← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 121

Sashe 111

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai rarrashinsa Imran yake yi, amma ina yaki yin shiru, sai ruwan hawaye yake yi bawan Allah, ba zai iya jure rashin Akila ba, ita ɗin ta zame masa wani ɓari na rayuwarsa, ita ce first love ɗinsa,. Sai da Imran ya ce ya yi mishi alkawarin zai shawo mishi kan Abba, duk wuya In Sha Allah Akila matarsa ce, sannan ne ya ɗan hakura ya dai'na ruwan hawaye, ita ma Ammie karfafa mishi gwiwa ta yi a kan kada ya damu, da izinin Allah Akila tasa ce, tun da har ta furta bata son Irfan to kada ya damu zasu shawo kan Abba idan ya dawo, da haka dai suka samu suka lallaɓa shi ya daure ya hakura ɗin.

Imran ya ce su je ya tuka shi zuwa gida, okey ya amsa tare da cewa Imran É—in dan Allah kada ya gayawa su Areef, idan ya gaya musu yasan Lion zai ce sai dai ya rabu da Heartbeat É—in tun da haka ne abin, to dan haka kada ya gaya musu, okey ya amsa mishi da shi, da haka ya yi wa Ammie sallama sai hakuri take bashi suka nufi gida.

Yana komawa bedroom nasa ya wuce ya haye gado saboda tsananin ciwo da kansa yake yi mishi, bai kula kowa ba yau a gidan, yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, sai sauke ajiyar zuciya yake yi cikin barci, shi kuma Areef yana can yana faman bincike a kan case É—in Jehan.

Da misalin karfe 8:30 na dare, bayan sun gama cin abinci, da kyar Rimsha ta ci abinci, nan ma har sai da Areef ya ɓata rai sannan ta yarda ta ci, shi ma dai Aseef ba wani abincin kirki ya ci ba, dan ma dai Imran ya sake kiransa a waya ya kara kwantar mishi da hankali ne yasa ya yarda ya ci abincin, da kuma baya son su Lion su gane yana cikin damuwa, dan Lion ba zai goyi bayansa ba, zai ce akan mace har zai ɗaga hankalinsa, shi bai san so ba, ganin abin banza yake yi mata.

Wanka ta yi ta shirya cikin wani wando da bai karisa kai mata idon sahu na kafarta ba, sai riga mai karamar hannu mai shegen kyau, ɗaura handkerchief ta yi a kanta, ta yi kyau ba karya, sai dai fa kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana cikin matsananciyar damuwa, plat shoe ta sanya a kafarta tare da nufar waje, ban da tunanin jenan babu wani abu da take yi, garden ta nufa dan ta rage wa kanta raɗaɗin abin da take ji, gabaɗaya blue light ne kunne a garden ɗin, saman sofa ta kwanta tana tunane tunane har barci ya yi awon gaba da ita, sai misalin karfe 11 na dare da sanyin ya ratsata ne ta farka, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata, ganin a cikin garden take yasa ta miƙe a tsorace, bata lura da akwai mutun a cikin garden ɗin ba kawai ta nufi cikin gida, sai dai kash Mark ya rufe gabaɗaya kofofin gidan, ga shi bata fito da wayarta ba bare ta kira Areef, ga kofar ko ta yi knocking ba lallai su ji ba, kuma ma tana tsoron yin knocking ɗin dan kada Lion ya tashi daga barci.

Ta jima tsaye a wajen tana tunanin mafita, can ta ɗan ji motsin su Brady, dake ɗaure a kusa da ta wajen pool, a guje ta juya ta koma garden ɗin, saman sofar da ta tashi nan ta koma ta kwanta tare da takure jikinta waje guda, ga sanyi ga kuma tsoro, sai ta takure sosai, ta datse idanunta gam tamkar zata fasa su, jikinta har wani kerma yake yi, duk abin da take yi yana kallonta, dama idan baku manta ba, wajen zamansa kenan da daddare, wani lokaci sai ya kai karfe 2 na dare a wajen, so yanzu ma yana zaune yana aikin latsa waya, da ya gaji sai ya kishingiɗa a saman doguwar sofa dake kusa da shi, sai dai tsawonsa ta fi ta sofar, dan haka sai ya ɗan naɗe kafa, duk wani motsinta yana gani, amma ita bata san da shi a cikin garden ɗin ba, da haka barci ɓarawo ya sake ɗaukarta, ta takure jikinta over.

Can cikin dare misalin karfe 1 sanyi ya sauƙo sosai, sai dai ita kuma ɗumi take ji yana ratsata ba sanyi ba, wani irin daɗin barci take ji abinta, miƙa ta yi da nufin bari ta juya daga yanayin kwanciyar da take, sai ta ji wuyarta na ɗan yi mata zafi, waro idanunta waje ta yi, idanun nata ɗauke suke sosai da barci, still dai a cikin garden ɗin take, yunkurawa ta yi zata miƙe sai ta ji kamar ba jikin sofa ta dafa ba mutun ta dafa, da yake akwai hasken blue light a wajen sai ta kai kallonta in da ta dafa kafin ta ɗago kanta izuwa kansa, yana zaune ya jingina kansa da jikin headboard na sofar, da alama shi ma barci ne ta yi awon gaba da shi. Abin da ya faru, da misalin karfe 12 na dare, sai rawan sanyi take yi, hakwaranta na garuwa da na juna sosai, kasa jure jin sautin hakwaran nata ya yi, suna toshe mishi kunne, hakan yasa ya miƙe tare da dawowa saman sofar da take kwance, sofar ta yi musu kaɗan, dan haka sai ya ɗaga kanta ya ɗaura saman cinyarsa bayan ya zauna kenan, sannan ya cire jacket dake jikinsa ya rufa mata, da yake jacket ɗin nasa yana da girma sai ta rufe ta da kyau, ga kuma kauri jacket ɗin, cigaba da latsa wayarsa ya yi har barci ta yi awon gaba da shi shi ma, to shi ne abin da ya faru, ya yi mata hakan ne kuma a cewarsa yanzu tausayi take bashi saboda irin wahalar rayuwa da ta sha, idan baku manta ba a Abuja ya faɗa, ita ce mutun ta farko da ta fara mashi tausayi a rayuwarsa.

(To mudai je zuwa daga tausayi se me readers?)

Ganin shi ne ba karamin ruwan mamaki ta sha ba, tunani ta fara yi a kan yaushe ya zo garden ɗin kuma? Bata san tun karfe 9 yana wajen ba, kai kallonta saman jacket nasa dake rufe da jikinta ta yi, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, da yake zuciya bata da kashi, sai ta ce yaya Saif yana da kirki, har ta manta abubuwan da suka faru a baya, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake barci cikin kwanciyar hankali, Allah ya yi halitta, kyau iya kyau, tsabar rashin ji irin nata sai ta kai hannu ta shafi kumatunsa, kada ku manta bashi da nauyin barci, tun motsinta na farko da ta yi lokacin da ta yi miƙa tana son juyawa kafin ta farka kenan, to motsin nata ya farkar da shi, sai dai da yake barcin yana kan shi sosai ne sai bai buɗe idanu ba, ya cigaba da lumshe su dan kada barcin ya watse mishi.

Daga ita har shi sai da suka ji wani irin yarrrrr a jikinsu lokacin da ta shafa lallausa kuma kyakkyawar kumatunsa, sai dai ko motsawa bai yi ba, hannunta na kerma saboda rashin ji sai da ta sake kai hannu saman dark black curly hair, shafawa ta yi a hankali har zuwa sajensa, a hankali ta gangaro da hannunta zuwa saman lallausan laɓɓansa, tana ɗaura hannun nata a lips ɗin nasa caraf ya cafke hannun nata ba tare da ya buɗe idanu ba, ba ƙaramin razana ta yi ba, a zafafe ta yi yunkurin sauƙa daga saman sofar ta gudu.

(to ki gudu ki je ina? Ba kin iya neman bala'i ba? Baki jin magana ai sai ki tsaya ayi wace za'ayi)

Riƙe hannun nata da kyau ya yi tare da sauko da kansa sai tin face nata, a hankali ya waro dara daran blue eyes nasa masu ɗauke da barci a saman razananniyar face ɗin tata, datse idanunta ta yi tana addu'ar Allah yasa kada ya ce zai dake ta, Allah yasa ya yafe mata, wai mema ya kai ta ne? Wani ɓangare na zuciyarta ne ya ce mata kyau mana, kyansa ya kai ki taɓa shi,.

"Open your eyes". Ya faɗa a sanyaye, ya yi maganar can kasar maƙoshinsa, da ni da ku dukka mun san idanun nata yake son kallo, suna matukar burgesa, izza ta hana shi ya nuna sun burge shi, dama duk wanda ya kalli sleeping eyes nata dole su burge shi, ga su dara daran farare tas kamar audiga, dole su ɗauki hankali dan idanun duniya ne, bare ma idan ta tsorata ta zarosu ai ba'a magana, zata sanya samari da ƴan mata faɗawa cikin kwata, dole idan ta tsorata ta burge mutun, ko dan kara zarosu da take yi.

Tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tare da waro idanun nata a hankali, kai tsaye sai cikin nasa idon, ita tana bala'in son na shi idon, shi ma yana son nata, ɗan kawar da kallonta ta yi daga cikin kwayar idanun nasa zuwa saman lips nasa da suke red color sosai.............❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*

E47-48💋

Tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tare da waro idanun nata a hankali, kai tsaye sai cikin nasa idon, ita tana bala'in son na shi idon, shi ma yana son nata, ɗan kawar da kallonta ta yi daga cikin kwayar idanun nasa zuwa saman lips nasa da suke red color sosai, ita dai a duniya wannan lallausa kuma kyakkyawan lips ɗin nasa suna bala'in burgeta, ji take yi kamar ta sa hannu ta taɓa, shi kuma ya zubawa idanunta kallo babu ko kyaftawa, kamar mai nazarin wani abin a tattare da ita.
Chapter 111 · 0% Book details