← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 121

Sashe 2

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan addu'a kuma da zaka karanta domin samun kariya daga matsafa, tsafi, sharri da komai da komai ba wani mai wahala bane face (Suratul Ikhlaash) kulhuwallahu ahad kafa uku, Suratul Naas kafa uku, sai Suratul Falaq kafa uku, sannan ku rufe da Ayatul kursiyu kafa É—aya, kowani bayan Sallar farillah idan kayi, in ma azahar ne ko la'asar, mangariba or isha'i au asuba'i fatan mun gane?.

MACE MAI CIKI, WANNAN MAGANI NE DAGA MANZON ALLAH SALLAHU ALAIHI WASALLAMA WADDA NANA MARYAM MAHAIFIYAR ANNABI ISA ALLAH YA CE TA YI AMFANI DA SHI DAN SAMUN HAIHUWA CIKIN SAUƘI, IDAN KINA DA CIKI, CIKIN NAKI YA KAI WATA BAKWAI, TO KI LIZINCI CIN DABINO A KULLUN, IDAN DA SON SAMU ME KI CI GUDA BAKWAI KO WANI SAFIYA KAFIN KI CI KOMAI, DA IZININ ALLAH ZAKI HAIHU BA TARE DA WATA WAHALA BA, BA ZAKI SHA WAHALA BA, ALLAH KUMA ZAI BAWA KE DA ABIN DA ZAKI HAIFA LAFIYA DA IZINSA, ANNABI YA BAWA MATA DA DAMA WANNAN MAGANI, DAN HAKA A CIKIN ILIMIN DA ALLAH YA BANI NIMA NA BAKU ƊAYA DAGA CIKI, IDAN KIN JI DAƊI KI YI MANI ADDU'A DA FATAN ALKHARI TARE DA FATAN NASARA A RAYUWATA DA IYAYENA, INA GODIYA. IN SHA ALLAH MAGUNGUNAR MUSULUNCI IRIN HAKA ZAN RINƘA SAƘO MAKU SHI IYA ILIMIN DA ALLAH YA BANI, DAN KUMA KU KARU, IDAN KINA DA WATA TAMBAYA KI YI MANI ITA KAI TSAYE, KADA KI JE KINA TAMBAYAR WATA, NI NA RUBUTA MAGANIN, NI ZAKI TAMBAYA, ALLAH YA BA MU DACE WA. 09262620621 Shine numberta Ma'assalam.✍️

Story

RIMSHA

Wani irin barci ne mai shegen daɗi ya kwasheta, sakamakon samun natsuwa da ta yi saboda addu'ar da ta rinƙa yi tare da ambatar sunayen Allah. Baiwar Allah a cikin barcinma sai sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya take yi, yau ta ga karfin addu'a iya ganin idonta, domin kuwa ba dan addu'a da ta rinƙa yi ba, to wlh da sai dai a ɗauki gawarta yadda yau ta yi mashi laifi sosai ɗin nan.

A ɓangaren su Jelly kuwa, wato gidan Abbi, zaune suke a palon kasa ita da Hanan, yayin da ita kuma Aunty take faman shirya abinci a saman table, Ayla kuwa tana wajen mijinta domin jiya ta ci bakar wuya a hannunsa, wadda ya ja mata zazzaɓi mai zafi, hakan yasa bai bari ta fito ba, ya zaunar da ita yana jinyar kayarsa.

Sai kallo suke yi, ɗan kwana biyun da jelly ta yi har ta koyawa Hanan kallo, jelly shugaba ce a iya kallon Film, ta kware sosai da sosai, duk wasu Indian music ta iya su sanka sanka, ga shegen son rawa kamar wata jikar Michael Jackson, kuma ta iya rawar sosai, sannan kuma bata da ƙiba ne yasa bata jin hauyin jikin tata take takawa son ranta, tana bawa jikinta a jikinsa shi ma.

A haka Hjy Batula ta shigo palon ta same su, ta yi wanka ta ci wani haɗaɗɗe kuma tsadadden lace black color, ɗinkin bubu gown, da yake dai gaba ɗaya familyn su daddy kyawawane tamkar wasu turawa or larabawa, haka suke, kuma gidansu two colors ne, akwai farare tas kamar turawa, sannan akwai chocolate color, Abba dai farine tas haka ita ka Hjy Umaiya, amma kuma Imran chocolate color ne irin Rimsha, to haka a gidan Abbi ma, Aafia da Irfan chocolate colors ne, saɓanin Umaisha da take fara tas Kamar ka taɓa ta jini ya fito, kun ga ita ma JEHAN fara ce tas kamar daddynsu, while shi kuma daddyn jelly bai yi tas ɗin ba dai, amma kuma ba chocolate color bane, shi irin farin Nigeria ne, su kuma farin waje ne da su gaskiya, da alama a cikin kakanninsu akwai Bature ko kuma balarabe, ɗaya dai daga ciki, domin kuwa wannan hasken nasu ba na nan bane, na can ne.

Sosai Hjy Batula ta fito reras abinta, saman sofar kusa da su ta zo ta zauna tana faÉ—in "Ke Jalila ina É—an kwalinki?".

Turo bakin nan ta yi kamar biro zata yi magana kenan Ommu ta sauƙo kasa tana surfa uwar masifa akan su rage Volume na Tv ko kuma ta kashe Tv gaba ɗaya.

Hanan dai da yake ta san halin ta, sai ta ɗauki remote ta rege Volume ɗin, ko sannu jelly bata ce mata ba, suka cigaba da yin kallonsu, yayin da ita kuma Ommu ta juya ta koma sama dan ta cigaba da abin da take yi, yau ta yi nasarar samun number Umaisha ta hannun Hjy Turai da ta karɓa mata daga wajen Aafia, murna a wajenta ba'a magana, tuni ta kyankyasawa Umaisha abin da take buƙata, da yake uwa da ƴa, kuma babba kam ko yaya babba ne, sai bata sha wahala wajen shawo kan Umaisha ɗin ba, karya ta zuba mata akan cewa ai bata da lafiya ne, tana da ciwo a zuciyarta, aiki za'ayi mata a kasar India, Abbi kuma ya ce ba zai biya kuɗin ba, tun da mijinta yana da kuɗi, idan ba damuwa ko sata ne ta sato mata wajen shi, tun da ba zai rasa ajiye kuɗi a gida ba, ko da bai cika 10 million ɗin lokaci guda ba, ta sato da kaɗan da kaɗan, kada ta yarda ta bari ya gane, da farko Umaisha ta ce a'a zata tambaye shi dan tasan ba zai hana ta ba, yana da kyauta sosai, kuma wa su ma a waje ya yi masu bare ita da take mahaifiyarta, ba zai taɓa hana ta ba, sai dai ma ya ce ta shirya su tafi asibitin a tare, da yake ba wani asibitin da zata je karya ce kawai, sai ta sawa Umaisha ɗin kukan munafurci tana faɗin "Ta ya za'ayi ki bari surukina ya san sirri na? Yanzu so kike ki tonawa Abbinki asirin na yaki biya mani kuɗi a kaini asibiti? Wannan ai abin kunya ne, me yasa ke kam wayuya ce? Ai ba'a gayawa miji sirrin gidan iyaye, domin watara sai ya yi maki gori".

Kafe wa Umaisha ta yi akan lallai yaya Akil ba zai yi mata gori ba, saboda ai Abbin babbansa ne, nan fa Ommu ta rinƙa yi mata bayani akan ko uwa ɗaya uba ɗaya kuke da mutun ma, wata rana sai ya yi maka gori, dan haka ta daina wani zancen ba zai yi mata gori ba.

To da yake kunsan yadda ƙwaƙwalwar ta Umaisha take, Baiwar Allah ko nonon uwa bata samu damar wani sha ba, ga wahala da ta sha na tasowa a hannun maza da suka reneta, wato Irfan da Abbi, kun san dai renon Namiji da mace daban daban, hakan yasa Ommu ta yi wasa da tunaninta, tare da gwada mata ainahin bariki har sai da ta yarda ta amince zata sato mata kuɗin Akil ɗin idan za su zo gida. BABBAR MAGANA. Kuna ganin Umaisha zata ɗauki kuɗin Akil ba tare da ya sani bane? Kuɗi kuma ba kaɗan ba, lallai ba shakka Ommu tana son kai Umaisha ta baro ta. Mu dai je zuwa.

Ommu kuwa abin da ya sanya bata son Akil ɗin ya sani, saboda a baya ta yi zama da Hjy Umaiya ai, ta san Ammie akwai shegen bala'in basira sosai da sosai, ga zafin rai da faɗa, sai dai sai an taɓa ta take faɗar tata, to tana da tabbacin da wuya idan su Akil ba su ga ji wannan basira ta Ammie ba, ta san tsab zai ce ta shirya su tafi asibitin ko kuma ya gane karya take yi, shiyasa ta fito da hanyar sanya Umaisha ɗin sato mata kuɗin kawai, a nata tunanin da wawtarta ta hakane kawai zata sami biyar bukatarta.

Lallai da akwai kura kenan, tab É—i jam.

Bayan Aunty ta gama shirya masu abincin ne ta zo ta zauna kusa da Jelly tana faÉ—in "Jellynmu ba karamin kyau kunshin nan ya yi maki ba". Murmushi ta yi tana faÉ—in "Aunty da gaske na yi kyau?" "E mana my baby jelly sosai ma kuwa".

Jelly zata yi magana kawai a ka sako wakar Sharukhan Kuci kuci hotaye, haba malam ai tuni ta miƙe tare da ɗaukar remote ta kure Volume na Tv tare da jawo hannun Hanan akan su taka tare, kwata kwata bata jin daɗin yin rawa ita kaɗai, ta fi son su taka a tare da wani, abin ya fi bada armashi, lokacin da suke Kano da daddy, idan aka sako waƙa a Tv, haka take saka bawan Allah nan rawan dole ba dan ya so ba, kawai dai dan ya rinƙa ganin farinciki akan fuskar ƴar tasa saboda maraicin ta.

Ai kuwa Hanan ma ba son rawar take yi ba, amma saboda bala'i irin na Jelly sai da ta sanya ta rawa, Hjy Batula kam waya ta É—auka ta kama yi mata video dan tana bala'in Kaunar Jelly fiye da tunanin mai tunani.

Sai wani juyi jelly ke yi kamar yadda maciji yake irin wannan nannaÉ—uwa idan zai hau itace, sai ka rantse da Allah bata da kashi a jikinta, saboda yadda take murÉ—e jikin nata, wannan idan ba'a san asalinta ba, da sai a ce kanwa ce ko kuma jika ce ga Michael Jackson, saboda iya rawa.

Suna tsaka da rawa sai ji suka yi an kashe Tvn, a fusashe ta juyo dan gani wani É—an uban ne ya yi hakan.

Ai kuwa ido huɗu suka yi da Ommu dake tsaye tana yi mata kallon sama da kasa, wani irin kallon banza Jelly ta yi mata kafin ta ce "Ke mai kama da pig na discovery me haɗin ki damu da zaki kashe mana kallon mu? Shin mun haɗa wani alaƙa dake ne?".

A fusace Ommu ta nufeta da nufin ta daketa, ai kuwa jelly na tsaye dan dai idan ba ku mance ba, bata da tsoro ga kuma uban rashin kunya tare da tsiwa.

Sai da ta bari Ommu ta iso zata daketa, ta gama sake jiki zata kai mata duka ai kuwa da iya karfinta ta sa kafa ta gale kafar Ommu, sai ga Ommu ta zube a kasa, a lokacin kuma dama Hjy Batula ta miƙe zata tare faɗar, zata tare kada a daki Jelly ɗin.
Chapter 2 · 0% Book details