← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 121

Sashe 21

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawaye ta fara yi tare da fara É—aukar attarugun tana kai wa bakinta, har ga Allah ita ma ba ma abociya cin yaji bane, bata ci ko kaÉ—an a baya, É—an zamanta a gidansu Kausar ne ma ta É—an koyi cin yajin, kunsan Yarabawa da shegen son yaji kamar me, to a nan ta É—an koya, amma a gida wajen mummynta, bata ci, mummy ma bata ci ne yasa bata sanya masu a cikin abincin, yau ta ga tashin hankali iya ganin idon ta.

Kwara ɗaya ta ci harshenta ya ɗaye ya yi jawur kamar wuta, kai gaskiya punishment ɗin soja Bala'i ne, shi saboda sun wahala wajen horo, sai ya rinƙa ganin kamar kowa ma irin sane, sai ya rinƙa ganin kamar komai ya yi wa fararen kaya daidai ne, saboda shi already ya hororu, abin da bata sani ba, duk abin da kake yi, zakaga kowa ma tamkar haka take yi, walau mai kyau walau mara kyau, shiyasa idan sojoji suna hukunta mutun, zaka samu hukuncin na da bala'in tsauri fiye da tunanin mai tunani, su kuma normal ne a wajensu.

Tana hawaye ta ɗauko na biyu, ga shi har guda goma ne a cikin bowl ɗin, alama ya yi mata da hannunsa ba tare da ya kalleta ba, akan ta ɗebo ruwan tea nasu mai jafi ta rinƙa korawa da shi, TASHIN SENSE bala'i kan bala'i kenan, zafi kan zafi, ruwan zafi haɗe da attarugu, eyya i pity you RIMSHA, Lion ya kware wajen horarwar mugunta, ba kalar da bai iya ba, attarugun ita kaɗan ta ma yaya bare kuma da ruwan zafi, ya ilahi ya lillahi.........😭

Haka ta ɗebo ruwan tea ɗin, ga shi ya haɗu mata da bata son green tea ɗin nan nasu, wlh yarinyar nan ta yi kuka ne har idanunta suka kumbura, shi kuwa tamkar babu shi a cikin ɗakin, Areef Imran suna Palo, kuma shi Areef ya san me yake faru, abin da yasa bai tinkari Lion ɗin ba, yasan idan ya je ba ƙaramin faɗa za su yi ba, saboda Lion ɗin yana jin yunwa sosai, yana son cin abinci ya yi barci saboda ya gaji, sun ɓata mashi rai sosai, a yadda yake nan babu uban da ya isa ya kwaci Rimsha da Mark a hannunsa har sai sun lashe hukuncin nan tas, to yasan idan ya je fa ba ƙaramin faɗa za su yi ba yau, to wai ita Rimsha me laifinta ne? Dan kawai ta kai mashi abin? Ita ta girka ne? Ita da kitchen ɗin ma bata shiga har sai idan zata je ɗaukar abinci, amma saboda bakar zuciya na fitar hankali shi ne har da haɗawa da ita.

Allah sarki duk wanda ya kalleta a halin da take ciki sai ya matsa mata kwallah, lips nata sun tashi daga pink sun yi jawur tamkar nasa lips É—in, kamar ta sanya masu jan lips stick, sai hawaye take yi, ta kasa sakin kuka mai sauti saboda kada ya ji, idan ya ji zai kara mata wani hukuncin, baiwar Allah idanunta sun yi hawur sun yi luhu luhu.

Haka ta cinye attarugun nan tas, hawayene majina ne duk sun haÉ—e mata waje guda, da dama ma ina ga hawayen jini zata yi. Hijabinta ta kamo bayan ta gama cinyewa, ta shiga goge hawayen nata tare da majinar tana mai dana sanin zuwanta gidan nan ma baki É—aya, wani irin azababben ciwo kirji ne ya dira mata lokaci guda, ga attarugun da shegen bala'in zafi, ga su manya ba halin ta haÉ—iye bata tauna ba, dole haka ta taunesu.

Duk abin da take yi yana same da ita, sai dai kawai shi ya fi karfi ya ɗaga ido ya kalleta ne a nasa cewar, har yau bai san kamannin fuskarta ba, ɗazun da ya juyo ne ma da tana kallon shi to za su iya yin ido huɗu, dan ita ya fuskanta, amma kuma ta yi kasa sosai da kanta, lokacin da ta yi mashi ɓari da rana kenan, hakan yasa bai ma ga face nata ba ya wuce dressing room, so bai san kalar face na ta ba, amma kuma tabbas ya riƙe wadda ta kira shi da sunan GAR a gidansu Imran a lokacin da ya zo, kuma e lallai yana son sani wace ce wannan, sai dai kuma bai tambayi Imran ba, dan gani yake shirme ne, kuma a haka maganar ta tsaya mashi a rai, abin ne da mamaki yadda ta gane ainahin face na shi ba tare da face mask ba, da yanzu Rimsha zata maimaita wannan suna na GAR to tabbas zai gane ita ɗin ce, abin da yasa yanzu bai gane muryarta ba saboda a ranar yadda ta kira sunan GRA daban da yadda take magana, har wani lankwatsa ta yi wa sunan kamar a bakinta a ka halinci sunan nan ranar, so ita ce magana ɗaya da ta tsaya mashi a ransa tun da ya zo Nigeria, yana ganin shirme ne yasa bai tambayi Imran ba, amma ya kasa mancewa da shirmen kuma. TO FA......🤔

Umarni ya sake yi mata akan ta cinye abincin da ta zuba mashi a cikin plate É—in, idan ta gama ta kwashi kayan abincin ta fitar mashi a É—aki, ba musu ta fara cin abincin, tasan baya magana biyu, tana ci harshenta tamkar zai É—aye saboda azabar zafi, ya yi wani jawur da shi kamar jini, azaban balai take yi mata, lips nata ma suka yi ja bare kuma harshe.

Allah ya rufa mata asiri ba dayawa sosai ta zuba mashi abincin ba, hakan yasa ta cinye da wuri, kwashe kayan abincin ta yi tare da nufar waje, har lokacin idanunta na zubar da kwallah sun ki tsayawa.

A palo ta isko su Imran kamar yadda ta tafi ta barsu, taki kallon in da suke bare su fahimci wani abin, shi kam Areef da ya san komai dan ya tambayi Mark da taren Spanish dan kada Imran ya ji, zuba mata idanu ya yi yana kallonta cike da tausayawa, Imran kuwa bai wani damu da ya kalleta ba, yana latsa waya, kafin ya É—ago kuma ta wuce izuwa palon kasa.

Babu kowa a kitchen É—in, ga wani abinci kuma an É—aura a saman wuta, ajiye kayan abincin ta yi, ta nufi fridge, a hanzarce ta fara dubawa ko zata sami Madara ta ruwa, ta ko yi Sa'a akwai, sauri sauri ta É—auko kwara É—aya, ga sanyi madarar, ta fasa tare da kafawa a É—an bakinta ta fara kwankwaÉ—a, azaba tai azaba, bata san time da ta sha kwankwani biyu ba, jin motsin mutun ne yasa ta farga ma ashe gwangwani biyu ta sha.

Mark ne ya shigo cikin kitchen ɗin dan duba girkin da yake yi, idanun nan nasa sun yi jawur, da alama ya sha bakar azaba, kuma shi ma da alama ya ci attarugu over, lips nasa duk da suke jawur yau sun kara ja over, har wani kumbura suka yi, ko kallon in da take bai yi ba, ya wuce gaban gas, mamaki take yi, a ranta tana faɗin "Punishment da zai sanya wannan jibgegen Bature sojan idanunsa su yi ja haka ba karamin abu bane, lallai tabbas Lion ya kware wajen mugunta, fata ɗaya kawai mutun zai, shi ne kada Allah ya haɗa shi da mummunar rana ta haɗuwa da hukuncin Lion, Allah ya rinƙa haɗa shi da ɗayar fuskar Lion ɗin, wato ta adalci ba ta mugunta ba". To amin dai kam, idan ba haka ba, fuskar muguntan Lion ai ko makiyi ba zaka yi mashi wannan mummunar fata ta haɗuwa da face ɗin ba.

Goge hawayenta ta yi tare da wucewa ta fice daga kitchen É—in, yau dai bata yi amai ba da ta ci abincin nasu, azababben raÉ—aÉ—in da harshenta yake yi mata ma, ai ya mantar da ita ta ci wani abu wai abinsu.

Bata bi ta kansu Imran ba, bedroom nata ta wuce, sauri sauri ta shige toilet, fuskarta ta fara wankewa fes, ta fito tare da canza kayan jikinta zuwa goguwar rigar Abaya launin Navy blue, ta yafo mayafin abayar a kanta, ta nufi Palo.

Still a in da ta barsu, a nan ta dawo ta same su, kusa da Imran ta zauna. Ɗan juyowa ya yi ya kalleta. "My first lady yau baki jin barci ne?" Shi ne abin da ya faɗa cikin harshen Hausa, ɗan kwantowa ta ɗan yi a kafaɗarsa, a shagwaɓe ta ce "Yaya Imran dan Allah yaushe zamu je gidan Bappa, wlh tun da naji daddy ya ce su Umaisha ƴan uwana ne ina matukar kaunar ganinsu, dan Allah ka kaina na ga ƴan uwana". Shiru ya yi yana tunani, yanzu ai ko uban Rimsha bai isa ya yi iko da ita ba, yanzu Lion ne sabon uban ta.....🤣

Shi maganar da ta yi ma ta tuna mashi da son tambayar Abbansa da yake yi akan me ya haÉ—a su faÉ—a da bappa Hosain, tun da dai sun ce shi bappa Hosain É—in nasu faÉ—ar daban ne dana su daddyn Jelly, ma'ana shi Daddyn Rimsha tun iyayensu na raye ya yi fushi ya bar gidan, su daddyn jelly kuma, sai bayan auren Abba da Hjy Umaiya, har ma an haifi Imran, sannan suka sami gagarumin matsala a tsakaninsu, amma fa kafin auren Hjy Umaiya É—in ma akwai wata tangarÉ—a da suka samu na kin auren, abun dai ya haÉ—u ne kashi kashi sai ya tadda gaba guda É—aya.

"Yaya Imran ka yi magana mana? Yaushe zaka kai Ni? Wlh ina bala'i kewar Aunty AKILA". Nishawa ya yi tare da sauƙe ajiyar zuciya. "Rimsha gobe zan kawo maki Akila gidan nan ku wuni, ita ma Umaisha zan samu lokaci na ɗauko maki ita, amma fita kam kema kinsan ba zai taɓa yiwu ba, yanzu kin zama sarauniya sai dai a kawo maki duk wanda ki ke da bukatar gani".

Narai narai ta yi da ido kamar zata yi kuka, shi dai Areef ya zuba masu idanu ne kawai tun da ba jin me suke faÉ—e yake yi ba, baya jin Hausa ko kaÉ—an, sai dai kawai ya yi ta binsu da idanu yana murmushi.
Chapter 21 · 0% Book details