← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 121

Sashe 92

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata same shi a wajen ba, kusa da mattress ɗin ta ajiye tray ɗin tare da juyawa da gudu zata bar wajen, dan ta tsorata rashin ganin shi a wajen, da yake tana gallon ƙasa ne sai ta yi karo da shi bata sani ba, faffaɗar kirjinsa kanta ya daka, shigowarsa wajen kenan ya je ya yi wanka ne ya shirya cikin wandon jeans baki da polo shirt sky blue, ya yi kyau over, ya saki gashin kannan nasa.

Baya ta yi zata faɗi ya sanya hannunsa ɗaya ya riƙo wuyar rigarta, hakan kuma ya yi sanadiyar bayyanar sunansa dake saman tudun tula tulanta, jawota ya yi ya tsayar da ita da kafafunsa kafin ya wuce zuwa wajen mattress ɗin, a gefe ya zauna tare da jawo wayarsa ya kira his excellency a kan ya sanya a turo ƴan sanda da fararen kaya su zo su kwashi gawarwakin nan da ya kashe jiya, abin da yasa ya kashe su dukka ba tare da bar ko guda ɗaya dan ya samu wasu bayanai daga wajen shi ba shi ne, su waƴan nan ba wani abin da suka sani fa ce a kirasu a waya a ce musu suje su kashe wane, hasalima basu san da waye suke waya ba, umarni kawai suke jira sai kuma diran kuɗi a account nasu, dan haka babu wasu bayanai da suka sani, kashe su shi ne dai'dai, shiyasa ya ɓarar da shegu, mugun iri ɓata gari.

Cikin sanyin murya cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ga tea". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba har His excellency ya ɗaga kiran nasa, kara wayar ya yi a kunnensa ya fara magana a nitse cikin kwanciyar hankali, yana fitar da words one by one, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake motsa kyawawan lallausan red lips nasa, ba zaka taɓa cewa shi yake maganar ba, magana cike da class❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*

Dedicated to Maman Yasmin💋

E39-40💋

Cikin sanyin murya cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ga tea". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba har His excellency ya ɗaga kiran nasa, kara wayar ya yi a kunnensa ya fara magana a nitse cikin kwanciyar hankali, yana fitar da words one by one, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake motsa kyawawan lallausan red lips nasa, ba zaka taɓa cewa shi yake maganar ba, magana cike da class.

Bayan ya kammala ya ajiye wayar a gefe tare da yin kasa da kansa kamar mai tunanin wani abin, daddaɗar kamshi su kaninfarin da chitta dake cikin tea ɗin sai dukan hancinsa yake yi, har ga Allah kamshin ta yi mugun yi mishi daɗi, ita kuma tana tsaye kamar wata soja, wani irin kara suka ji tamkar fashewar glass a palon kasa, a guje ta watso ta haye saman mattress ɗin ta ɓuya a bayansa, har da kankame shi ta yi, mamaki ne ya kama shi, wai wannan wace iriyar yarinya ce, tsoronta ya yi yawa, ko motsawa bai yi ba. Sun ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ya yunkura zai miƙe dan ya je ya ga menene ya fashe a palon.

Kankame shi sosai ta yi, ba ƙaramin haushi ta bashi ba, ya tsani mutun matsoraci, a ɗan fusace ya juyo tare da fisgota da karfi, gabaɗaya ta tafi sai saman faffaɗar kirjinsa, damko wuyarta ya yi yana ƙoƙarin fara magana, zaro idanunta waje ta yi a matukar tsorace, ba ƙaramin kyau razananniyar face ɗin nata ta yi mishi ba, musaman ma da ta zaro idanun nan nata, ga su sleeping eyes dara dara, ga su farare tas kamar audiga, ya tsani ganin matsoraci, amma yau fuskar matsoraciya ya burge shi, tsoron ya yi wa face ɗin nata kyau, sake ta ya yi tare da miƙewa ya nufi palon kasan, ita kuma kwanciya ta yi a wajen ta takure waje guda, jikinta sai wani kerma yake yi.

Babu kowa palon kasa, daga in da yake tsaye ya hango cikin kitchen, ashe cup É—in daddy da ta É—auka bata mai da drawer da kyau ta rufe ba, kuma ta jawo tray É—in cups É—in baki baki dan tsawonta bai karisa kaiwa can ba, to shi ne tray É—in ya faÉ—o gabaÉ—aya glass cups É—in suka fashe, guntun tsaki ya ja tare da juyawa ya koma saman.

A in da ya tashi ya koma ya zauna, cup ɗin tea ɗaya ya ɗauka cikin natsuwa ya ɗan zuba sugar kaɗan ya fara sha, dan kamshin tea ɗin ya yi mugun tafiya da shi, haka zalika ɗanɗanon tea ɗin ta yi mishi daɗi, kuma yunwa yake ji sosai yasa shi ya sha, idan baku manta ba, bai ci abincin daren jiya ba. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba, Lion ya sha tea ɗin da ta girka mishi, har wani nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da miƙewa zaune a tsakiyar mattress ɗin tana ɗan satar kallon shi, da yake suna kusan a jerene waje guda, sai dai da ɗan rata a tsakaninsu.

Wayarsa ce ta fara kara alamar shigowar kira, yana dubawa sai yaga Aseef ne, nisawa ya yi, ba ƙaramin daɗin kiran nan ya ji ba, yana kewarsu sosai da sosai, ɗaukar kiran ya yi, suna haɗe su dukkansu biyu kwance a saman bed nasa, cool murmushi Aseef ya saki, shi dai Areef bai da yawan fara'a, amma akwai kyan zuciya kamar me, zuciyar zinari ke gare shi, ba kowa da kowa yake samun ni'ima da baiwar zuciya irin makamanciyar tasa ba.

Kamar abin haɗin baki, har suna rige rigen tambayar ina Rimsha, Lion ya ɗan yi mamaki, wai ba za su tambaye shi ya yake ba, ya ya isa garin da ba nasu ba, ya ya kwana, sai ina Rimsha suke tambaya?, Ko gaisawa basu yi ba, su dai ina Rimsha kawai, lallai Rimsha ba ƙaramin samun damar mallake zuciyar ƴan uwansa ta yi ba,.

Shiru ya yi musu bai tanka ba, turo baki Aseef ya yi tare da saka mishi kukan shagwaɓa a kan lallai shi sai an nuna mishi Rimsha. "Ka sha maganinka Areef?" Shi ne abin da ya ce dasu, gyaɗa mishi kai ya yi yana mai kara tambayarsa dan Allah ina Rimsharsu take. "Yau ya kamata ka cire bandejin dake wajen ciwon ai, yanzu komai normal ne". Ya sake faɗa a sanyaye, tamkar bai ji tambayarsa Rimsha da suke yi ɗin ba, amsa mishi da okey Areef ɗin ya yi tare da sake tambayarsa ina Rimsha a karo na uku.

Shiru ya yi bai amsa ba, cikin zoyala Areef É—in ya sake cewa "Wai Saif me ya faru ne na ganka kamar sabon ango? Sai wani kyalli face naka take yi, ko dai garin Abujan ne ta yi daÉ—i sosai?". Kwashewa da dariya Aseef ya yi yana faÉ—in "Ni dan Allah ka nuna mini my Rimsha, ita nake son gani, idan ba haka ba, wlh bani ba cin abinci yau". Ya san halin Aseef sarai, zai aikata ya ki cin abincin.

Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, ya fahimci ba za su barshi ya yi numfashin or ya sha iska ba matikar bai nuna musu in da take ba, da alama kuma idan bai nuna musu ita ɗin ba, ko abinci ba zasu ci ba, yadda suka kafe da sanyin safiyar nan suke wani tambayarsa ita, wannan kenan dan ita suka kira shi ba dan lafiyarsa ba, ita suka kira su kallah ba wai su tambaye shi ko ya isa lafiya ba, lallai ma sun shahara, yanzu Rimsha ta zama kamar kishiyarsa a zuciyarsu.

Gently ya ɗan waigo tare da ɗago dara daran blue eyes nasa ya sauƙesu a kanta, tana zaune shiru kamar mai tunanin wani abin, ba karya ta yi kyau sosai cikin kayan jikin nan nata, gabaɗaya shape nata sun bayyana, ga shi ba'a magana in dai wajen shape ne, akwai shi sosai, ƙasa ta yi da kanta dan kada su haɗa idanu, yatsun hannunta ta fara wasa da shi kamar wata mara gaskiya, zazzaƙar sexy voice nasa ne ya ratsa dodan kunnenta, calmly ya furta ta zo nan, ba musu ta matso gefen shi sosai tana wani yin kasa da kai, Aseef yana ganinta ya furta "Our Queen!" Shi kuma Areef ajiyar zuciya ya sauke.

Jin muryar Aseef yasa ta ɗago kanta, wani irin kyakkyawar kayatatcen cool murmushi ta saki wadda sai da dimple nata suka yi wani irin lotsawa na musamman, siririn wishiryarta dake tsakanin fararen hakwaranta ya bayyana, ba zaka taɓa cewa abinci ko wani abin ya taɓa ratsa cikin hakwaran nan nata ba saboda haskensu, sai kyalli suke yi, suna shan wankewa ne da kayan wanke baki masu inganci, shiyasa suke tas.

Shagwaɓe murya ya yi yana faɗin "Our Queen ina missing naki over wlh, yau ba zanci first spoon naki bafa". Ita ma shagwaɓe murya ta yi kamar dai yadda ya yi mata magana, tamkar zata yi kuka ta ce "Nima ina kewarku sosai, Yaya Areef dan Allah ku shigo mota kawai ku biyo mu, zan fi jin daɗi, yanzu wlh ina tsoron gidan sosai, akwai wasu mutane, dan Allah kuzo zan fi jin sanyi". Yadda tayi maganar sai da ta sanya Lion ɗin waigowa ya kalleta, ga shi tana magana dimple nata na wani irin lotsawa, duk wanda ya kalleta sai ta burge shi, ga shagwaɓa da take zubawa Aseef, abin ba'a cewa komai, yau har cikin zuciyarsa sai da ya ji ta burge shi, kawar da kallonsa ya yi daga kan nata tare da cigaba da shan tea ɗin nasa ya kawar da wayar daga face nasa zuwa saitin tata.
Chapter 92 · 0% Book details