← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 121

Sashe 82

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka ta gaya mata duk abin da ya faru daga A har Z ta feÉ—e mata biri har wutsiya, daga karshe ta É—aura da cewa ita test nata ne ma ya dame ta, yanzu Mr Emmanuel ya ce ba zai sake bata result mai kyau ba, ta shiga uku ya zata yi.

Goge mata hawayen nata ta fara yi tana rarrashinta tare da bata hakuri akan kada ta damu dan ya bata zero, ta barshi da Allah, zai saka mata, idan ta je gida ta kwana sallah ta kai kukanta ga Allah, zai yi mata maganin shi, da kyar ta samu ta rarrasheta ta yi shiru, a yau dai basu fita break ba har a ka dawo class, duk sun yi jugum jugum da su, abin gwanin ban tausayi, Rimsha abin ya shiga jininta sosai, ta san ita ma da wuya idan ba zero zai yi ta bata ba, yau duk wani karatu da aka yi musu, bai wani shiga kansu ba, har lokacin tashi ya yi, Rimsha aka fara zuwa É—auka, tana ganin motarsu ta ce da Anaya ta zo su gaisa da Æ´an uwanta, da murna Anayan ta bita suka je, sai dai ga mamakinsu sai suka ga Mark ne kawai ya zo, ta so ta tambaye shi inasu yaya Areef, amma ba sai na gaya muku ba, kun san halinsa sarai, bata ga fuskar tambaya ba, ko kallon in da take ma bai yi ba, Anaya tana ce mishi good afternoon sir, amma ina ko kallonsu bai yi ba bare su saka ran zai amsa musu.

Ɗan zunguran Rimshar ta yi kasa kasa ta ce "Rimsha a ina kuma kika samo Bature? Ko dai ɗan uwan ki ne? Dama kuna da ƴan uwa turawa ne?". Da yake bata taɓa bata labarin TRIPLETS ba, ita tana da siriri sosai, iya hirar school kawai take yarda su yi ban da na gida, wani lokaci har faɗa Anaya ɗin take yi mata ta ce wato ba zata bata labarin ƴan uwanta bako, sai dai ta yi murmushi ta ce zata bata mana, da haka suke rabuwa. Yanzu ma murmushi ta yi tare da shigewa cikin motar tana faɗin "Idan nazo gobe zan gaya miki, amma dai ba ɗan uwana bane, soja ne mai yi wa su yaya Areef girki". Ɗan sake leƙo shi Anaya ɗin ta yi, har ga Allah ya yi mugun shiga ranta, ta ji tana bala'in son shi, shi kuwa Rimsha na shiga ya kunna motar ya wuce suka bar Anaya tsaye tana ɗaga musu hannu.

Suna fita school ɗin uncle Shitu na danno hancin kan nasa motar, ya zo ɗaukar Anaya, Rimsha hankalinta na kan jakarta tana ɗan duba takardunta, bata gan shi ba, sun yi saɓani.

Uban gudu sosai Mark yake shararawa a kan titin nan, suna mantawa nan a Nigeria suke, ba Washington DC ba ne, Allah ya tsare suka isa gida lafiya lou, yana kashe motar a parking space ta riga shi fitowa ta nufi cikin gida, binta da kallo gateman ya yi, babu kowa a palon kasa, kai tsaye sama ta nufa.

Tana saka kafarta a saman benen shi ma yana sako kafarsa Brady na makale a bayan shi, dan bashi da wajen zama sai ya ɗane bayan Lion ɗin, ya iya tsiya sosai karen nan, baya taɓa yarda ya tafi da kafafunsa in dai ba dole ba, tun yana ɗan jariri Lion ya saba da goya shi a baya, shiyasa da ya girma ma yaki dena hayewa, ko Lion ya ce ya sauƙa ya tafi da kafa sai yaki kamar wani yaro, duk wata tsiya karen nan ya iya shi sanka sanka, da alama garden zasu je, yana ganinta ya diro kasa daga bayan Lion ɗin, kunsan karnika da shegen son shinshina mutun su ji ko daga ina ya fito, kun san su kamshi suke bi.

Ganin ya diro kasa yasa ta fara ja da baya da baya, ko sannu Lion bai ce mishi ba, bata ankara ba sai ji ta yi ta buge mutun ta baya, da sauri ta juya dan ganin waye ne.

Areef ne daga shi sai singlet da three quarter, yau garin ana zafi, rana ta take, kallon Lion dake ta tafiyarsa ko kallon in da suke bai yi ba ya yi, shi kuma Brady duk da Areef ya zo bai dena nufota ba, zuba mishi ido Areef ya yi sai da ya kariso wajen yana ƙoƙarin fara shinshinarta, wani wawan mari Areef ɗin ya kai mishi a kumatunsa, da karfi ya daka haushin da ya sanya Lion da ya yi gaba juyowa dan ya ga me ya same shi.

Kara mishi wani marin Areef ɗin ya yi, cikin harshen turanci ya tambaye shi me Rimsha ta yi mishi da yake takura mata a gidan nan? Ta shiga harkarsa ne? Ko kuma ta taɓa kula shi ne? Sit ya natsu tamkar yaro da aka nitsar ake yi wa faɗa da nasiha mai ratsa jiki, kun san fa suma dabbobi suna jin magana sosai,. Abin ya ɓatawa Lion rai, dan me akan wata Rimsha za'a marin masa Bradynsa, dan haka cikin harshen turanci ya ce da Brady "B fight for your ride!". Yana kai karshen maganar ya fice daga palon abinsa.

Ai kuwa tamkar alluran soja ya yi wa Brady ɗin, nan take ya daka haushi tare da yin tsalle ya haye jikin Areef ɗin ya fara kai mishi yagushi a fuska, ba ji ba gani yake yagushin shi, ƙoƙarin kama hannun nasa Areef ya yi, amma ina yaki yarda ya bada damar yin hakan, daga jikin Areef ɗin ya sake daka tsalle zuwa jikin Rimsha dake tsaye a wajen, ita ma yagushi ya fara kai mata ta ko'ina, yana yi yana daka uban haushi kamar ba gobe, da ganga kuma Lion ya ce mishi hakan, dan yasan Areef ba zai iya kama shi ta sauƙi ba, horon sojoji gare shi, ya horu ba karya, idan baku manta ba na gaya muku mafaɗaci ne na a mutu, kama shi ba abune mai sauki ba, yana da wayo over, dama shi Lion ɗin ne ya ce mishi ya rinƙa jin maganar TRIPLETS nasa, shiyasa yake raga musu, yanzu kuma tun da an ce ya kwaci ƴancinsa ai shikenan.

Sai ihu Rimsha take yi ta zube kasa tana birgima, ganin zai yi mata illah sosai ne yasa Areef ɗin nufarsa a zafafe, ransa a matukar ɓace ya yi ƙoƙarin kama shi, da yake yasan idan ya kama shi ba zai yi mishi da daɗi ba, sai da ya bari ya iso yana ƙoƙarin damko shi, sai ya daka wani uban tsalle ya haye saman kan Areef ɗin ya rufe mishi idanu da gashin jikinsa, kokawa suka fara yi ba kaɗan ba, a tsatsan ɓacin rai Areef ya yi wurgi da shi, ya bugu da jikin bango ya faɗi kasa, wani mahaukacin haushi ya sake dakawa tare da miƙewa ya yi wani girgiza, a guje ya sake mufarsu, Areef bawan Allah ba zai iya faɗa da shi bane saboda ciwon dake kirjinsa, bai gama warkewa ba, shiyasa ma Bradyn ya bashi wahala, baya iya ɗaga hannunsa sosai dan a gefen kafaɗa ne ciwon take, kuma Lion yana sane da hakan ya ce Bradyn ya kwatan wa kansa ƴanci, yasan a yanzu haka Brady zai ji musu ciwo sosai, da dai Areef yana da lafiya ne, da wane kaniyar Brady ya iya taɓasu ma, tuni zai yi wurgi da ɗan banza ko ya murɗe mishi wuya ya mutu kowa ma ya huta da masifarsa.

Yana nufosu da gudu Aseef da ya fito tun ɗazun ya zuba musu idanu ya sha gabansa, shi kuma Areef bama ta su yake yi ba, ya duƙa yana rarrashin Rimsha da Brady ya yagushiwa hannu, fuskarta ya so yagusa da waƴan nan shegun faratun nasa masu tsini, shi ne ta sanya hannunta ta tare face ɗin nata yagushin ya sauƙa a hannun nata, sai jini yake yi, shi ne Areef ya tsugunna yana bata hakuri tare da riƙo hannun nata yana dubawa.

Shi kuma Brady, faɗa suka fara yi da Aseef gadan gadan, sai wani ƙoƙarin yagushin Aseef yake yi, ai kuwa Aseef ya yi wurgi da ɗan banza, da gudu ya sake tashi ta nufo shi, a karo na biyu kuwa, maƙogoronsa Aseef ɗin ya damko, da karfi ya shaƙesa tare da zare mishi ido, cikin harshen turanci dai ya ce mishi "Au ka manta ni na sayo ku kenan? Da ni zaka yi faɗa? Ko Areef da ka jiwa ciwo dan bashi da lafiya ne mara kunyar banza, idan baka rabu da mu ka bar palon nan ba Allah sai na murɗe maka wuya ka mutu mun jefar da banza". Haushi ya daga mishi da karfi, mari shi kuma ya kifa mishi a fuska tare da damko hannayensa dukka biyu ya sake yin wurgi da shi a jikin bango, a wannan karon dai a hankali ya yi haushin, alamar ya jigata kuma ya wahala, ko kallon in da yake Aseef ɗin bai yi ba ya nufi su Areef dake ta faman yi wa Rimsha sannu.

Kusa da ita shi ma ya zo ya tsugunna tare da kamo hannun nata yana mata sannu, sai kuka take yi, shi ma Areef ya sha yagushi a fuska ba karya, miƙar da ita Aseef ya yi a kan suje ya saka mata magani, ba musu ta bi shi, shi kuma Areef ya ɗauka mata jakar school nata, suka karisa hayewa saman suka bar Brady kwance a kasa yana mayar da numfashi, ya wahala, ba karamin buga shi da bango Aseef ya yi ba, dan ma ya yi sa'a Areef ba shi da lafiya ai da murɗe wuyarsa zai yi ya mutu, dan yanzu tun da ya fara takurawa Rimsha Areef ɗin baya son shi, ita kuma abin da bata gane ba, idan ta gansu kada ta gudu, in ta gudu sai sun bita, amma da ta gansu zata zura a guje dan tsoro.
Chapter 82 · 0% Book details