Sashe 49
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin sallamar Areef yasa ya saki vest ɗin nata tare da sakinta, daidai lokacin shi kuma Areef ya kariso wajen, ya sha ruwan mamakin ganinta a jikin Lion ɗin, bai yi tunanin wani abin Lion ɗin ya duba a jikin nata ba, bai ma lura da zip ɗin rigarta a zuge kasa ba, da yake kunsan akwai vest, hakan yasa bai gane ba, amma dai kansa ya ƙulle, ya san dai dole akwai abin da ya kawo ta jikin Lion ɗin, to menene wannan?.
Zama ya yi kusa da ɗan uwan nasa har lokacin bai kau da idanunsa daga kansu ba, ita kuma idanunta a datse har lokacin, shi kuma Lion tun shigowar Areef yake kallon face nata yana nazarin wani abin, yes tabbas akwai abin da yake nazari dan gane da face ɗin nan nata, tabbas ya taɓa kallon mai irin wannan fuska sak a tare da Josephine, to wace ce? Ya tambayi kansa.
"Stand up from my body!" Shi ne abin da ya furta a nutse. Jikinta sai kerma yake yi ta miƙe daga jikin nasa ta sauƙa kasa, har ga Allah ganin sunansa yasa gabaɗaya ya ji wani iri, jikinsa ya yi sanyi, amma yana da bukatar ya tabbatar da tun yaushe aka yi wannan zane dan ya lura kamar ba na yanzu bane, idan zanen ya jima kenan hakan yana nufin dan Allah aka yi shi, idan kuma bai jima ba, akwai dalilin yin ta.
Cike da tsoro da fargaba idanunta a rufe bata lura da Areef ba, ta nufi hanyar fita daga ɗakin, har lokacin jikinta na karma, da kyar take iya taka kafafunta ta riƙe kanta dan kada ta zube kasa.
"Come here". Ya furta tare da dawo da kallonsa a kan Areef. Da kyar ta iya juyowa ta nufo shi tana mai kallon kasa, ta ki yarda ta É—ago kanta bare ma su yi ido huÉ—u.
In da ta saba zama, a nan ta koma ta zauna. "What is your Name?" Ya tambaya yana É—auko wayarsa. GabaÉ—aya ta nemi natsuwarta ta rasa, ta rasa ina zata sanya ranta ta ji daÉ—i, ta rasa me yake yi mata daÉ—i, da kyar murya na rawa ta bashi amsa da "My name is Rimsha". Shi dai Areef sai mamaki yake yi, wai me ya haÉ—a su ne? Ya kasa ganewa fa, a fitar da shi daga duhu.
"Yaushe kika yi wannan zanen? Kuma me yasa kika yi ta?". Yana maganar yana tura saƙo a watarsa zuwa ga Aseef. Cike da tsoro da fargaba, bata san lokacin da ta ce mishi last week ta yi ba, ta rikice ta manta ko yaushe nema ta yi zanen.
Jin ta ambaci last week yasa ya ce ta É—auko mishi chemical da ya zubawa mata a lallen hannunta ranar bari ya zuba ya goge zanen, wani irin mahaukacin razana ta yi tare da sakin kuka mai sauti, ita kaÉ—ai tasan azabar dake tattare da wannan shegiyar chemical É—in, shi dai Areef ya zubawa sarautar Allah idanu kawai yana kare musu kallo, tun da an rasa me fidda shi daga duhu.
Ɗago dara daran blue eyes nasa ya yi tare da sauƙesu a kanta, nan take ta natsu sit tare da haɗiye kukan nata, ta nemi kukan ta rasa, tuni ya gudu, wargi ma ai waje ya samu, ba tare da ya yi magana ba ya mai da kallonsa izuwa saman drawer da chemical ɗin yake ciki, ta gane nufinsa, wato ba zai maimai ta maganarsa ba kenan.
Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi wajen drawer, shi kuma Areef ya sanya hannu bibbiyu ya tallaɓo kumatunsa ta yadda zai ji daɗin mai dasu Tv'nsa kawai, tun da an rasa mai fidda shi duhu.
Ɗauko chemical ɗin ta yi tazo ta miƙa mishi tare da zube gwiwowinta a kasa, karɓa ya yi tare da buɗewa, gently ya ce ta cire rigar tata sannan ta sanya hannu ta tare chemical ɗin ta zuba a kirjin nata da kanta, shi kuma zai zuba mata a hannun, kuka take yi baiwar Allah, hawayen nan wani na bin wani, kara tsananta kermar jikinta ya yi, idanunta tamkar zasu firfito su faɗo kasa, hannayen nata sun kasa tsayawa wajen jan vest ɗin nata zuwa kasa, tsantsar kerma da jikinta yake yi ne, yasa komai nata ya kasa tsayawa waje guda, duk wata zuciya mai imani idan ta ga halin da take a ciki sai ta matsa mata kwallah, amma shi kuma Lion tamkar wani mai zuciyar dutse, ko kaɗan bai ji tausayinta ba.
"Lion wai me yake faruwa ne?". Cewar Areef ya yi maganar yana kamo hannunta dake ta faman kerma ta ɗaura a saman kirjinta ta kasa jan vest ɗin nata kasa, shiru Lion bai tanka mishi ba, riƙota da kyau Areef ɗin ya yi tare da jawota ta dawo kusa da shi, har lokacin kuma kallon ɗan uwan nasa yake yi, ya kasa kawar da kansa yana jiran amsa.
"Sister me yake faruwa? Me ya haÉ—aki da Lion?". Kasa magana ta yi, kuka yaci karfinta Baiwar Allah, hawayen nata ya fara goge mata yana mai kara jawota jikinsa.
Daga ita har shi sai da suka yi wani mahaukacin razana jin tsawar da Lion É—in ya daka musu akan ta bashi hannunta ya zuba mata chemical É—in nan ta zuba a kirjinta, tsabar razana bata san lokacin da ta kankame Areef da hannayenta dukkan biyu ba, ganin ta fita a hayyacinta sosai ne yasa Areef É—in ya rungumota sosai a jikinsa yana É—an bubbuga bayanta.
"Saif me yake faruwa ne? Me ta yi maka?". A karo na biyu ma shiru ya yi bai tanka ba, miƙewa da ita a jikinsa Areef ɗin ya yi, bayan sun miƙe tsaye sai ya saɓata a kafaɗarsa dan ya lura ba zata iya tafiya ba, kuma ya lura muddin bai fitar da ita daga ɗakin nan ba tana iya mutuwa saboda tsabar razana.
Bai ce da su komai ba har suka fice daga ɗakin, ya yi hakan ne kuma dan saboda baya son ja in ja da Areef ɗin, duk abin da zai yi yana yin shi ne da lissafi, baya taɓa yi wa TRIPLETS nasa faɗa ko magana mara daɗi a gaban wani, dan baya son kowa yasan tsakaninsa da ƴan uwansa, ko ranar da ya ce Mark ya sanyata tsalle kwaɗo Areef ya hana, yana sane, abin da yasa bai yi magana a lokacin ba, baya son su Mark su raina TRIPLETS nasa, yana son tamkar yadda kowani securitynsa zasu ji maganarsa, to haka zasu ji maganar TRIPLETS nasa, yasan cewa idan ya yi magana a lokacin Mark zai raina Areef ɗin, zai zama idan Areef ya yi magana ba zai ɗauki maganar da muhimmanci ba, hakan yasa ya yi shiru sai da Areef ɗin ya shigo ɗaki ya same sa ne ya yi mishi faɗa tare da gaya mishi baya son ya rinƙa shiga irin wannan magana, idan ya bawa wani punishment to baya son su rinƙa saka baki, haka kuma ya saba yi musu, daga shi sai su yake yi musu faɗa, ko Imran baya bari yasan tsakaninsa da TRIPLETS nasa, yanzu ma yana jiran Areef ɗin ne ya dawo, kuma ma abin da yasa bai karfafa dole sai ya sanya mata chemical ɗin ba, saboda yasan zanen ba na yanzu bane, rikicewa da shiga ruɗu ne yasa ta ce na yanzu ne, amma a matsayinsa na babban soja ya san tabbas ba na yanzu bane, an jima da yin shi, to shiyasa bai karfafa dole sai ya zuba mata ba, ku kunsan da ya karfafa wane Areef ya karɓeta daga hannunsa, ba'ayi wadda zai iya karɓarta ba, bugu da kari fuskarta, wannan fuska tata ta sanya shi cikin tunani, akwai wani ɓoyayyen sirri a tarrare da face ɗin tata a cewarsa, bai kawo cewa son shi ne yasa ta yi zanen sunan ba, dan a yadda yake ganinta, kallon karamar yarinya yake yi mata, bata san menene ma soyayya ba, kuma kuma masu karatu kunsan a lokacin da ta yi wannan zanen ta yi ne ba dan tana son shi ba, ta yi ne kawai dan yana burgerta, a lokacin bata iya banbance soyayya da burgewa ba.
(Amma kuma da ta tara hannunta da gaske fa zai zuba mata chemical ɗin nan, gaskiya Lion halinsa sai shi, baka gane gabansa bare bayansa🤔)
Kai tsaye ɗakinta Areef ya wuce da ita, zaune ya isko Akila tana aikin latsa waya, ganinsa ɗauke da Rimshar yasa ta miƙe tsaye tana tambayarsa ko lafiya, bai ce da ita komai ba, ya wuce ya kwantar da ita a saman gado tare da zama a gefenta yana kallon yadda jikinta ke uban kerma tamkar mazari.
Gently ya fara magana "Rimsha ya isa haka nan, ki dai'na wannan kukan, yanzu ki tashi ki gaya mini gaskiya me ya faru tsakaninki da Lion? Me ya haɗa ku?". Ta ɗauki tsawon a kallah minti goma kafin ta iya dawo da natsuwarta, da kyar ta tattaro sauran muryar da ya rage mata, cikin shasshekar kuka ta fara magana "Yaya Areef ba zan ɓoye maka ba, dan ya kalli zanen dake a kan kirjina ne ya ce zai zuba mini chemical na goge shi". "Zan iya ganin wani zane ne?" Ya tambaya yana kallon kirjin nata, sai yanzu ya lura da zip ɗin rigarta a zuge kasa, abin ku da Turawa, kwata kwata basu san menene kunya ba a rayuwarsu, Akila kam ta zuba musu idanu kawai tana kare musu kallo.
Da kyar ta iya miƙewa zaune tare da sanya hannu cike da kunya ta ɗanyi kasa da vest ɗin jikinta kaɗan zuwa rabin tudun tula tulan nata, ta nuna mishi zanen, zuba wa zanen idanu ya yi yana karantawa.