AKWAI AIKI.

"Kai Aseef ka kawo good shawara fa, zan tambaya maka Rimsharmu idan tana da sister zan nemota na taho maka da ita, amma kuma sai dai kamar da wuya fa ace tana da sister, domin da uncle ya zo mummynsu kawai ya tambaya, ban ji ya ce ina sister ta ko wani abu makamancin haka ba, amma zan bincika".

Aseef zai yi magana zazzakar murya Lion ya katse su da cewa "Haba Areef ka tashi mani a jiki kada ka karya ni mana, kuma ai na ce maka yunwa nake ji ko?". Cikin sauri Aseef ya ce "Kai Areef ka tashi ka bashi abinci mana, please ka yi sauri, nima har kasa na fara jin yunwa".

Kwafa Areef ya yi. "Ba zan tashi ba karfi ya tashe ni, kuma abinci dai ba za'a ci ba, tun da yau ya shaƙe mani sister ba zai ci abinci a gidan nan ba". Zaro ido waje Aseef ya yi. "Haba mana Lion meyasa zaka shaƙeta? Ai gwara ni kazo ka shaƙeni, ina fa sonta, sister mu ce fa, ƴar uncle ce fa, muna kaunarta ni da Areef, kuma ya kamata kai ma kaso abin da nake so tun da kana so mu, please ka daina shaƙeta ka ji? Saboda ni zaka yi ka ji my pleasure? Our king". Tamkar bai ji su ba, tabbas yasan suna bala'in kaunar Rimsha, dan ya ga irin zaman da suke yi da Areef, ya ga yadda Areef yake bata kulawa ɗazun, abin ma mamaki yake bashi, sai dai shi kuwa bata ma ishe shi kallo ba.

"Areef zan yi maka rashin mutunci fa idan baka tashi mani a jikina ba". Ya faÉ—a gently.

"Areef please stand up mana, ko so kake ka saka ni kuka ne? Ya ce maka yunwa fa yake ji, please ka tashi, dan kaga muna lallaɓaka baka da lafiya ko, to Allah ka tashi ko kuma muyi sama da kai, kuma ai ba zan sake shaƙe sister taka ba, na ari bakin ɗan uwan, na yi magana a madadinsa, dan haka yanzu dai ka tashi maza". Cewar Aseef

Kin tashi ya yi tamkar bai ji me suke faɗe ba, sai da ya kalli Lion ya lumshe idanu alamar ransa ya ɗan ɓaci, dan a gaskiya yana jin yunwa sosai, kuma baya son ya yi wurgi da Areef ɗin ne, dan saboda ciwon dake jikinsa, hakan yasa yake mugun tausaya mashi, amma Areef na neman kai shi bango.

Ganin ya lumshe idanu ne yasa Aseef ya yi mashi alamar ya tashi ya bashi abinci dan Allah, ko da kuma Aseef bai faɗa ba, to ya zama dole shi ma Areef ɗin ya tashin dan kansa, baya son ɓacin ran ɗan uwan nasa.

Miƙewa ya yi tare da dirowa kasa yana faɗin "Ba dan halinku na tashi ba". Har lokacin wayar tana a hannun Saif ne.

Wucewa ya yi zuwa wajen da Rimsha ta ajiye abincin, tare da zama ya fara zuba abincin a plate.
Chapter 23 · 0% Book details