← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 121

Sashe 100

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba zaki gaya mini gaskiya ba?" Zazzaƙar muryarsa ya sake dakan dodan kunnenta. Ɗan ɗago kai ta yi tana kallon sarkar dake kirjinsa, ɗayar hannunsa riƙe da hotunan da ya kwaso a ɗakin mum, ɗayan kuma riƙe da cardboard paper zanen, haɗe cardboard paper da hotunan ya yi a hannu guda ya riƙe, ya sanya ɗayar hannun nasa ya ruƙo sarkar dake wuyarta yana ganin chain ɗin, ya kusa yin kama da nasu, amma kamar yadda Aseef ya gaya mata da akwai banbanci sosai haka ne, nata round ne nasu Heart, nata akwai mix nasu zallar zinari ne.

Sake sarkar ya yi tare da ɗago haɓarta suna fuskantar juna, runtse idanunta ta yi gam, "Zaki bani amsa ne ko sai na karya ki?" Yana magana yana karewa face nata kallo, a hankali ta motsa laɓɓanta ta furta "Wlh yaya Saif ni ban san ya akayi ba, kawai dai idan na zauna ina tunanin yadda kyanka zai iya kasancewa ne a zahiri, shi ne yasa nake zanawa, bayan haka wlh babu wani abin dana sani, please kada ka dakeni, zan ƙona dukka zanen in baka so". Shiru ya zubawa lips nata idanu, yana kallon yadda take motsasu har ta kai ƙarshen maganar nata. "Ya za'ayi ki zanani tsab yadda nake a zahiri harta yawan sajen dake fuskata sai da kika zana kuma kice a iya tunani kika sanni?". Ya yi maganar tare da kara rage tsawonsa, ya ɗan kara rankwafowa kanta kaɗan.

"Wlh yaya Saif iya gaskiya kenan na gaya maka, bayan haka babu wani abin, kuma duk wanda zai gaya maka wani abu bayan haka to karya ce, ni kai'na idan na gaya maka wani abu bayan haka to wlh karya nayi maka". "Open your eyes". Ya faɗa a sanyaye can kasa kasa, ba musu ta waro dara daran sleeping eyes ɗin nata, kai tsaye sai cikin idanunsa, da sauri ta kawar da kallonta zuwa saman faffaɗar kirjinsa, sakin haɓar tata ya yi yana mai buɗe zanen ya sake gani, har lokacin suna nan daf da juna kamar zata shige jikinsa.

Zubawa zanen face nata dake jikin paper idanu ya yi, ita kanta sak kanta ta zana, harta sleeping eyes nata bata bari ba, tun daga jiya zuwa yau da ya kare mata kallo, babu wani abin da yake mishi kyau a tattare da ita sama da wannan idanun nata, suna da bala'in kyau over, gasu farare tas, sun yi mishi kyau sosai har ya ji yana son ajiye hotonsu a wayarsa, sai dai bai nuna hakan a fili ba.

Ɗan baya ya ja yana ƙoƙarin barin wajen zazzakar muryarta ta katse shi da cewa "Yaya Saif in kona zanen dukka?". Juyowa ya yi da kallonsa a kanta "Time da kika zana kin gaya mini ne?". Girgiza kai ta yi tana kallo ta bayansa, Malika ce ta bayyana a wajen, kara zaro dara daran fararen sleeping natan nan ta yi, hakan ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, tana mamaki ne na ganin Malika, shi kuma hakan ya yi mishi kyau sosai dan kuwa ya karawa idanun nata kyau, juyawa ya yi ya bar wajen ya nufi waje, da sauri ta bi bayansa dan ba zata biyewa Malika ba wasu karti su zo su kamata, murmushi Malika ta yi, dan bata ga laifinta ba, irin yadda ake farautar rayuwar nan nata ai dole ta rinƙa binshi duk in da zai je, idan ba haka ba ta jita a in da ba'a dawowa.

Cikin trolleynsa ya je ya sanya hotunan da kuma zanen nata, kafin ya zauna a gefen bed nasa ya kira daddynsa a waya, lokacin da ta shigo yana waya da daddy, "Jeki ki kawo mini fruits". Ya faÉ—a tare da cigaba da magana da daddyn nasa. "Kai da waye Romeo? Na ji kamar mace ka ambata". Cewar daddyn, kai tsaye ya ce mishi "Ni da sister su Aseef ne". (Wato shi ba sister shi bace kenan? Kai Romeo duniya ne wlh).

"Who is Aseef?" Da yake idan baku manta ba shi daddy bai san sun musulunta ba, so bai san Michael ya koma Aseef, James ya koma Areef ba, "Daddy what is your business about them?" Ya faɗa yana ƙoƙarin jawo laptop nasa dake ɗan nesa da shi.

Ba karamin ruwan mamaki daddy ya sha ba, baki ba zai iya misilta irin mamakin da daddyn ya sha ba, yau Romeo ne inuwa ɗaya da mace? Kai anya kuwa yaransa ne kuwa? Dole ya zo Nigeria dan ya tabbatar ba wani abin aka yi musu suka canza ba, ranar ya kira waya mace ta ɗauka, yanzu kuma ya ji yana cewa mace ta kawo mishi fruits, to ko dai ɗan nasa ya fara neman mata ne? Ya tambayi kansa. Cikin sauri ɗaƴar ɓangare na zuciyar tasa ta bashi amsa da ina, Romeo ba shi da lokacin duk wata mace a duniya, akwai dai wani abin a kasa, ya kira Michael zai sami amsa, idan baku manta ba Michael da ya sani a baya, baya karya, kuma baya ɓoye abu, komai ka tambaye shi kai tsaye zai gaya maka ba wata kona kona, bai san cewa yanzu Aseef yake ba Michael ba, yanzu ya san me ake cewa sirrinta abu, ya san abin da ya kamata ya faɗa da wanda bai kamata ba.

Zazzaƙar sexy voice ɗin ɗan nasa ne ya katse mishi tunani a in da yake magana da Rimsha, "Ni zan yanka fruits ɗin kenan?". Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, tare da tsugunnawa a gaban bedside drawer ta fara yanka mishi.

"Romeo i want to see your face now". Cewar daddyn, Okey ya amsa mishi da shi tare da juya kiran zuwa video call, kira É—aya ya É—auka, yana zaune a palon kasa shi da uncle Herry, kamar kullum suna shan tea suna kallon labarai a Tv.

"Romeo ina son ganin yarinyar nan da kake magana da ita yanzu". Ba musu ya juya mishi wayar zuwa kanta tana faman yanka mishi apple, gyaran murya ya yi mata ta ɗago dan daddy ya kalli face nata da kyau, tana ɗagowa suka yi ido biyu da juna, wani irin haɗe rai daddyn ya yi tare da ɗaure fuska kamar hadari, da ɗan tsawa ya ce "Romeo na gaya maka bana son yarinyar nan, because bana son bakaken fata, bana son ta zo kusa da ku". Gently ya amsa da cewa "Dama ni son ku nake bi ne?, Ni dama abin da kowa baya so ni shi nake son aikatawa". Babbar magana, abin da ba'a so shi yake so shi kuma? Wannan wani irin mutun ne? Shi dai yaga yana ɓatawa kowa rai kenan shi ne burinsa ko yaya?, Shi wato daban yake da kowa, abin da jama'a basa so, shi yake so, lallai akwai aiki.

"Romeo i said a hate this girl, kuma kada ta sake zuwa kusa da ku, bari ka ji da turawa ƴan uwanku kawai zaku yi mu'amala banda baƙaƙen fata".

Shiru ya yi tamkar ba zai amsa ba. Almost 2 mins daddy na surfa bala'i baya son bakaken fata. Calmly ya fara magana "Dad ban taɓa jin cewa da mutun or da mace nake tare ba ma, amma yanzu da kayi magana ka ce baka sonta, sai naji ashe da mace nake zaune, kuma na ji daɗin zama da ita da baka sonta, wannan matsalar ka ce kana sonta or not, ni dai zama da ita ba fashi har sai na kammala abin da nake yi".

"Romeo kana son ka rinƙa ɓata mini rai ko? To ina nan zuwa Nigeria gobe". "Babu in da zaka zo daddy, ban yi tunani akan hakan ba, kuma ba za'ayi ba". "Romeo for sure dole nazo". Shiru ya yi bai sake tankawa ba, dan idan ya biyewa daddy zasu yi kaca kaca ne, saboda wlh shi babu wanda ya isa ya juya shi ko ya ce mishi ga abin da zai yi a rayuwarsa, idan ya yi magana ya yi kenan, duk bala'in da za'ayi sai dai ayi baya canzawa, zai ga ta yadda daddyn zai zo ba tare da izininsa ba, abin da ko gidan nasu ma ba wanda ya isa ya fita idan bai bada izini ba.

Ita kuma ba ƙaramin tsorata ta yi ba jin yadda suke sa in sa da daddyn nasa, duk da ta san cewa su a wajensu yin hakan ba wani abu bane ma, zaka iya samun uba da ɗa ma suna dambe, amma kafiya irin na Lion ɗin ne yake bata mamaki, idan ya kafe a kan abu ba mai tanƙwara shi, idan ya yi magana ba sauyawa, wannan wani irin mutun ne,? Wai abin da ba'a so shi kuma shi yake aikatawa, wannan kalma ta tsaya mata a rai, da ta yi tunani kuma sai ta ga haka ne, duk rayuwarsa idan aka ce ba'a son abu to sai ya yi, a iya zaman da ta yi da shi, ta fahimci hakan, da daddynta ya ce baya son ta zauna a gidansu ne, shi kuma ya ce sai ta zauna, da daddynsa ya ce baya son su zauna a Naija, shi kuma ya ce sai sun zauna, wannan bala'in da me ta yi kama?, Mutun kamar ba mutun ba, ba zaka taɓa gane mishi ba, yau fari gobe bakin kirin, duk zuciyar da ta yadda da shi ma a kan zai iya sauyawa to ta yaudari kanta, a cewarta.

Jingina wayar tasa ya yi da jikin pillow ta yadda daddy'n zai sami damar ganinsa da kyau, ya miƙe ya nufi toilet, jim kaɗan ya fito ya wanke hannayensa, a in da ya tashi, a nan ya koma ya zauna tare da ɗaukar apple da ta yanka mishi ya fara kai wa ɗan bakinsa, "Romeo ka sani a duniya babu wanda ya kai bakaken fata mugunta, ka dai'na cin abin hannunsu dan kada su cutar mini da kai". Cewar daddyn.
Chapter 100 · 0% Book details