← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 121

Sashe 32

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kina da murya mai shegen daÉ—i, idan kina magana bana son ki daina, just like uncle Musharraf voice naki yake, shima haka voice nasa yake da zaki, sai dai fa kina magana a sanyaye kamar Lion, ke da Lion sam baku son buÉ—e baki ku yi magana sosai, i don't know why, ko dai bakinku na yi maku zafi ne idan kuka É—aga murya?". Yana magana yana satar kallon É—an uwan nasa, wadda tamkar babu shi a cikin É—akin.

Zuba mashi abincin ta yi ta tura mashi a gabansa tana faÉ—in "Yaya Areef nifa wlh kawai ban san ya akayi maganata take a haka ba".

Sai da ya bari ta gama zu ba masu abincin, ta turo masu, sannan ya kira Aseef video call dan su takurawa Lion, yau sai sun sanya shi ya canza magana, dole ya barta ta koma school, yarinya yar karama ace ba zata rinƙa zuwa school ba, cutar ta zaayi.

Ya danna video call ɗin yana faɗin "A'a akwai dalili dai, sai ku rinƙa magana kamar baku son yi?".

Bugu É—aya Aseef ya katse kiran ya kirashi, hakan zai tabbar maka da cewa haÉ—a baki suka yi, sun shiryawa Lion kitimurmura, kuma da alama da wuya ya tsallake masu yau, dan sune rauninsa dama.

"Da gaske yaya Areef......" Bata kai karshen maganar ba zazzaƙar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta. "Get out". Sun cika mashi kunne da surutu, ba damar ya kori Areef, amma ita yana da damar korinta.

Cikin sauri ta miƙe ta nufi waje, tana jiyo voice ɗin Areef yana faɗin "After 30 mins ki zo ki kwashe kayan abincin". Okey ta amsa da shi tare da ficewa abinta.

Kada ku mance da Turanci suke magana.

Duk abin da ya faru, Aseef yana jinsu, dan Areef ya yi picking call ɗin. Jawo ɗan ƙaramin kyakkyawar table dake wajen ya yi tare da ɗaura wayar, ya jingina wayar da tissue pack, ta yadda Aseef zai ji daɗin ganinsu su biyun dukka da kyau.

"My bloods wlh kewarku zata iya yi mini illah fa, please ku dawo ko kuma ni na taho, saura mani Exam har guda huÉ—u fa, ni gaskiya almost 2 weeks suka rage ba zan iya jira ba, ya yi mini nisa".

Lion bai san time da Areef ya kira Aseef É—in ba, jin zazzakar murya É—an uwan nasa yasa shi ya É—ago blue eyes nasa daga kan abincin da yake ci zuwa kan wayar.

Zubawa Aseef ɗin idanu ya yi yana kallon yar ramar da ya yi, da alama dai yana yawan tunanin ƴan uwan nasa sosai, Allah sarki bawan Allah, tun da suka taso basu taɓa rabuwa su yi nisa har haka ba sai wannan karon, duk ya shiga damuwa sosai, dan ma Musharraf na rage mashi damuwar, amma duk da haka sai da damuwar ta fito ta hanyar sanya shi rama.

"Our pleasure muma muna kewar ka sosai, ban taɓa shiga damuwa sosai irin na wannan karon ba, seriously tamkar na rasa wani ɓangare na jikina haka nake ji, amma dai ka kammala Exam ɗin, 2 weeks ai kamar yau ne". Cewar Lion kenan, kuma tun da yake sai yau ya taɓa yin magana makamanciyar hakan, ya yi ne kuma dan ya kwantarwa da ɗan uwan nasa hankali ya samu ya natsu ya rubuta Exams nasa cikin kwanciyar hankali, sannan kuma har ga Allah yana kewar ɗan uwana nasa over, abin na damunsa a rai, dan dai kawai bai da yawan magana ne yasa ba zaka fahimci hakan ba.

Nisawa Areef ya yi kafin ya ce "Ni ba zan iya misilta kewarka da nake yi ba my blood, baki ba zai iya faɗa ba, a kullun ina ji tamkar na yi fiffige kawai na ganni a tare da kai". Turo baki ya yi zai fara yi masu shagwaɓa.

Har lokacin Lion bai ɗauke idanunsa daga kan wayar ba, ji yake tamkar ya sanya hannu ya fito da ɗan uwan nasa ta cikin wayar su rungumi juna. "Zaka fara yi mana shagwaɓar kenan ko?" Cewar Areef.

"Ni ba wani shagwaɓa da zan yi maku, yanzu dai Lion ina son kayi mini wata alfarma ne ka ji?". Shiru bai yi magana ba, sai dai ya ɗaga mashi gera ɗaya alamar ya ji.

Shiru shima Aseef É—in ya yi ya rasa ta ina zai fara. "Aseef abin da nake so da kai shi ne, ka daina yawan tunaninmu da kake yi, bana son ganinka a ramen nan, idan kana son sanya ni cikin damuwa kuma shikenan". Cewar Lion ya yi maganar yana mai da spoon É—in hannunsa ya ajiye a cikin plate É—in abincin.

"To Shikenan Lion na yi alkawarin zai dai'na duk wata tunani, zan daure yanzu dai please my blood ina son ka bar Rimsha ta rinƙa zuwa school, ma'ana ta daina yi muku aikin safe, ya zamana iya na rana da dare ne kawai zata rinƙa yi muku, kaga yarinya ce, idan aka yi mata wasa da karatu a yanzu to za'a canzawa rayuwarta akalar shi ne, please ni zakayi wa ba kowa ba, idan ka yi hakan zan yi murna sosai wlh". Ya kai karshen maganar cikin sigar shagwaɓa.

Ɗaukar spoon ɗin da Lion ɗin ya ajiye Areef ya yi, ɗibar abincin ya yi tare da kawo wa ɗan uwan nasa a bakinsa, buɗe baki Lion ɗin ya yi ya karɓa yana mai dawo da kallonsa kan Areef ɗin, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, cigaba da bashi abincin a baki Areef ɗin ya yi tamkar wasu mata da miji.

Kuka Aseef ya fara yi musu a kan lallai shi gobe zai zo, ya za'ayi yanzu shi ba mai bashi abinci a baki, shi wlh ba zai yarda ba, ya gaji, yanzu ba mai bashi first spoon fa.

Girgiza kai Lion ya yi, Aseef sai Allah, yana bala'in kaunarsu fiye da tunanin mai tunani.

Shi kuma Areef ɗebo abincin ya yi tare da kawowa saitin wayar yana faɗin "Ɗan nema to maza buɗe bakinka na zuba maka, ba dai first spoon ba? To ga shi nan, har ma da last spoon zaka samu, ɗan babynmu, auntar TRIPLETS, sweetien daddy, pleasure Lion, shagwaɓati kuma damuwati na, ciwon kan Uncle T, ciwon cikin Uncle Herry, matsalar Jonh, addabawa rayuwar Jay, wadda mummy ta fi so, dukka kai kaɗai maza buɗe baki, yi sauri......" Bai kai karshen maganar ba ya yi shiru sakamakon damko gashin kansa da Lion ya yi, da ɗan karfi ya ja mashi gashin nasa.

"Wash Lion me nayi maka kuma? Ko mugunta zaka yi mini ne nima, kamar yadda kake yi wa sauran mutane". Shiru ya É—an yi kafin ya ce "Me pleasure na ya yi muku da zaka ce mashi ciwon kan Uncle T, ciwon cikin Uncle Herry, me yake yi masu da ya zama ciwon kansu? Me yasa zaka zage shi?". Cewar Lion.

"Kai fa Lion ka iya mugunta, kuma baka son gaskiya, ai ka sani, waye Aseef ya raina biyun Uncle T, ba dole ya rinƙa sanyawa uncle T ɗin ciwon kai ba, duk wata tsiyarsa idan ya ɗebo a kansu yake sauƙewa, mu kuma ya zo nan yana yi mana kuka da shagwaɓa." Cewar Areef, yana magana yana ciza laɓɓansa, saboda zafin riƙe mishi gashi da Lion ɗin ya yi.

Kara jan gashin nasa ya yi, har sai da ya yasar da spoon ɗin hannunsa ya damko hannun Lion ɗin da hannayensa dukka biyu yana faɗin "Wash wlh wasa nake yi Mishi, ai kowa yasan pleasure ka bawan Allah ne, mumini, shi da ko magana ma baya yi".......... Oh su Areef an ji wuya har ya sauya zance🤣

Runtse idanu Aseef ya yi, har cikin ransa yake jin wannan wash É—in da Areef yake faÉ—a, ji yake yi tamkar shi ake jawa gashin ba Areef ba. "My Lion na yafe mishi, ka sake shi, gashin nasa fa zai iya cirewa, ni wlh na yafe mishi, gara ni ka ja nawa gashin ka sake mishi mashi". Yana magana idanunsa a datse, dan baya son ganin face É—in É—an uwan nasa cikin jin raÉ—aÉ—in zafin da yake ji.

Shiru Lion ya yi tamkar bai ji ba, shi kuwa Areef da ya ji azaba da gaske, bai san time da ya sake jiki ya kwanta a cinyar Lion ɗin ba, hakan kuma ta sanya dole Lion ɗin ya sake shi ba dan ya so ba, ba ta yadda zai yi ya cigaba da riƙe gashin yana kwance a jikinsa.

Duk da ya sake shi bai tashi daga cinyar tasa ba, sai ma gyara kwanciya da ya yi yana mai da numfashi, shi kuma Lion ruwa ya É—auro ya fara sha.

After 2 mins "Tashi mini a kafata" Ya faɗa a sanyaye. Ƙin tashi ya yi, a kule ya ce "Wlh ba zan tashi ba, kazo ka cire mini fatar kai ne zaka wani ce na tashi, to naki tashi sai ka yi jinyata".

"My Areef please ka tashi kada ya sake ja maka gashi, idan ya sake zan yi kuka wlh". Cewar Aseef, ya yi maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka.

ÆŠan zaro mashi dara daran blue eyes nasa Lion ya yi, har É—an tsorata ya yi, saboda da ya zaro idanun nasa, har wani kyalli suka kara yi. Sake turo É—an bakin nan ya yi "Haba mana Lion me nayi maka kuma da zaka tsorata Ni?". Kara zaro idanun nasa sosai ya yi, a sukwane Aseef É—in ya datse nasa idanun kamar zai yi kuka.

Dama abin da Lion yake so kenan, yana son Aseef É—in ya runtse idanu domin ya yi mashi kallon tsab, ya kalle shi da kyau, dan ya lura da canzawar É—an uwan nasu.

Sosai yake kare mashi kallo, yasan idan idanunsa a buɗe, ba zai taɓa yarda su kare mashi kallo ba, sai ya zulle masu, wai kunyar ganin cikin idanunsu yake ji. Shi ma Areef juyo da kallonsa izuwa kan wayar ya yi ba tare da ya tashi daga kan cinyar ɗan uwan nasa ba.
Chapter 32 · 0% Book details