Sashe 47
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Yanzu cin amanar taku har ta kai ranar kwanana ku tsaya a palo kuna iskancinku ta yadda ma zan gani kenan ko? Wato na zo na gani da kyau kunci amanata ko? To Allah ya isa kuma sai Allah ya saka mini, ke kuma Halima ki jira ki gani, bakar munafuka, ai kinsan yau a É—akina yake, shegiya kullun kina wani sunnar da kai kamar ta Allah ashe Musa ne baki fir'auna a zuci ko? Bakar azzaluma algunguma kullum cikin faÉ—ar Allah ya ce Annabi ya ce kike, amma baki amfani da abin da kike faÉ—a, yanzu idan da ke malamar Allah da Annabi ce ai da ko kallon shi kin san haramun ne a wajenki yau kam tun da a É—akina yake, mayya kin bi kin cinye mini kurwar miji, ya tattare ya tare a wajenki, to wlh ta Allah ba taki ba, ki gama tsafinki da asirinki duk haka zaki ganni ni Deeje ki barni, na fi karfin yarinya sai dai Uwar yarinya, wlh idan......" Bata kai karshen maganar ganin zata tara musu jama'a yasa Abbi ya daka mata wata uwar tsawa mai firgitarwa.
"Hadiza kina shan giyar wake ne? Kanki ɗaya ne ko akwai motsi a ciki? Kin san me kike faɗa kuwa? Kin san me kike yi kuwa? To idan ma kanki ba ɗaya ba ni zan dawo miki da shi ɗaya yanzun nan, ki sani ba zan iya wannan halin naki ba, kuma Halima ba zan iya raba makwanci da ita har na rinƙa raba muku kwana ba, kin manta shekaru nawa kika sa kafa kika yi fatali da aurenki kika bar gidan nan ne? To a wancan lokacin baki san da hakkin nawa ba kenan ko?, A wancan lokaci baki san da raba kwana zai zo ba kenan sai yanzu ko?, Ko dama kina tunanin zan yi ta zaman jiranki ne?, Idan haka kike tunani to kin tabbata mai ƙwaƙwalwar kifi, kinje kin yi ta yawace yawacenki na tsawon shekaru kin dawo, ban ce miki komai ba, na ɗaga miki kafa saboda albarkacin ƴaƴan dake a tsakaninmu, yanzu kin dawo kina son sake ɗaga mini hankali ki takurawa matata farincikina ko? To ina son ki sani ba zan iya rabuwa daidai da kwana ɗaya da matata mai sona domin Allah ba, Halima ita ce farincikina dan haka ki je na sake ki saki ɗaya". Ya yi maganar cikin faɗa da zafin zuciya, ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun Aunty suka nufi saman benen.
Ta gefenta suka raɓa suka wuce, mamaki ne ko tsoro waya san mata, ta dai kasa magana, sai binsu da idanu take yi, jin abin take yi tamkar a mafarki, ita yau Abbi ya saka, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, ta furta a cikin ranta tare da juyawa jiki a mace ta koma cikin bedroom nata zuciyarta cike taf da tunanin mafita.
Shi kuwa Abbi yana shiga bedroom nasa toilet nufa dan ya yi wannan, duk zafin rai da ɓacin ran da Ommu ta sanya mishi a Palo, yana shigowa cikin ɗakinsa ya ji sanyi a zuciyarsa, Aunty ta gyara mishi ko'ina, sai tashin wani fitinannen daddaɗar kamshin air freshener ɗakin yake yi, ga wani daddaɗar sanyin Ac dake gudu a tsaka tsakiya, daddaɗar sanyin Ac da ni'imantaccen kamshi idan suka haɗu ya kuke tunanin abin zai kasance? Ai abin sai wanda ya ji.
Nan take ya nemi ɓacin ran nasa ya rasa, wani muguwar soyayyar Aunty ce ta karu mishi a cikin zuciyarsa, sai albarka ya ke zuba mata a cikin zuciya, da haka ya shiga cikin toilet, ita kuma ta hau fitar mishi da kayan sakawa, Baiwar Allah har ciwo kanta ya fara yi mata saboda hayaniyar da Ommu ta yi yanzu, da Ommu ta fara bala'in, ta yi ƙoƙarin guduwa ta haye sama, Abbin ne ya riƙeta ya dakatar da ita, dan yana son ta rinƙa rage tsoron nan nata, ta cika shiru shiru da bala'in tsoro, shiyasa duk wanda ya ɗebo rashin mutumcinsa sai ya sauƙe a kanta, to yana da kyau ta koyi faɗa ko kaɗan ne, dan ta rinƙa kwatarwa da kanta ƴanci, shiga ɗaki tana kuka ba shi ne mafita ba, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce idan aka yi maka abu ka ji ba zaka iya hakuri ba, ka rama daidai da abin da aka yi maka, kada ka kuskura ka kara koda kwayar zarrace a kan abin da aka yi maka ɗin, daidai zaka rama, wannan shi ne ka'ida ta musulci, amma idan zaka iya yafewa, to yafiyar dai tafi, zaka sami Rahmar Ubangiji, Allah kasa mu a cikinta.
A ɓangaren Ayla kuwa, tana fita wajen mijinta ta nufa, lokacin yana wanka, kai tsaye wajen drawer kayansa ta nufa, kananan kaya ta fitar mishi da su, da yake ba wani iya aikin kirki ta yi ba, sai gyaran ɗakin nata bai yi kyau sosai ba, amma ta yi ƙoƙari, ta shinfiɗa musu gado ta yi shara iya yadda ta iya, kada ku mance irin rayuwar da ta taso a ciki, bata zauna a gida ba bare ta koyi wani aiki, iya abin da ta koya a gidan su Kausar sai kuma wadda Aunty ke ɗan koya mata a yanzu shi kaɗai ta iya.
A saman gado ta ɗaura mishi kayan, ita ma ta zauna a gefen kayan tana jiran fitowarsa,. Yana fitowa da kyakkyawar fuskarta ya fara tozali, cool murmushi ya sakar mata kafin ya buɗe mata hannayensa akan ta zo, da sauri ta miƙe ta nufe shi, rungumeta ya yi sosai suna sakin Murmushi a tare. "Nayi kewarki sosai my baby". Ya faɗa kasa kasa.
"Daddy nima nayi kewarka, har ciwo sai da kaina fa ya yi dan baka dawo da wuri ba". Ta yi maganar a shagwaɓe. "Subhanallah ciwo kuma?" Ya tambaya yana ɗago haɓarta, gyaɗa mishi kai ta yi alamar e. "Ayya Sorry ba zan sake tafiya wani waje mai nisa na barki ba, idan zan tafi to kafata kafarki, idan ba haka ba, na fasa zuwa". Murmushi ta sakar mishi tare da kara lafewa a jikinsa, tana jin daɗin wannan damshin ruwan jikin nasa dake taɓata, ya lura da hakan, cikin sauri ya sake ɗago haɓarta suna kallon juna, tabbas idan ya canka daidai ciki gareta, dan ga alamominsa dukka sun bayyana a tattare da ita, wani irin mummunar faɗuwar gaba ya ji lokacin da ya tuna menene silar mutuwar mummyn jelly, Haihuwa, haihuwa ta zo yi Allah ya karɓi kayansa, kwata kwata ma ya mance da zancen kamanni dake tsakaninta da mummy'n Jelly ɗin, shi dai murna ya fara yi ya samu abin da yake so.
Sakinta ya yi tare da nufar gaban mirror, cikin sauri ya shirya tare da yi wa Allah sujudur shukur, sai bin shi da idanu take yi, bayan ya kammala ya zo ya runhumeta sosai a jikinsa yana zuba mata godiya da sambatun me take so ya yi mata, mamaki ne ya kamata, me yake faruwa ne kuma? Ta tambayi kanta.
Zaunar da ita a bakin gado ya yi tare da riƙo hannunta, cike da so da Kauna ya fara magana. "Babyn daddy kina jina ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e "Nine auta a wajen mamana, bayan ni babu wasu, mamana tana sona fiye da tunaninki, amma a haka ta barni tana kuka ta tafi, ba ma wannan ba nake son gaya miki, kinga ni bani da kani kuma Allah bai bani yara da yawa ba, jelly kawai gareni, zan so ki haifa mini yara dozen da zan rinƙa kallah ina jin daɗi, ina rage zafin kewar mamata". Ya yi maganar idanunsa cike tab da kwallah.
Da yake yarinya ce sai bata hango tsantsar ciwo dake cikin rayuwarsa ba, bata hango irin bakin cikin da yake ciki ba, ta É—auka kawai irin kwallan da ya saba yi ne, bata san wannan kwallah mafi azaba bane a gare shi ba.