Sashe 115
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Babu alamar shakka ko tsoro, nadama bare kuma sarewa a tattare da matar, idanunta a tsaitsaye, a bushe garau, ta ce "Kishiyata mana na zubawa shinkafar ɓera taci ita da ƴaƴanta biyu suka mutu, ni kuma aka wucu dani nan, ni wlh wannan gidan ma ya fi mini daɗin zama, amma wai fa kashe ni za'ayi, kawai zaman ɗan lokaci nake yi a nan, kuma da kike ganina a cikin ɗakin nan, nine mai ƙaramin laifi, wancan kuma ban san me ta yi ba, mun tambayeta sai ta ce babu komai, to babu komai za'a kawota nan ne?".
Ai kuwa Jehan bata san time da ta sake ta ba, baya kaÉ—an ta ja tana kare mata kallo, jibi yadda ta furta ta yi kisan tamkar wadda ta kashe kaji ko tattabaru, ba mutane ba, anya wasu suna son samun rahmar Ubangiji ko yaya take kuwa? Kai gaskiya wasu dai sun rantse dole dole sai sun tabbata a wutar jahannama, a haka kuma wai ita ce mai karamin laifi da suke ikirari a cikin waÆ´an da suke a É—akin before Jehan É—in, wannan bala'i da me ta yi kama?.
Kallon banza Asiya wadda ta yi magana É—azun ta wurgawa Jehan É—in kafin ta ce "Me kika wani ja baya dan kinji abin da Raliya ta ce? Ai ke karamar Æ´ar iska ce, mu kam ai jiga jigai ne, dan haka ma ki daina tsoro na gaya maki, a duniyar yanzu kada ki ji tsoron kowa nake gaya miki, ki zama jaruma kamar dai mu?". Da alama wannan Asiyar Æ´ar wiwi ce, Æ´ar hauce ba kaÉ—an ba, tana abu kamar wata jikar kauraye.
Shiru Jehan ta yi tana tunanin in dai zata zauna a nan, to ya zama dole ta fito da halinta na baya, domin ta lura gabaɗaya ƴan gidan nan tantiran ƴan iska ne, to dole ta koma ainahin jinin Nawazudden ɗinta dan su ci uban juna, daga zuwanta yau taga bala'in da ya sha gaban tunaninta, ji bi yadda suke faɗar laifukansu da bakinsu sanka sanka, lallai duniya abin tsoro ce, ba dole mu rinƙa shiga masifu kala kala ba.
Matsowa kusa da ita É—ayar da bata yi magana ba take shiru shiru mai suna Ameera ta yi tana faÉ—in "Ni ban san sunanki ba, amma dai koma ya sunanki ina son ki sani wlh ban aikata wani laifi ba aka kawo ni nan, zaluntata aka yi, kawai fin karfi a ka nuna mini".
Juyowa Jehan É—in ta yi suna fuskantar juna da Ameera É—in, yarinya yar matashiya da ba zata wuci 21 years ba, zuba mata idanu Jehan É—in ta yi, da alama yarinyar tana da ilimi kuma ta yi karatu.
"To me yasa aka kawo ki nan?" Miƙewa ta yi ta dawo saman gadon Jehan ɗin tana faɗin "Wani yaron amshakin mai kuɗi ne ya yi wa wata yarinya fyaɗe, shi ne iyayen yarinyar suka kai kara court, dana ji labari a matsayina na ƴar jarida mai son tallafawa kasar, sai na nemi zantawa da yarinyar, ni gaskiya ƴar talakawa ce, da kyar da suɗin goshi iyayena suka iya biya mini kuɗi nayi karatu, iya diploma na tsaya a karatu na, Allah ya sa dai ina da rabo na sami aiki, to kamar dai yadda kika sani ne a duniyar yanzu mai kuɗi shi ne mutun, talaka kuma bawa ne, haka aka tauyewa yarinyar nan hakkinta, aka rufe case ɗin da wasu kananan shaidu wai dama yarinyar bin maza take yi, shi yaron lokacin da abin ya faru ma baya kasar, kawai dai talauci ne ya yi wa iyayenta yawa yasa suka yi wa yaro wannan sharri dan su sami kuɗi, iyayen yaro suka saye alkali ya basu gaskiya, har da ɗaurawa iyayen yarinya diya da zasu biya wai dan sun ɓata wa yaro suna, ni kuma dana ga haka sai na yi ƙoƙarin zantawa da yarinyar, na samu hujoji daga wajenta shi ne nayi ƙoƙarin bankaɗo gaskiya, daga haka ne fa suka ɗaura mini sharrin ina dillancin kwayoyi, ni ban san taya akayi kwayoyin maye suka shiga jakata har gidan mu ba, ina dawowa daga wajen aiki ƴan'sanda suka kamani wai sun sami information a kan ina dillancin manya manyan kayan maye, daga haka court ta yanke mini hukuncin ɗaurin rai da rai a nan gidan, dan ba kananan kayan maye aka samu a jakata ba, ban san hawa ba ban san sauƙa ba, sai dai na ganni a nan, yanzu sai Allah kaɗai ya san ya iyaye na suke, yau watana uku kenan a nan, kanina ne kawai ya taɓa zuwa sau ɗaya farkon rufeni da aka yi, ya ce mini baba yana asibiti, tun daga ranar ni ban sake ganin kowa nawa ba". Ta kai karshen maganar tana sharar kwallah dake zubo mata, ita kam Jehan ta rasa ya zata yi da waƴan nan abubuwa, can gidan Hjyr daɗi ga Maryam da take son ta kama ubanta ta yi mishi ɗan yen hukunci, nan kuma ga Ameera, wannan bala'i da me ya yi kama ne wai?
Dariya Asiya ta kwashe da shi har da shewa tana tafa hannu, ita ma dai Raliya dariya ta kwashe da shi tana faɗin "Yo idan ban da abin ɗan talaka da neman saka kai cikin masifa, ina ke ina nemo wasu hujjoji dan ki tona mishi asiri fisabillilahi? To ai shikenan yanzu ga shi ai kin kare a wannan gida ɗaurin rai da rai, dama wannan abin ne kike ɓoyewa kika ki gaya mana laifinki? Wlh na zaci ma kan wani kika fille ko kin kwakwale idanun wani jaririn ne? Ashe ke salihar baiwa ce ma ban sani ba, to ai ga shi yanzu zaki kare gabaɗaya kuruciyarki har tsufa zuwa mutuwa a nan, kuba ƴan shisshigi ba? Ɗan talaka da bai iya samun karamar dama ko ya take ba, to yanzu ai sai ki baza shaidar kowa ya gani". Ta kai karshen maganar tare da sake tuntsurewa da dariya.
A walaƙance Jehan ta kalleta ta watsar kafin ta ce "Ke dai anyi dabba jahila wlh, an gaya miki shi talaka ba mutun bane? To idan baki sani ba ki sani, wani talaka da yake yawo a cikin bola sai ki tarar ya fi shugaban kasa samun matsayi a wajen ubangiji, ki zama mai yin fariya da aikata aikin Allah ba saɓon Allah ba, ki bugi kirji ki ce kina da kusanci da Ubangijinki ta gefen sallah, azumi, Zakka, sadaka, da sauransu, ba ki daki kirji kina cewa kin fi wani abu kaza na duniya ba, Allah da ya baki ba wani abin kika yi mishi ya baki ba, haka suma waƴan da bai bawa din ba, ba wani abin suka yi mishi ya hana su ba, bai manta da kowa ba, yana sane da dukka bayinsa, so ki zama mai fariya da kin fi kowa aikata aikin Allah ba kin fi wata or wani samin wani abu na duniya ba, banza ballagaza kawai, wadda bata san ciwon kanta ba". Ta kai karshen maganar rai a matukar ɓace.
A fusace Raliyar ta damko wuyar rigarta tana faɗin "Bani da mutunci, wlh yanzun nan sai na saɓa miki kamanin, ke har kin isa ki ɗaga mini murya a cikin ɗakin nan dan ubanki?". Buge hannun nata jenan ɗin ta yi, a walakance ta ce "Ke ma kika ce baki da mutunci bare kuma ni, to da kike kallona hakan nan, sam ban san menene mutunci ba, na fiki zama mara kunya, dan haka ina mai baki shawara wlh tun wuri ki kama kanki babu ruwanki da ni, bana shiga harkar kowa, amma idan mutu ya shiga tawa, to fa ya sani duk girmansa bana shayin na bi ta kan mutun na take banza!!".
A harzuƙe Raliyar ta miƙe tare da sake riƙo mata wuyar riga ta ɗaga hannu da nufin marinta, cak Jehan ɗin ta riƙe hannun nata tare da miƙewa ita ma tana faɗin "Wlh idan kika yi gigin marina bazaki sake marin wata ba a duniyar nan, an gaya miki ni irin kishiryaki da kika kashe ne? To ni ba haka nake ba, ni kaɗai na gayyya ce mai zaman kanta, idan kina so ki jawa kanki bala'in da gabaɗaya zuria'arku ba zasu iya ɗauka ba kuma to Bismillah zaki iya sanya hannunki a jikina".
Abinku da prison, Asiya tana makale saman gadonta tana zuga Raliya a kan kada ta yarda wannan ƴar yarinya ta ɗaga mata murya, ita taki yarda ta sauƙo ta shiga faɗar dan tana tsoron idan gandurobobin sun ji ana faɗa suka zo, su haɗa da ita su yi mata hukunci, shi ne taki saukowa ta shiga, tana daga sama tana kara hura wutar abin.
Miƙewa Ameera ta yi tana rokonsu a kan dan Allah su bari, ita kuwa Raliya har cikin ranta ta tsorata da jin kalaman Jehan, tana ganin kamar Jehan ɗin ta taki wani tsiyar ne, dama kunsan irin wannan idan baka san mutun ba irin haka ta kasance a tsakaninku, to zaka rinƙa ganin kamar ya taki wani abin ne, tsoron da ta ji ne yasa da Ameera ta basu hakuri, sai ta hakura ta saki Jehan ɗin ta koma saman gadonta ta kwanta, ita ma Jehan komawa saman nata gadon ta yi ta zauna tana tunanin yadda zata ɓullowa waƴan nan abubuwa da suka sha kanta.