Sashe 95
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nauyayyar ajiyar zuciya ga sauke tare da jan dogon numfashi ta sauke a hankali, zuba mata idanuwansa ya yi yana kallon yadda take motswa a hankali tana son farkawa, miƙa ta yi sosai tare da juyawa saura kaɗan ta faɗi kasa ya tareta da hannu ɗaya, bata san cewa ba'a saman bed take ba, saman kujera ne, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata kai tsaye sai cikin idanunsa, da sauri ta mayar da su ta datse gam, dan har gobe tsoron ganin cikin kwayar idanunsa take yi, rufe robar ruwan ya yi tare da juyawa da kyau yana ƙoƙarin kunna motar, ɗaura rubar ruwan ya yi a mazauninsa kafin ya ɗaga nata kujerar nata.
Walkiya da rugugin hadari ne suka fara wanzuwa a sararin samaniya, kunna motar ya yi suka nufi hanyar da suka bi su zo, wani katafaren super market suka nufa, kayan drinks ya saya da su fruits, sai kwai, ita kuma ya ce ta ɗauki abin da take so, kayan sakawa ya ɗauka, wandunan jeans da sauransu, sai wasu high heels guda biyu da ta ɗauka, ganin irin man wanke kansa yasa ta ɗauka mishi har guda biyu, shi kuma bai gani ba, dan bai je wajen ba, idan baku manta ba ta taɓa shiga toilet nasa, bata da mantuwa, bata manta kalar mayukan da ta gani a cikin toilet ɗin ba, da yake duk rabin kayan da muke amfani da su a kasar nan na kasar waje ne, kuma super market ɗin banbane sosai, sai ta sami irin shampoo ɗin nasa, ita ma ta ɗaukawa kanta ɗaya dan ta yi amfani da su ta gani, basu wani kwashi kaya sosai ba, amma sai da ta saki baki jin irin uban kuɗin da aka kira musu zasu biya, batasan mayukan nan da ta ɗauka sune masu uban tsada ba, ga shi har guda uku ta kwasa abinta, tambayarsu ya yi zasu karɓi dollars, e suka amsa mishi da shi, bata key ɗin motar ya yi a kan ta je ta ɗauko kuɗi a ciki mota, har ta nufi waje, kome ya tuna sai ya ce ta dawo, karɓar key ɗin ya yi ya tafi da kansa.
Jim kaɗan ya dawo tana tsaye a wajen, lissafi suka buga mishi ya kirga ya basu, ma'aikatan wajen ne suka kwasa musu kayan zuwa cikin mota, ba ɓata lokaci suka shiga suka bar wajen, suna fita wajen motar Hajiyar daɗi na danno kai ita da Jehan sun zo sayayya, dama idan baku manta ba sun ce zasu zo sayayya, to shi ne suka zo, sun kuma yi babbar saɓani da su Lion, da yake dukkansu bakaƙen glass ne da motar tasu kamar wasu marasa gaskiya, sannan ita Jehan tana gidan baya suna hira da wata yarinya sabuwar zuwa da kuma Adiva, sun baro Maryam a gida, A'isha kuma shiru har yanzu, ba su sake jin ɗuriyarta ba.
Gida Lion ya nufa, amma kafin nan sai da ya tsaya ya sayi jarkar man fetur guda dan su kunna engine, hadari ne sosai ya taso kafin su isa gida, lokacin da suka isa ta sauƙa ta buɗe mishi gate har an fara yayyafin ruwa, yana shigo da motar ruwan saman ta kece kamar da bakin kwarya, tsalle ta buga tare da nufar wajen kwano in da ruwa ke zuba sosai ta tsaya, sai murmushi take yi, sarkin son ruwa, ta manta ma bata kulle gate ɗin ba, zuba mata idanu ya yi yana kallon ikon Allah, yarinya ne kamar wata kifi, sai shegen son shiga ruwa, wannan ma ya ga akwai pool a gidan nasu, idan linƙaya take so to ta shiga mana, amma ita ba haka take so ba, ta fi so ne taga ruwan na zubo mata daga kanta har zuwa kasa, ta yi ta juyi yana zubo mata, ba ƙaramin daɗin hakan take ji ba, har wani garɗi, garɗi barci, barci take ji idan tana cikin ruwan sama.
Sosai ya tsareta da ido, ba ƙaramin burge shi kuma ta yi ba, yadda take juyi a cikin ruwan ba'a magana, kowa ya ganta sai ya sake waigawa ya kallah. Almost 30 mins yana cikin mota ita kuma tana cikin ruwa, da ya ga ruwan ba shi da niyar tsagaitawa ga kuma mattress sun bari a sama da wuya idan bai jike bama, kuma yana son zuwa ya kunna engine dan ya sanya su Maltina a fridge su yi sanyi ya sha, yana jin yunwa, hakan yasa ya buɗe kofar motar kawai ya fito, a rumfar parking space ɗin ya tsaya yana kara kare mata kallo, wato ita fa ko kwana ruwan sama zai yi ita ma zata iya kwana a cikinsa, kwata kwata bata wani tunanin illar hakan, nufar gate ɗin ya yi ruwa na jiƙa shi ya je ya jawo dan ya rufe, jin karar gate ɗin yasa ta juyo ga gate ɗin da sauri, ganin shi ne yake ƙoƙarin rufewa yasa ta nufe shi da sauri ta ma mance da zancen rufewa, hannu tasa da nufi bari ta karɓe shi ta rufewa, bai kula ta ba ya rufe tare da miƙewa, ita ma miƙewa ta yi tana son ta ce mishi ya yi hakuri, tana tsoro dan ta ji an ce baya son kalmar sorry.
Da hannu ya yi mata nuni da ta wuce cikin gida, okey ta amsa tare da juyawa da sauri zata bar waje, tsantsi ne ya ɗebeta ta yi baya ta faɗi kasa, saboda ta juya da sauri dan ta tafi, tiles ɗin kuma akwai ruwa sosai, ga jikinta da ruwa, ga ruwan kuma yana zuba, zaman ƴan bori ta yi a kasan ta kasa miƙewa, da farko kamar ba zai kulata ba zai wuce, sai ya tuna anjuma akwai in da zai je da ita, dole ya tabbatar tana lafiya kafin lokacin, tuna hakan yasa ya juyo ya miƙa mata hannansa a kan ta kama ta miƙe, ba musu ta kama, sai dai ta kasa miƙewa, saboda ba karya ta bugu, zafi take ji, ganin hakan yasa shi ya kama hannunta ya fisgota da karfi ta miƙe tare da faɗawa saman faffaɗar kirjinsa, ga ruwa na zuba kamar ba gobe, ƴar kara ta saki dan kuwa fisgota da ya yin nan ya yi mata zafi, hannunta ya yi mata zafi, sannan kuma mazaunanta da ta bugu suma sun mata zafi, zuba mata idanu ya yi ga sanyin ruwan saman na ratsa shi, wani irin yanayi mai daɗi ya tsinci kansa a ciki, ita kuma sai aikin turo baki take yi tana ƴar kara,
Bin ɗan bakin nata da kallo ya yi, ba ƙaramin kyau lips nata suka yi mishi ba, yadda ruwa ke zuba a kansu, ƙoƙarin raba jikinsa da nata ya yi dan ya je ya zuba mai a engine ya tayar, cikin sauri ta kankame shi tana faɗin "Wlh yaya Saif ba zan iya takawa ba, Allah na bugu sosai". Sak yadda Aseef yake magana idan iya shegensa sun motsa, haka ta yi magana ita ma, tana yi tana turo baki, Aseef ya gama koya mata tsiyar nan tasa, har cikin ransa ya ji wannan magana da ta yi, lumshe idanunsa ya yi yana mai ɗaga kansa sama ruwa yana sauka a saman face ɗin nasa, ɗaga kai ɗin nan da ya yi wannan kashin na wuyar maza nasa ta bayyana, tsabar rashin ji irin nata bata yi tunanin me zai je ya zo ba, sai ta kai hannu ta taɓa ƙashin, ga bala'in tsoronsa kuma kamar zai kasheta, amma sai uban rashinji cike a kanta.
A sukwane ya sauƙo da kan nasa kasa tare da sauke kallonsa a saman face nata, nan take ta yi narai narai da idanu, jikinta ya fara kerma ta fara nadamar hakan da ta yi, kullum sai ta yi laifi take fara danasani, lokacin da zata yi bata danasani har sai ta yi, yama rasa wani irin hukunci zai yi mata, baya son ya taɓa lafiyar jikinta sam, dan anjima da daddare akwai in da zasu je, kuma wannan waje ne mai matukar muhimmanci wadda yasa ran dole zai sami wanda yake nema a wajen, to wani hukunci zai yi mata ta ji ba daɗi sosai ba tare da ya taɓa lafiyarta ba? Ya tambayi kansa.
Tsareta da idanu ya yi, can zuciyarsa ta tuna mishi da abin da ya faru ranar da ya taɓa tula tulanta by mistake, abin ya yi mata ciwo sosai har ta kira Anaya a waya dan ta gaya mata, har kuka sai da ta yi, tuna hakan ne yasa yasa hannun shi ɗaya ya matso da ita jikinsa sosai, har lokacin ruwan saman bai tsagaita ba ko kaɗan, ɗayar hannunsa ya sanya ya gangaro da wuyar rigarta zuwa kasan breast ɗin nata, nan take sunansa ya bayyana, ga shi da ruwa ya jiƙa zanen sai suka kara fitowa ɓaro ɓaro, kankame shi ta yi tana ɓuye kirjin nata a jikinsa, ba zata iya guduwa ba dan ba karya ta bugu, da karfi ya ɗan raba jikinsu tare da sanya hannusa ɗaya ya damki breast ɗin nata gu ɗaya, ihu ta kurma mishi shima sakinta ya yi ba shiri, dan wani irin shock da ya ji, runtse idanunta gam ta yi tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a kalla mata su ma bare taɓawa, ji ta yi kamar ta tsinke shi da mari sai dai ya kasheta idan zai kasheta mugu kawai.
Shi kuma ba zai iya shiga cikin gida ya barta a nan ba, saboda lafiyarta dan fitar da zasu yi, dole haka ya saɓeta a kafaɗarsa tana kuka ya wuce da ita ciki, yau idan ranta ya yi dubu to ya ɓaci, kuka take yi ba kaɗan ba, a tsakiyar palo ya sauketa tare da komawa waje ya fito da fetur ɗin zuwa wajen engine, zubawa ya yi ya tayar sun yi sa'a ba abin da ya sami engine ɗin.