← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 121

Sashe 22

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya Imran ya batun zuwa school fa?" Shafa kanta ya yi. "My Rimsha, na gaya maki babu uban da ya isa ya fitar dake daga cikin gidan nan sai idan shi ya bada dama, fitar ki ba zai yi wu ba har sai ya bar Naija, sun kusa komawa ai, na ji jiya yana magana da daddynsu akan maybe next week su shigo Usa ɗin, amma kafin ya koma ma, idan ya sauƙo yana iya barinki ki koma school, abin da nake so dake yanzu shi ne, ki natsu, ki natsu sosai, ki daina rawan kai, ki daina yi mashi laifi, wlh dannewa yake yi, idan kika bari Saif ya yi maki koda bari ɗaya ne, ina mai tabbatar maki sai kin kurmance, to dan haka ki kara natsuwa, ki bi komai a sannu dan ku rabu lafiya, idan ba haka ba kuma, wlh ina mai tabbatar maki zai iya tafiya dake kasarsu ki je kina yi mashi aiki, kuma babu wanda ya isa ya tinkare shi bare ma har ya yi gigin yi mashi maganar ya yi hakuri ya kyale ki, ko daddynki bai isa ba, idan kuka ce kun shigar da shi kara court, to fa court ɗin gabaɗaya ma zai iya ɗaukowa ya kawo maku gida, dan ku ji daɗin shari'ar da kyau, shiyasa kika ga daddynki bai ja da shi ba, saboda bashi da dukiya da kuma power iya ja da shi, to muda gabaɗaya kasarmu ma take a karkashin su, sufa suke juya mu, kinga kuwa ba mu isa ja da shi ba, to kawai shawarar da zan baki, ki natsu ki bi Saif a hankali ku rabu lafiya, Allah ya rabaku lafiya, tun da ya kusa komawa Alhadulillah zamu ce". Ya kai karshen maganar yana shafa kanta.

Shiru ta yi tana tunanin zalunci irin na Saif, mutun tamkar ba mutun ba? Kamar dutsene a jirjinsa, sai izzar bala'i, ka nuna isa a abin da take mallakinka har ma da wanda yake ba mallakin ka ba, wannan ai zalunci ne.

Ganin ta yi shiru ne yasa Areef ya ce "What are you thinking my sister? What prof told you that make you angry like this?".

Kai kallonta kanshi ta yi, tare da ƙaƙalo murmushi dole tana girgiza mashi kai alamar babu komai, da hannu ya yi mata alama akan ta zo, ba musu ta miƙe ta koma kusa da shi ta zauna.

Hannayenta ya riƙe a cikin nasa, cikin zolaya ya yi magana da harshen tunaranci. "What lion did to you ya sa ki angry haka?".

"Yaya Areef ni ai yaya Saif bai yi mani komai ba, kawai barci nake ji ne". Dawo da kallonsa kan Imran ya yi. "Prof ka koya mani wannan yaren naku, dan gaskiya ba zan yarda ba, kuna cutata da yawa, how zaku yi magana ban ji me kuka ce ba, a maganar taku kuma ka sanya sister ta ta ɓata rai, na tambaya kuma all of you kuna gaya mani ba komai ko?". Dariya ta yi mashi tana mai buga hammar barci.

"Serious Areef ba wani magana muka yi ba, ta ce mani ne tana son komawa school, shi ne na ce mata ta yi hakuri Saif ya kusa komawa, idan ya koma shikenan sai ta koma school É—in". Girgiza kai ya yi, yana mai matukar tausayawa Rimsha, domin kuwa, Lion ba next week zai koma ba, wata aiki ma yake yi a Nigeria, aikin kuma ya shafi Musharraf and gwamnatin Nigeria, albarkacin farincikin da Musharraf yake sanya Aseef yasa Saif kwana biyu da suka wuce ya fara bincike akan tun ainahi menene ya faru da har yarabasu da family'nsa haka, menene ya raba kansu da har yake tunanin family'nsa sun rasu, mutumin kirki kamar haka.

A ka'ida irin ta aikin Lion idan zai yi aiki baya tambayar abun da ya faru, dan yasan kowa kansa kawai ya sani, da wuya mutun ya faɗi gaskiyar komai da ya faru, bare ma kuma idan mutun ya yi laifi, to zai yi kokarin ɓoye laifin nasa ne ya bayyana na abokin faɗar nasa, hakan yasa ma baya tambaya, bincikensa kawai yake yi, da kansa yake gano gaskiyar ko wace ɓangaren, ya kuma yanke hukunci da ta dace da ko wace ɓangaren, ɗazun da yamma da suka zauna da Rimsha, ya so tambayarta went last ta rabu da su mummynta, sai kuma ya fasa, dan ya fuskanci kan Rimsha na rawa sosai, shi kuma baya son mutun haka, ba ya zama inuwa ɗaya da mutun mara natsuwa, idan bata gyara ba 1 day 1 time zai yi wurgi da ita waje kawai kowa ya huta.

Shi Areef ɗin abin da ya sanya ya gane Saif ya fara bincike a kan case ɗin Musharraf ɗin, jiya ne da ya shiga bedroom ɗin na ɗan uwan nasa, a nan ne ya gani cikin laptop nasa, ya sha mamaki shi ne ya fara binciken tun yaushe Lion ɗin ya fara aikin, sai ya ga ma kwana ɗaya ne da ta wuce, ba wani jimawa bane, sai dai kuma Areef ya sa a ransa Lion zai barta ta cigaba da zuwa school, bari dai su samu ya ɗan sauƙo, idan baku manta ba, Lion yana son karatu, yana son yaga kowa yana karatu, baya son jama'a su zauna a cikin duhun jahilci, so da wuya idan zai hanata zuwa school.

Shiru suka yi kowa da abin da yake tunani, suna a haka har Mark ya kammala girki, ya zo ya sanar da Areef ya gama girkin oga, bayan ya gaya masu kuma ya koma kan punishment da Lion ya bashi, yau kwana zai yi a waje, Allah sarki, shima bada son shi bane hakan ta faru, bai so ba, bai ma san ya akayi ya sanya yaji a abincin ba, tun da suke yau shekara almost 10 kenan suna tare, bai taɓa yin kuskure maka mancin haka ba, sai yau, amma Lion bai yi mashi afuwa ba, domin a tsarin Lion babu kuskure sai dai ganganci. TAB DA ALAMA AKWAI ABUBUWA DA DAMA DA ZA'A KAMA LION DA SHI, BAI YARDA AKWAI RAUNI A DUNIYA BA, HAKA BAI YARDA DA KUSKURE BA SAI DAI GANGANCI, BAYA SON YARA BARE SHI YA HAIHU, BAYA SON KALMAR SO, KAI SHI DUK WATA ABIN ARZIKI BAYA SO, A LALLAI DA AKWAI BABBAR RINA A KABA.......🤔

Rimsha dai bata so ba, amma haka ta miƙe ta nufi palon kasa, babu kowa a kitchen ɗin, wanke hannunta ta yi before ta ɗauki abincin.

Kamar yadda ta saba, da sallama ta shigo cikin É—akin, bawan Allah ya yi barci da yunwa, dama barci yake ji tun É—azun, da alama kuma barcin É—aukarsa ta yi ba tare da ya shirya ba, ga wayarsa a hannunsa da alama latsawa yake yi barcin ta zo.

In da ta saba ajiye mashi abincin, a nan ta ajiye mashi, ta juya ta nufi hanyar fita. Har ta kai tsakiyar ɗakin sai kuma ta nuyo dan ta sake kallon shi, nan take ta ji zuciyarta na ingizata akan ta zo ta rufa mashi bargo ta kashe mashi wutar ɗakin, ta kuma zame wayar nan nasa da ya riƙe ta ajiye mashi a saman bedside drawer.

Ai kuwa bata yi wata wata ba, ta tako izuwa gaban gadon, a hankali ta ja mashi wanan katon bargon nasa, da kyar ma ta iya jawo bargon ta rufa mashi zuwa jirjinsa, yau gata ga shi kuma yana barci, amma ta kasa kare mashi kallo, zuciyarta ta karaya, ba zata iya kallon shi ba, idan ta yi hakan kuma ta san zata yi ihu ne, zata firgita sosai, domin rikita mata kwakwalwar yake yi a duk san da ta kalle shi, wani irin kwarjini Allah ya yi mashi.

Bayan ta rufa mashi bargon, a hankali ta duƙa a gabansa, har lokacin taki kallon shi, hannu tasa tana ƙoƙarin zame wayar nasa, kirjinta sai dukan uku uku yake yi.

Wani irin Mahaukaciyar damka ya kaiwa wuyarta, idanunsa a lumshe bai buɗe su ba, bai kawo cewa ita ba ce, a cikin barci kawai ya ji tana zare wayar a hankali hankali daga hannunsa, shineyasa ya kai mata damƙa, sai kuma ya yi Sa'a ya capki siririn wuyar nan nata.

Tsabar razana bata san time da ta kurma ihu ba, ai kuwa rige rige Imran da Areef suka yi wajen shigowa ɗakin, har lokacin bai saki wuyar tata ba, ganin hakan yasa Areef ya gane abin da ya faru, Rimsha bata san cewa Lion bashi da nauyin barci ko kaɗan ba, zai iya yana barci kuna hira a palo ma yana jinku sama sama, haka yake, baya da nauyin barci, kuma a yadda ta zo zame wayar tasa, ta yi mashi abu kamar ɓarawo, a hankali take zameta, wai dan kada ta tashe shi, shi kuma ya damketa, a yanzu dai ko bai buɗe idanunsa ba, ya san wuyar waye ya damƙa, tun lokacin ma da ya damka ɗin, ya ji wuyar ɗan siriri, bata ma kai kaurin singalalalin hannunsa wajen ɗaura agogo ba, tun da ya ji haka ta gane wuyar kanwar Imran ce, sai dai kuma bai sake ta ba, dan a ganin shi ta raina shi ne, a kan me zata ta taɓa mashi waya ko wani abu nashi, shiyasa ya kara shaƙe ta yana da ga kwance, idanu a rufe kamar mai barci, dama ga yunwa yana ji.
Chapter 22 · 0% Book details